Akwai abubbuwan da ake tanada, idan za
a haɗa miyar alayyafu.
i. Alayyafu
ii. Albasa
iii. Daddawa
iv. Gishiri
v. Gyaɗa ko Egushi
vi. Kabushi
vii. Kayan yaji/ƙamshi da tafarnuwa
viii. Magi
ix. Mai
x. Ruwa
xi. Sure/yakuwa
xii. Tarugu
xiii. Tattasai
xiv. Tumatur
xv. Wake
Za a niƙa tumatur da tarugu da tattasai da kabushi da albasa a ɗan jefa ’yar kanwa kaɗan a aje gefe. A gefe guda kuma, za a tafasa nama da magi
da albasa. Idan ya dafu shi ma a a je shi a gefe. Idan kuma kifi ɗanye, za a ɗan tafasa shi da ɗan gishiri a zubar da ruwan a bar shi ya tsane. Idan kuma
busashe ne, za a zuba masa ruwan zafi a wanke shi sannan a cire ƙaya. Daga nan sai maganar yanka alayyafu
da kuma sure kaɗan.[1]
Yayin wanke waɗannan ganyaye, akan yi amfani da
gishiri.
Da za rar an kammala wannan, sai batun hura wuta da kuma aza tukunya. Akan saka man gyaɗa ko manja. Bayan sun ɗan soyu, sai a zuba albasa. Bayan sun soyu, sai a sanya jajjagen
tumatur a ciki a bar shi ya soyu sosai har mai sai ya fito sama, sannan a zuba
daddawa wadda
dama an daka ta tare da kayan yaji da tafarnuwa. Idan suka soyu za a yi sanwa a
saka nama da ruwansa. Idan ba a buƙata,
za a soya tumatur tare da naman. Za kuma a zuba sauran kayan miya irin su magi da gishiri.
Za a bar miyar ta dafu sosai yadda ko’ina za a iya jin ƙamshinta, wanda shi ne alamun nama ya nuna da har zai iya rabuwa da ƙashinsa. Sannan za a samu wuri a kwashe naman inda ba zai huce ba. Sai kuma a saka alayyafu da sure a cikin miyar. Idan ana buƙata za a iya niƙa alayyafun ko a daka a turmi in ba a buƙata a bar shi zai wadatar. Bayan an ɗan saka alayyafun da kimanin mintina biyar, za a zuba gyaɗa ko egusi. Kowane aka saka daga ciki ya wadatar. Wani lokaci ma wake ake sakawa. Idan ta nuna za a burkaka da maburkaki sannan a mayar da naman cikin tukunya ya ƙara jiƙa a ciki. Idan da wake za a yi amfani, to akan surfe waken tare da daka shi ko markaɗe shi sannan a zuba. Za a iya cin miyar da kowane tuwo kamar tuwon shinkafa da na masara da na samo da na sakkwara da na masa da kuma na ɓula da sauran su.
[1] A miyar alayyahu, akan zuba sure ne ɗan kaɗan ba mai yawa ba. Wani lokaci ma ba a
zubawa kwata-kwata.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.