Ɗan Tama-Tsitsi
Kayan haɗin da za a tanada:
i. Garin ƙwame/Ɗan kuka
ii. Garura
iii. Suga
Ana samun ƙwame busasshe a fasa, sannan a daka har sai ya yi gari, sai a tankaɗe a cire ’ya’yan da zare-zaren da ke ciki. Daga nan za a tanadi suga da garura (garura na da launuka mabambanta) da kuma suga. Za a jiƙa su wuri guda gabaɗayansu. Damun da za a yi musu zai kasance mai ɗan kauri-kauri. Za a riƙa ɗiba ana ƙullawa ƙanana-ƙanana a cikin leda.
Ƙwanƙwalati (Kakan Daɗi)
Kayan haɗin da za a tanada:
i. Suga
ii. Tsamiya ko lemon tsami
Yadda ake samar da ligidi haka ake samar da kakan daɗi. Bambancin kawai shi ne, ba a sanya kakan daɗi cikin sanho. A maimakon haka, ana sanya shi ne cikin ƙwanƙwalati, wato marfin lemon kwalba. Wannan ne ma ya sa ake
kiran sa ƙwanƙwalati.
Alewar Madara (Tuwon Madara)
Kayan haɗin da za a tanada:
a. Madara Kwata
b. Ruwa
c. Suga
Za a samo suga da madara kwatankwacin kwata. Sugan za a ɗora shi ne a
wuta, sannan a zuba ruwa ɗan kaɗan. Tun kafin ya narke yake sauya launi, sai a zuba wannan madara a ciki. Haka za a ci gaba da juyawa har sai ya haɗe gaba ɗaya. A gefe a samu tire a shafa mai a
samansa sannan a juye wannan tuwon madara. Bayan ya ɗan huce kaɗan, sai a riƙa tsaga shi da wuƙa ko wani abu mai kama da wannan. Ana
yin sa ƙanana-ƙanana.
Garin Ɗan Buɗiɗis/Garin Buɗus
Kayan haɗin da za a tanada:
a. Bombita
b. Madara
c. Suga
d.
Ɗiyan ƙwame ko waken suya
’Ya’yan cikin ƙwame ake ɗorawa a wuta cikin tukunya a soya ba tare da mai ko ruwa ba. Za a yi ta
juya su ne kawai cikin tukunyar.
Daga nan za a daka shi har sai ya yi laushi. Sai kuma a zuba wa dakakken garin
madara da bombita da suga. Shi ma ana ƙullulle
shi ne a cikin leda ko takarda. Wani lokaci ana amfani da waken suya a maimakon
ɗiyan ƙwame.
Gugguru
Kayan haɗin da za a tanada:
a. Filebo
b. Madara
c. Masara
d. Suga
Za a gyara masara sannan a sanya ta cikin tukunya kan wuta ba tare da an sanya komai ba. Za a riƙa gaurayawa har sai ta tsattsage gaba ɗaya. Daga nan za a sauke ta, sannan a sanya filebo da
madara ta gari tare da suga. Za a gauraya gaba ɗaya su game ko’ina. Ana sanyawa cikin leda ko takarda ko
ma roba domin sayarwa.
Baba Dogo
Kayan haɗin da za a tanada:
a. Gyaɗa
b. Suga
c. Tsamiya
Za a soya gyaɗa a fece, sannan a kai markaɗe. A gefe guda kuma za a ɗora suga cikin tukunya a saman
wuta a bar shi har sai ya yi ja. Za a zuba tsamiya kaɗan cikin wannan suga. Bayan sugan ya koma ruwa-ruwa, sai a
zuba wannan markaɗaɗɗiyar gyaɗa
ciki a yi ta juyawa har sai ya yi jawur gaba ɗaya.
Daga nan za a shafa mai a kan faranti sannan a juye shi. Za a riƙa ɗiba
ana mulmulawa dogi-dogi (wato masu tsayi ba dunƙulallu ba). Wannan ne ma ya sa ake kiran sa da suna baba
dogo.
Fitsarin Abiyola
Kayan haɗin da za a tanada:
a. Fanta
b. Jolijus
Fanta ake saya tare da joli jus. Sai a jiƙa wannan joli jus, sannan a riƙa haɗawa
da fanta. Ana samun leda irin ta lalle wadda tana iya jawuwa ta ƙara tsayi ba tare da ta
katse ba. Ciki ake sanya
fanta kaɗan, sannan sai a saka jiƙaƙƙen
joli jus a ɗaure. Wannan shi ake kira fitsarin
Abiyola.
Ƙamƙam/Kantun Gana
Kayan haɗin da za a tanada:
a. Gyaɗa
b. Suga
c. Tsamiya
Gyaɗa za a soya a fece, sannan a ɗan daddaka ta sama-sama. A gefe guda kuma za a sanya suga cikin wuta. Bayan ya yi ja sai a zuba wannan gyaɗa ciki. Za a yi ta juyawa har sai ya haɗe gaba ɗaya. Daga nan sai a shafa mai kan tire
a juye ciki. Bayan ya bushe ne za a riƙa
ɓaɓɓalla shi daidai adadin girman da ake
buƙata.
Suya
i. Garin fulawa
ii. Gishiri
iii. Kayan yaji
iv. Magi
v. Mai
vi. Ƙwai
vii. Ruwa
viii. Tarugu
Za a kwaɓa
fulawa da gishiri, sannan
a mulmula ta curi-curi. A gefe guda kuma,
za a fasa ƙwai a sanya
masa gishiri da magi tare da jajjagen tarugu. Za a ɗora mangyaɗa a saman wuta, bayan ya yi zafi, sai a riƙa ɗauko wannan mulmulalliyar fulawar a
riƙa sanyawa a cikin ƙwan sannan a riƙa
soyawa cikin man. Da zarar an kammala wannan, to an samu suya kenan.
Karashiya (Ka Fi Amarya)
a. Mai
b.
Ƙwai
c.
Ƙwai da ƙwai/Awara
Da farko, za a yanka awara/ƙwai-da-ƙwai a shanya.
Bayan ya bushe, sai a ɗora
mai a wuta sannan a a fasa ƙwai a gefe guda. Za a riƙa sanya wannan busasshen awara a cikin ƙwai
ana soyawa tare da
mai.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.