Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Danwake Da Tubani a Abincin Hausawa

Gabatarwa

Wannan babi na goma sha ɗaya zai yi bayani ne game da yadda ake yin ɗanwake da tubani. An haɗe su wuri guda ne saboda makusanciyar kamanceceniyar da su ke da ita. Duk da haka, ɗanwake da tubani wasu nau’o’in abinci ne masu zaman kansu.

Yadda Ake Ɗanwake

i. Kanwa         

ii. Kuka           

iii. Kayan ɗanɗano

iv. Mai             

v. Ruwa          

vi. Fulawa ko alabo da wake da dawa

Akwai ɗanwaken da ake yi ta hanyar haɗa wake da dawa da alabo,[1] amfani da wake da ake yi a matsayin babban sinadarin haɗi, ana hasashen shi ne ya sa ake ce masa ɗanwake. Bayan an haɗa waɗannan kayayyaki, sai a daka a turmi ko kuma a niƙa su a dutsen niƙa ko kuma a injin niƙa (injimin rida). Idan dakawa za a yi, za a iya sanya kuka a daka su tare. Idan kuwa niƙa ne, akan niƙa ne haka nan bisa dutse ba tare da kuka ba, amma idan a inji ne akan sanya kukar. Da zarar an kammala, sai a tankaɗe. Idan haka ta faru, to za a sanya tankaɗaɗɗen garin kuka bayan an dawo daga niƙa. Daga nan kuma za a kwaɓa wannan gari tare da ruwan jiƙaƙƙiyar kanwa ba mai yawa ba. Wannan ruwan jiƙaƙƙiyar kanwar, shi zai mayar da kwaɓaɓɓen garin mai danƙo.

A gefe guda kuwa, za a ɗora ruwa bisa wuta. Bayan ya tafasa, za a riƙa ɗiban wannnan kwaɓaɓɓen garin ɗanwake da hannu ko da cokali ko kuma da wani abu makamancinsa ana sanyawa ƙanana-ƙanana cikin wannan tafasasshen ruwan da ke bisan wuta. Bayan an saka daidai adadin da tukunyar za ta iya ɗauka, sai a bar ta haka nan. Ɗanwaken zai riƙa samar da wani kumfa yayin da ruwan ke tafasa. Za a riƙa amfani da ludayi da ruwan sanyi kaɗan domin mayar da wannan kumfa da ke tasowa.

Yadda ake gane ɗanwake ya nuna shi ne, idan aka ɗauka aka sanya cikin ruwan sanyi, zai koma ƙasan ruwan. Wanda bai nuna ba kuwa, zai zauna a saman ruwan. Ana cin ɗan wake da mai da da gishiri da yaji. Wani lokaci ma akan ci shi da jar miya(miyar da ake cin shinkafa) ko miyar gyaɗa.

Yadda Ake Tubani

i. Rogo             

ii. Ganyen rogo ko na masara

iii. Kanwa       

iv. Kuka          

v. Wake

A wannan nau’in abinci, za a niƙa wake ne ko a daka shi, sannan a tankaɗe a saka garin kuka kaɗan a kwaɓa da ruwan kanwa. Ganyen rogo ko na masarar da aka samo, ana buƙatar a wanke shi domin ya samu cikakkiyar tsafta. Idan ganyen ya bushe, sai a riƙa zuba wannan kwaɓin da aka yi bisa ganyen ana naɗewa. Bayan an kammala sai maganar sanyawa a cikin tukunyar da aka sanya bisa wuta.

Kammalawa

Ɗanwake da tubani nau’o’in abinci ne sanannu a ƙasar Hausa. Kamar yadda aka bayyana a sama, wake shi ne babban sinadarin haɗin waɗannan nau’o’in abinci. Sai dai zamani ya zo da hanyoyi daban-daban da ake sarrafa su.



[1]Rogo da aka yayyanka aka shanya ya bushe. 

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments