Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Masar Gero Da Masar Shinkafa Da Masar Masara

Masar Gero

Kayan haɗin masar gero:

i. Albasa          

ii. Gero          

iii. Kanwa

iv. Mai             

v. Ruwa

Da farko, za a surfe gero a bushe, sai kuma a ɗebi wani adadi na geron a matsayin ƙullu; ragowar za a daka ya yi laushi sosai, sannan a tankaɗe. A gefe guda kuwa, za a sanya ƙullun da aka keɓe a tukunya a aza bisa wuta, a dafa. Bayan ya dafu sosai, za a sauke a bar shi har sai ya yi sanyi. Garin da aka tankaɗe, za a baza shi a ƙwarya. Daga nan ne kuma za a baza wannan dafaffen ƙullun a gauraya.

Da zarar wannan ya samu, za a zuba gaba ɗaya a turmi sannan a kirɓa tamkar dawo/fura. Ana yanka albasa ciki kafin a fara kirɓawa. Bayan ya kirɓu tsaf, sai a juye a tukunya ko ƙwarya a rufe. Za a ajiye shi ya kwana. Yayin da gari ya waye, za a tarar da ya hau.[1] Za a jiƙa kanwa a gefe guda, sannan a dama wannan kullu da ruwan kanwar. Da zarar wannan ya samu, sai batun soyawa a tanda.

Za a hasa (hura)wuta sannan a wanke tanda a ɗora. Za a riƙa sanya mai a gurabun tandar sannan a riƙa zuba ƙullun daidai gwargwado. Yayin da ɓari guda ta soyu, sai a juya ta zuwa ɗayan ɓarin sannan a ƙara yaryaɗa mai. Da zarar ta soyu, masa ta samu ke nan. Ana cin masa da yajin ƙuli ko maɗi ko miya. Wani lokaci kuma akan ci haka ba tare da yajin ƙuli ko miya ba.

Masar Masara

Kayan haɗin masar masara:

i. Albasa          

ii. Mai

iii. Masara       

iv. Ruwa

Yayin samar da masar masara, masara ake surfewa a bushe. Za a jiƙa wannan masara a bar ta har sai ta kwana, ta jiƙa sosai. Washe gari za a tsame wannan masara a shanyata. Bayan ta tsane, za a sanya a turmi a daka. Za a rinƙa dakawa ana tankaɗewa tare da fitar da tsaki gefe. Wannan tsaki shi ake dafawa a matsayin ƙullu.

Kamar yadda ake masar gero (wanda aka yi bayani a 13.1 da ke sama), ana zuba ƙullun kan garin bayan an sauke ya yi sanyi. Za a yayyanka albasa ciki sannan a zuba a turmi a kirɓa. Za kuma a rufe a tukunya ko ƙwarya a bar shi ya kwana. Da safe za a tarar da ya hau, sai kuma a jiƙa da ruwan kanwa. Ana soya masar masara kamar yadda ake soya ta gero.

Masar Shinkafa

Kayan haɗin masar shinkafa:

i. Albasa          

ii. Kanwa       

iii. Mai

iv. Ruwa         

v. Shinkafa

Da ɗanyar shinkafa ake yin masar shinkafa.[2] Za a wanke shinkafar sannan a ware ƙullun. Ƙullun za a sanya shi cikin tukunya a dafa. A ɓangare guda kuma, za a daka sauran shinkafar sannan a tankaɗe ta. Bayan ƙullun ya yi sanyi, za a zuba bisa wannan garin dakakkiyar shinkafa sannan a kirɓa. Daga wannan gaɓa, hanyar da ake bi domin samar da masar shinkafa daidai take da ta masar gero, wadda tuni aka yi bayanin yadda ake samar da ita a ƙarƙashin 13.4 da ke sama.


[1]Kumbura

[2]Ɗanyar shinkafa ita ce wacce ba a turara/guma ta ba kafin a sussuke.

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments