Gabatarwa
A Æ™asar Hausa, bayan tuwo da miya, Hausawa kan iya sauya abinci domin samun wani É—anÉ—ano na daban. Hausawa na yin amfani da dabaru wajen sarrafa kayan abincin da ke kewaye da su ta É“angarori daban-daban domin samar da nau’o’in abinci iri-iri. Wannan ya sanya a har kullum, suke samun sababbin salailan sarrafa nau’o’in abincin da ya dace da muradansu. Dambu na É—aya daga cikin abincin Bahaushe da guguwar zamani ba ta yi awon gaba da shi ba. Wannan babi yana Æ™unshe da bayanai dangane da ire-iren dambu da Bahaushe ke amfani da su.
Ma’anar Dambu
Dambu, wani nau’in abinci ne da ake
sarrafa shi da gero ko dawa ko masara ko kuma shinkafa da dangoginsu, yakan kasance
wasar-wasar idan an kammala shi.
Yayin samar da dambu, akan niƙa (barza) ɗaya daga cikin waɗannan kayan haɗin da aka lissafa a sama, amma tsaki-tsaki ba niƙan laushi kamar na tuwo ba. Wannan ne ma ya sa a koyaushe dambu ke
kasancewa wasar-wasar. Baya
ga haka, akan sanya wasu nau’o’in kayan haÉ—i da suka shafi nau’o’in kayan lambu.
Idan aka lura da bayanin da ke sama,
za a fahimci cewa kayan haÉ—in dambu ba wani abu na daban ba ne
daga kayan haÉ—in abincin Hausawa da aka yi magana a sama (tuwo da miya). Kenan dai, salon sarrafa su ne ya
bambanta. Ko a cikin dambu, akan samu nau’o’i daban-daban wanda ya danganta da
kayan haÉ—in da aka sanya a ciki da kuma yanayin yadda ake
sarrafa su.
Kashe-Kashen Dambu
Kamar galibin
abincin Hausawa, dambu ya kasu kashi daban-daban. Akwai
dambu na gargajiya da kuma na zamani. Dambu na gargajiya shi ne wanda Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni. Ci gaban
zamani da aka samu da
kuma cuÉ—anya da baÆ™in al’ummu na kusa da na nesa, ya sa dambun Gargajiya ya sauya salo zuwa na zamani, musamman ta fuskar yanayin
sarrafawa da kuma na
É—anÉ—ano.
Wannan kuwa ba sabon al’amari ba ne ga dukkan al’ummun duniya, wato sauye-sauye a É“angarori daban-daban na
rayuwa, ciki har da nau’o’in abincinsu.
Dambun Gero
Yayin samar da dambun gero, geron ne kan kasance babban abin haÉ—i. Akwai kayan haÉ—i da akan tanada da suka haÉ—a da:
i. Albasa ii. Barkono (tonka) iii. Gero iv. Kanwa
v. Ƙulli vi.
Mai vii. Ruwa viii.
Rama ko Zogale
Da farko za a fece gero a tabbatar da an cire masa tsakuwa da duk wani haki da ke ciki. Daga nan sai a niƙa, kamar yadda aka gani cikin gabatarwa,
niƙansa zai kasance ɓarza ne ba gari ba.
A gefe guda kuwa, za a wanke rama ko zogale sosai a tsabtace ta sannan a dafa cikin
tukunya tare da kanwa kaÉ—an.
Baya ga haka, akan iya wanke rama ko zogale a aje kawai ba tare da dafawa ba.
Daga nan za a ɗauko niƙan ɓarzar da aka yi a wanke sannan a regaye
domin fitar da ƙasar da ka iya
samu a ciki. Da an kammala wannan, sai batun aza tukunya bisa wuta tare da ruwa. A bisa tukunyar za a sanya
madambaci/gittere. Daga nan za a aza wani faifayi ko marfin kwano da zai rufe huji-hujin
madambacin sannan a zuba gari. Abin da aka sanya cikin madambacin
shi zai hana É“arzazjen geron tsiyayewa cikin ruwan.
Kafin zuba É“arzajjen
geron cikin madambaci, sai an gauraya shi da ganyen zogale ko rama da aka tanada. Sannan za a yanka albasa a kai a barbaÉ—a gishiri sannan a yayyafa ruwa. Da zaran an
kammala wannan, sai a zuba cikin madambaci. A saman
madambacin akan sanya buhu ko leda (amma an fi son saka buhu), sannan a É—ora marfin tukunya a kuma É—ora wani abu bisa marfin kamar dutse.
Duk ana wannan ne domin kada tiririn ruwan ya samu hanyar ficewa.
Bayan an kammala waÉ—annan,
za a jira tukunyar har sai dambun ya dafu. Yadda ake gane dafuwarsa kuwa shi
ne, za a ji ƙamshi ya game
ko’ina, sannan tururinsa na É—an fitowa daga cikin tukunyar. Akan ci
wannan nau’in dambu da yaji da kuma mai, musamman
mangyaÉ—a.
Dambun Masara
Wannan ma wani nau’i ne na dambu da
ake yawan samu a ƙasar Hausa. Shi kuma ana amfani da masara ne yayin samar da shi. Akwai abubuwan da ake
tanada yayin yin dambun masara. WaÉ—annan abubuwa sun haÉ—a
da:
i. Alayyafu ii. Albasa iii.
Barkwano iv. Gishiri v. GyaÉ—a
vi. Ƙuli-ƙuli vii. Mai viii.
Masara ix. Ruwa
Shi ma dambun masara ana yin sa ne tamkar na gero, sai dai shi akan surfa masarar kafin a
niƙa; yayin da wasu kuma sukan jiƙa masarar kafin a kai niƙa. Idan an kai masara niƙa ba tare da an surfa ba, to akan bushe/heshe dusar bayan
an dawo da ita daga niƙa.
Shi ma wannan nau’in dambu akan ci shi ne da barkwano da kuma mai, musamman na
gyaÉ—a.
Dambun Tsakin Masara
Dambun tsakin masara na matuƙar
kama da dambun masara na kai tsaye. Dalili kuwa shi ne, dukkaninsu daga masara
ake samar da su. Sai dai shi dambun tsakin masara, ana samar da shi ne daga
tsaki. Wato yayin da aka tankaÉ—e garin masara domin yin tuwo ko wani abu mai kama da wannan, akwai wani tsaki da yake ragewa. To
irin wannan tsakin ne ake amfani da shi domin samar da dambun tsakin masara.
Wani bambancin da ake samu kuma shi ne, dambun tsakin masara ba ya son ruwa
sosai. Saboda haka, da zarar
tiriri kaÉ—an ya buge shi, to zai dafu. Kenan
dai, yana dafuwa da wuri idan aka kwatanta shi da sauran nau’o’in dambu da aka
yi misali a sama.
Dambun Shinkafa
Wannan kuma nau’in dambu ne da ake
samarwa daga shinkafa. Akwai kayan haÉ—in da ake tanada yayin wannan dambu waÉ—anda suka haÉ—a da:
i. Albasa ii. Gishiri iii. Kayan yaji
iv. Mai v. Nama
vi. Ruwa vii. Shinkafa viii. Tarugu ix. Tattasai x. Zogale
Shi ma dambun shinkafa a can da ana
yin sa cikin sigar da aka yi na masara ko gero. Wato ba a saka masa komai, sai an
gama za a saka mai da yaji sannan a ci. Dukkanin dambun gero da na masara dafuwa guda
ake musu a sauƙe su a ci.
Kammalawa
Kamar yadda aka gani a sama, dambu
abinci ne da ya fi kama da na ƙwalama.
Yawanci akan ci shi a marmarce, musamman idan an yi masa haÉ—i na a-zo-a-gani. An fi cin dambu a matsayin abincin
rana, komabayan dare ko safe. Kamar yadda bayanin ya zo a sama, yawancin
nau’o’in dambun da Hausawa ke samarwa ba su da wahala wajen
sarrafawa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.