Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Aure Da Ta Samu Ciki Ta Hanyar Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam barka da dare. Malam ni mai laifice Kuma laifin babba. dan Allah malam wlh na yi nadama na yi dana sani kullum cikin neman yafiyar Allah nake yi na aikata laifin zina da aurena yayin da na tuba na koma neman gafarar Allah kawai na gane ina dauke da ciki Kuma na san ba nasa ba ne malam mene ne makomar wannan cikin malam ina cikin damuwa na rasa yadda zan yi da cikin nan ina neman fatawarka malam Dan Allah yazama sirrin tsakaninmu. Ga shi yana son cikin mijina saboda ba mu taɓa haihuwa ba yan uwansa Sun sani a gaba suna kirana juya ni yanzu ban san yadda zan yi ba dan Allah a taimaka min

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh

Babu makawa abin da kin aikata na zina kina matar aure yana cikin manyan laifuka, ko da zina zunubi ce maigirma ita kaɗai to girman zunubin nakaruwa idan aka ce mai aure ta yi zina, shiyasa ma hukuncin mazinacin da bai taɓa aure ba shi ne bulala 100, wanda kuma yake da aure ko yataɓa aure shi ne ajefeshi harsai ya mutu.

Hakika kin tafka babban kuskure. Domin zina tana cikin Kaba'irori wato zunubai mafiya girman laifi a wajen Allah. Awani hadisi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa ya yi "Bayan yin shirka da Allah, babu wani zunubi mafi girman laifi kamar maniyyin da namiji ya sanyashi a cikin mahaifar matar da ba ta halatta gareshi ba".

Duk macen da ta yi zina alhalin tana da aure haƙiƙa ta ci amanar mijinta, kuma ta tonawa 'yaƴanta da danginta asiri, saboda duk wani mutum kirki zai ƙyamaci auren 'yaƴanta don gudun gori daga bakunan mutane. Kuma ga babban cin mutuncin da ta yi wa mijinta wanda tabbas sai Allah ya bi ma sa haƙƙinsa a ranar alƙiyamah matuƙar be yafe mata ba. Saboda haka ki nemi yafiya a wajen mijinki cikin salo ba tare da ya gane abin da kika aikata ba.

An tambayi SHAIK BIN BAAZ dangane da matar datake da aure sai ta samu ciki ta hanyar zina, shin ya halatta ta zubda cikin ɗan? ko za ta kyaleshi, idan ta kyale cikin shin za ta baiwa mijinta labari ko ba zata bashi ba? sannan mene ne yake wajibi akan mijin a wannan halin?

Sai ya amsa dacewa: Bai halatta agareta ta zubda wannan cikin ba, abin da yake wajibi akanta shi ne tuba zuwa ga Allah maɗaukakin sarki, da kuma kin bayyana al'amarin, ɗan da ta haifa kuma za a jinginawa mijinta ma'ana ɗansane, saboda faɗin Annabi sallahu Alaihi wasallam (Ɗa na mai aure ne mazinaci kuma uƙuba ce kawai tasa) Ma'ana wanda yai zina baida hakkin ajingina ɗan gareshi, shi kawai uƙubar zinarce akansa. Fatawa bin baaz (21/205).

Da wannan majalisar fatawa ta kasar saudiyyah tai fatawa, Allah yagyara halayen mu gaba ɗaya.

Tare da girman laifin da kika aikata da muninsa a al'ada da kuma hankali, babu wanda zai shiga tsakanin Allah da bawansa, Allah yana farin ciki da tuban bawa kuma yana karɓar tuban, Allah maɗaukakin sarki Ya ce:

قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ

Ka ce: (Allah Ya ce): ''Ya bayĩNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rayukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gafarta zunubai gaba ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gafara, Mai jin ƙai.' (Suratul Zumar Aya ta 53).

Ibnu kasir rahimahullah Ya ce: Wannan aya tana kirane ga dukkan masu saɓo harda kafirai su tuba su koma zuwa ga Allah, tana kuma ba da labarin Allah yana gafarta zunubai baki ɗaya ga duk wanda ya tuba yadawo daka aikata laifukan, komai irin yawansu da girmansu ko da sunkai yawan kumfar kogi, matukar an yi tuba nagaskiya Allah yana gafarta su.

Amma nasabar ɗan za a jingina shi ga mijinki na aure ne, matukar yasadu dake, saboda faɗin Annabi sallallahu Alaihi wasallam daya ce: (Ɗa na me aurene) ma'ana ɗan na mijin dakike aure da shi ne ko da ba a saduwa da shi cikin ɗan ya shiga ba, in dai kin kwanta da mijin bayan zinar ɗan na sane.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments