Nakiyar Gero
Kayan haɗin nakiyar gero:
a. Gero
b. Kayan yaji
c. Maɗi
Za a nemi gero a surfe, a dake, sannan a tankaɗe. A wannan gaɓa ana da zaɓi guda biyu.
(i) Za a iya soya garin[1]
(ii) Za kuma a iya turara shi kamar yadda ake turara garin tuwon buski. Yayin da aka soya garin ko aka daka shi, za a sanya kayan yaji ciki tare da maɗi sannan a gauraya. Daga nan sai a zuba shi cikin turmi gaba ɗaya a yi ta dakawa. Za a dage da dakawa har sai ya fara fitar da wani maiƙo(mai), wato ya yi danƙo. Za a ga ya cuccure wuri guda. Yayin da aka ga ya koma haka, nakiya ta kammalu ke nan, sai maganar yayyankawa daidai girman da ake buƙata.
Nakiyar Shinkafa
Kayan haɗin nakiyar shinkafa su ne:
a. Shinkafa
b. Kayan yaji
c. Maɗi
Ana wannan nakiya ce da ɗanyar shinkafa.[2]
Za a wanke shinkafa sannan a ɗebi wata adadi na shinkafar a ajiye gefe guda. Wadda aka ɗiba ita ake kira dawaki. Za a turara shinkafar ko
a soya kamar dai yadda ake yi wa gero.[3]
Bayan an soya ko an turara, ana sanya dawaki ciki tare da kayan yaji da kuma maɗi. Daga nan sai maganar kirɓawa a turmi. Da zarar ya kirɓu, nakiyar shinkafa ta samu ke nan.
[1]Yadda ake
soya garin shi ne, za a sanya shi a tukunya sannan a ɗora bisa
wuta. Ba za a
sanya ruwa ko mai ba. Za a riƙa juya wannan gari ana iza wuta. A haka har sai garin ya fara
komawa launin ja.
[2]An
bayyana abin da ake nufi da ɗanyar shinkafa a ɗuren da aka kawo
a ƙarƙashin 13.3.
[3]A duba
masar gero a ƙarƙashin 13.5.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.