Miyar Zogale
Miyar zogale miya ce da ake yi da ganyen zogale. Zogale bishiya ce da takan yi tsayi, wadda kuma take ɗauke da ganyaye ƙanana. Yawanci akan same ta a cikin gida ko bayan gidan Bahaushe. A wasu lokuta kuma, akan shuka wannan bishiya a gonaki.
Mahaɗin
Miyar Zogale
Akwai abubbuwan da za a tanada, idan
za a haɗa miyar zogale.
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv. Gyaɗa
v. Kayan yaji
vi. Magi
vii. Manja ko gyaɗa
viii.
Tumatur
ix. Ruwa
x. Tafarnuwa
xi. Tarugu
xii. Tattasai
xiii. Zogale
xiv. Nama ko kifi (idan akwai)
Yadda
Ake Miyar Zogale
Da farko za a samo zogale ɗanye a jiƙa shi
ya ɗan yi kimanin mintuna goma. Daga nan za a sanya kanwa ko
gishiri a wanke. Miyar zogale na da matuƙar kama da miyar alayyafu ta fuskar
yadda ake samar da ita.
Bambancin kawai shi ne, yayin da sanwa ta tafasa, a maimakon a sanya alayyafu,
a nan sai a zuba zogalen
da aka wanke sannan aka aje gefe tun farko. Daga nan sai batun sanya gyaɗa dakakkiya. Akan yi amfani da miyar zogale
yayin cin tuwon shinkafa ko na masara ko sakwara ko tuwon samo haka ma masa da
sinasir ko funkasau
da makamantansu.
Tsokaci
Wannan miya na da matuƙar amfani ga lafiyar jiki. Wannan ne ma ya sa da wuya a
samu wani gari a ƙasar
Hausa da ba a amfani da wannan miyar. Ko ma ba don miya ba, akan yi amfani da
zogale a matsayin magani yayin da aka sarrafa ta ta
hanyoyi daban-daban.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.