Gabatarwa
Abincin garau-garau, abinci ne da za a iya dafa shi ba tare da an tuƙa shi ba, kuma za a iya cin garau-garau haka nan ba tare da miya ba. Sannan akan iya cin sa da wani abu daban ba da miya ba, kamar manja ko mangyaɗa. Garau-garau ba sabon abinci ba ne a ƙasar Hausa, yana cikin nau’in abincin da aka gada tun iyaye da kakanni. Sai dai a yau, akan samu nau’o’in garau-garau da zamani ya zo da su waɗanda suka bambanta da waɗanda aka saba da su.
Kashe-Kashen Garau-Garau (Wasa-Wasa)
Kamar yadda
nau’o’in abincin da aka lissafo a baya rukunan su ya kasu iri daban-daban, shi ma wannan nau’in abinci za a iya raba shi zuwa wasu
rukunai ta hanyar la’akari
da kayan haɗi da kuma yadda ake sarrafa shi. Ga wasu
daga ciki kamar haka:
Wasa-Wasar Dawa
i. Barkono
ii. Dawa
iii.
Gishiri
iv. Mai
v. Ruwa
Dawa za a surfe sosai, sai a wanke ta
sannan a bar ta ta tsane. Idan ta tsane, za a ɗora tukunya saman wuta a zuba ruwa a cikinta. Bayan ruwa ya tafasa sai a ɗauko dawar a zuba a ciki,
sannan a sanya gishiri a ci gaba da dafuwa. Idan ta dafu, za a sauƙe tukunyar ta ɗan
huce, sai a riƙa ɗiba ana ci da mai da yaji kamar yadda ake cin shinkafa.
Wasa-Wasar Shinkafa
i. Barkono
ii. Gishir
iii. Mai
iv. Ruwa
v. Shinkafa
Da farko, za a gyara shinkafar a wanke ta, sannan
a aza tukunya da ruwa bisa wuta. Bayan ruwan ya tafasa, sai a zuba
wannan shinkafar a ciki tare da ɗan gishiri daidai gwargwado.
Bayan shinkafar
ta dafu akan ci ta da mai da yaji ko kuma da miya idan da hali.
Wasa-Wasar Gero
i. Barkono
ii. Gero
iii.
Gishiri
iv. Mai
v. Ruwa
Yadda ake yin wasa-wasar dawa haka ake ta gero. Bambancin kawai shi ne, a nan ana
amfani da gero ne a maimakon dawa.
Wasa-Wasar Dambu
i. Mai
ii. Ɓarzazziyar Masara ko Shinkafa
iii. Ruwa
iv. Yaji
Akan dafa dambun masara ko na shinkafa haka nan ba tare da an saka
masa komai ba. Akan yi wannan dafuwa ne ta hanyar turara shi a madanbaci.
Idan an tabbatar da ya yi yadda ake so sai
a kwashe shi. Za a iya cin sa da mai da gishiri da Barkono (tonka). Haka kuma,
shi ma za a iya saka ganye da ƙuli-ƙuli a
yi kwaɗo da shi, kuma za a iya
saka masa miya idan ana buƙata a ci da shi.
Wasa-Wasar Burabusko
i. Barkono
ii. Burabusko (Ɓarzazziyar masara)
iii.
Gishsiri
iv. Mai
v.
Ruwa
Shi ma wannan nau’in dambu akan yi shi ne kamar yadda aka yi
bayanin sauran
da ke sama. Akan yi shi da ɓarzazziyar masara. Bayan ya kammala, akan sanya masa
mai da yaji domin a ci. Wani lokaci akan ci da miya.
Wasa-Wasar Wake
i. Barkono
ii. Gishiri
iii. Kanwa
iv. Mai
v. Ruwa
vi. Wake
Ita ma wasa-wasar wake duk lokacin da aka buƙaci yin ta ana wanke waken ne sannan a tsince
wanda ba shi da kyau. Idan ruwan da aka ɗora a saman wuta ya
tafasa, sai a zuba shi a saka ’yar kanwa da gishiri
a ciki, sai kuma a saurara har
sai ya dafu sosai. Akan ci da mai da yaji, ko kuma a sanya miya idan da hali.
Kammalawa
Nau’in abincin wasa-wasa, abinci ne mai sauƙin dafuwa ba tare da an saka kayayakin
lambu a wajen dafuwa ko cinsa ba. Duk da haka, akan samu waɗanda ke amfani da kayan lambun yayin cin wasa-wasa. Mafi
yawanci abinci ne da ake cin sa da mai da yaji. Wani lokaci kuwa akan sanya
miya, musamman a zamanin yau.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.