Ticker

6/recent/ticker-posts

Faten Tsakin Masara Da Faten Shinkafa Da Faten Wake

Faten Tsakin Masara

Kayan haɗi sun haɗa da:

i. Albasa          

ii. Gishiri         

iii. Gyaɗa       

iv. Kayan ƙamshi      

v. Mai              

vi. Tarugu       

vii. Tattasai     

viii. Tsakin masara    

ix. Sure (yakuwa) da alayyafu

A duk lokacin da aka zo gudanar da wannan nau’i na fate, akan gyara tsakin masara tare da cire dusar da ke cikinsa. Daga nan za a yanka alayyafu da sure a kuma jajjaga tarugu da tattasai da albasa a soya da mai. Idan sun soyu za a saka gishiri da kayan yaji a yi sanwa da ruwa daidai gwargwado. Idan sanwa ta tafaso za a wanke tsakin masara a tsane shi a zuba a ciki. A gefe guda kuwa, za a wanke alayyafu da sure a saka a ciki a sake yanka albasa a zuba. Idan ya dafu za a ji ƙamshinsa, sai a sauke tukunya a zuba shi a faifayi a ƙara soya wani mai a saka a saman sa. Wanda bai son mai sosai kuwa, da zarar ya dahu haka shi ke nan, wato ba sai an ƙara mai a samansa ba.

Faten Shinkafa

Kayan haɗi sun haɗa da:

i. Albasa          

ii. Attarugu    

iii. Kayan ƙamshi       

iv. Kifi (idan da hali)

v. Lawashi (Ganyen Albasa)  

vi. Mai                        

vii. Shinkafa

viii. Wake        

ix. Yakuwa da Alayyafu

Za a gyara kayan miya a jajjaga su a ajiye su gefe, sannan a ɗauko mai na gyaɗa ko manja a soya a zuba kayan jajjage a ciki tare da kayan yaji. Idan ya soyu a zuba ruwa a ɗauko magi da gishiri a saka. Za a tafasa wake daban, a saka shi a cikin ruwan sanwa. Daga nan a wanke shinkafar da aka riga aka ɓarza a aje ta domin ta tsane. Sai kuma a yanka alayyafu da sure a wuri daban a saka gishiri kaɗan a wanke su sosai. Sannan a wanke shuwaka a dafa ta daban a tace, idan ta tsane sai a haɗe su da alayyafu da yakuwa. Za a ɗauko ɓarjajjiyar Shinkafa a riƙa zubawa a hankali ana jujjuyawa da muciya har sai an ƙare, sannan a ɗauko ganyen nan da ke aje a zuba ana juyawa da muciya. Za kuma a yanka albasa a saka, a kuma wanke kifi a zuba bayan an cire masa ƙaya. Za a sake juya faten da muciya, idan ya yi ƙarfi kuma ana iya ƙara ruwa a ciki idan an ga ruwan ba zai kai ba. Daga nan za a bar shi har sai ya nuna, inda za a sauke tukunya. An fi son a ci shi da ruwa-ruwa da kuma zafi.

Faten Wake

Kayan haɗi sun haɗa da:

i. Alayyafu     

ii. Albasa         

iii. Daddawa   

iv. Gishiri       

v. Kayan Yaji  

vi. Mai             

vii. Ruwa       

viii. Wake

A ƙarƙashin 22.2 da ke babi na ashirin da biyu an kawo bayani kan faten wake. A hirar da aka yi da Gwaggo Shuka, (2019) ta tabbatar da cewa, akwai bambance-bambance sosai dangane da yadda ake samar da faten wake a tsari irin na gargajiya da kuma yadda ake samar da shi a zamanin yau. A gargajiyance kayan haɗinsa ba su da yawa kamar yadda suke a zamanance, bugu da ƙari, a yanzu yawanci sai an tafasa waken an zubar da ruwan kafin a ɗora sanwar faten.

The book “Cimakar Bahaushe” (Diets of the Hausa People) is a collection of 293 traditional and modern diets of the Hausa people. Detailed explanations of the recipes and ingredients are provided. Comments are provided on the areas of the Hausa land where specific diets are mostly found, the age categories of people that usually use it, as well as the scientific impact of some of the diets to human biology.  Data is collected from interviews with different categories of people including:  i.                    Food sellers within the Hausa land: Mainly to have an idea of recipes on the diets.  ii.                  People of older age: Mainly to have insights on traditional diets of the Hausas.  iii.               Hausa scholars: Mainly to verify and justify the validity of the information obtained as well as provide further expert explanations on the diets.  Moreover, over two hundred (200) pieces of literature were reviewed to have better insight on the topic in question as well as get scientific and professional clarifications on some key concepts relevant to the research. The pieces of literature cover major relevant phenomena such as diet and hunger. Others are on the Hausa land and the Hausas.  The book contains thirty-three (33) chapters. Chapter one is the main introduction in which a concise explanation is provided on the Hausas, their history, their land, social life, and transformations due to globalization, acculturation, and modernity. Chapter two detailly discusses the concepts of diet and food from the Hausa point of view. That includes the meaning and the usage of diets in some Hausa works of literature both verbal and written (i.e. prose, poetry, proverbs, etc.).  Chapters three and four discuss the sources of Hausa diets and their forms accordingly. Chapters five to seventeen discuss some traditional Hausa diets including hard and soft ones. Chapter eighteen concentrates on the influence of modernity and globalization on Hausa diets. It has been discovered that there have been some significant changes in the Hausa diets ranging from recipes to kitchenettes.  Chapters nineteen to thirty-two discuss modern Hausa diets. Some traditional diets are still retained with little modifications, while on the other hand, there are a lot of new ones. Chapter thirty-three discusses “hunger” from the Hausa point of view. The relationship between hunger and food is examined. Additionally, the use of hunger in various Hausa literary works is studied. It is concluded that hunger is like a disease whereby its cure is food.  7th November 2022
Citation (Manazartar Littafin): Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

abuubaidasani5@gmail.com 

Post a Comment

0 Comments