Ƙosen Wake
Kayan haɗin ƙosen wake:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Mai
iv.
Ruwa
v. Tarugu
vi. Tattasai
vii.
Wake
Za a jiƙa wake, sannan a surfe a wanke shi tare da cire hancinsa. Idan da dare ne, za a baza shi a faifayi ko a wani masaki mai faɗi kafin gari ya waye, gudun kada ya yi tsami. Daga zarar gari ya waye, sai a ɗauraye shi da ruwa mai tsabta. Daga nan za a gyara tarugu da tattasai da albasa a yanka a sanya a cikinsa. Za a iya sanya tafarnuwa idan ana buƙata. Da zarar wannan ya samu, sai maganar markaɗawa bisa dutsin niƙa ko kuma injin markaɗe.
Bayan an markaɗa, za a zuba a ƙwarya ko wani mazubi, sannan a sanya gishiri a yi ta burgawa
har sai ya gaurayu sosai. A gefe guda kuma, za a ɗora kasko bisa wuta a zuba man gyaɗa. Daga nan za a riƙa ɗibar ƙullun nan kaɗan-kaɗan ana zubawa a
cikin mai. Yayin da gefe guda ya soyu, sai a juya ɗaya gefen da tsinke ko wani abu mai kama da shi ta yadda
shi ma ɗaya gefen zai soyu
sosai. Da zarar ya soyu, ƙosai ya samu ke nan.
Ana cin ƙosai da yajin
barkono ko na ƙuli.
Ƙosen Rogo
Kayan haɗin ƙosen rogo:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Rogo
iv. Ruwa
v. Tarugu
Za a niƙa rogo a tankaɗe a kwaɓe shi da ruwan ɗumi, sannan a saka gishiri da albasa da tarugu waɗanda aka jajjaga. Daga nan za a riƙa cuccurawa daidai yadda ake buƙata, sai kuma a soya shi irin yadda ake soya ƙosen wake, wanda bayanin yadda ake yin sa ya gabata a ƙarƙashin 13.8 da ke sama.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.