Ƙuli da ƙuli-ƙuli da ƙarago, duk abu guda suke nufi. Yayin samar da ƙuli, akan tanadi abubuwa kamar haka:
i. Gishiri
ii.
GyaÉ—a
iii. Man gyaÉ—a
iv.
Ruwa
Za a soya gyaɗa, a murje sannan a fece ta. Daga nan za a sanya a turmi a kirɓa. Bayan ya kirɓu sai a nemo dutsin niƙa a fara markaɗawa sannu a hankali har sai ya markaɗu tsaf. Za a sanya wannan markaɗaɗɗiyar gyaɗa a turmi sannan a yi ta juyawa da taɓarya. Za a sanya ruwa kaɗan. Yayin da ake ci gaba da juyawa, zai riƙa fitar da mai. Za a riƙa yi ana ɗebe wannan man.
Yayin da aka fahimci ba sauran mai da zai iya fita, sai a
juye wannan tunkuza a ƙwarya ko a wani
mazubi. Za a riƙa ɗaukar wani adadi daidai gwargwado daga tunkuzar ana
matsewa bisa dutsin matsa. Mai (mayi) zai ci gaba da fita har sai an ga ya je
ƙarshe. Wannan tunkuza da aka gama matse manta ita ake
soyawa a cikin man gyaÉ—a. Ana iya sanya
mata gishiri yayin suyar.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.