Mahaɗin
Miyar Tumatur
Yayin samar da miyar tumatur, ana buƙatar kayan haɗi kamar haka:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kanwa/bakin foda
iv. Kayan yaji
v. Kori
vi. Lawashi
vii. Magi
viii. Mai
ix. Nama ko kaza
x. Ruwa
xi. Tarugu
xii. Tattasai
xiii. Tumatur
Yadda
Ake Miyar Tumatur
Za a tafasa nama (idan
akwai) tare da kori (da sauran kayan ƙamshi
irin waɗannan) da ɗan gishiri, a sauke in ya ya nuna. Daga nan sai a niƙa tumatur da tattasai da tarugu da
albasa. Kar a saka tarugu da yawa a wurin niƙa. Haka kuma, kar a niƙa tumatur luƙui-luƙui, a maimakon haka, za niƙa shi ne tsaka-tsaki. Yayin kai markaɗen yana da kyau a sanya ’yar kanwa ko bakin foda.
Bayan an dawo da shi
daga markaɗe, za a aza bisa wuta domin ya tsane. Daga nan kuma sai maganar
soyawa tare da kayan yaji. A lokacin saka kayan yaji, kada a saka su da sauri.
A maimakon haka, a bari sai tumatur ya fitar da wata kumfa ɗorowa ita ake kira (yami). Daga nan ne za a zuba kayan
yaji. Idan aka yi haka, to an fi jin ƙamshin
miyar sosai. A lokacin da jajjagen ya soyu, za a sake kwashe nama daga cikin
ruwa a haɗe da tumatur a ci gaba da soya su
tare. Idan tumatur ya ƙara
soyuwa za a yi sanwa da ruwan nama a saka magi. A
lokacin za a yanka lawashin albasa wanda da ma an riga an wanke shi, a saka ciki. Idan miyar ta dafu ta yi
kauri sosai, za a iya saukar da tukunya. Akan ci nau’o’in tuwo daban-daban da wannan miyar. Daga cikin nau’o’in tuwon da ake ci da ita sun haɗa
da tuwon masara, da taiba da tuwon shinkafa da
sakwara da semo da makamantansu.
Tsokaci
Kusan za a iya cewa, babu wani ɓangare daga ƙasar Hausa da ba a amfani da miyar tumatur. Za kuma a iya hasashen cewa, an fi samun irin wannan nau’in miya a bira ne, duk kuwa da yake ƙauyukan sun fi birane yawaitar tumatur.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.