Sanga-sanga ganye ne ba mai tsawo sosai ba, sai dai kuma yana da faɗin kunuwa. Da an zo da shi za a ji warinsa kai tsaye. Yana da zaƙi-zaƙi idan aka ci shi a baki. Wannan ganye na matuƙar kama da tafasa, sai dai ya fi tafasa faɗi da ƙarfi. Har wayau, yakan rayu a wurin da tafasa take iya rayuwa.
Mahaɗin
Miyar Sanga-Sanga
Kayan haɗin
da ake tanada yayin samar da miyar sanga-sanga sun haɗa da:
i. Albasa
ii. Daddawa
iii. Gishiri
iv.
Kabushi
v. Kayan yaji
vi. Mai
vii. Ruwa
viii.
Ganyen Sanga-sanga
ix. Tarugu
x. Tattasai
xi. Tumatur
xii. Wake
Yadda Ake Miyar Sanga-Sanga
Akan sarrafa miyar sanga-sanga ne
tamkar yadda ake miyar alayyafu ko tafasa ko zogale, da dangoginsu. Akan iya sanya kabushi a cikin
wannan miya domin ya ƙara
mata ɗanɗano.
Tsokaci
Sanga-sanga miya ce da ita ma take da matuƙar muhimanci ga al’umma ta fanin kiwon
lafiya. Akan yi amfani da ganyen sanga-sanga a wajen warkar da ciwo, musamman
irin ciwon zazzaɓin cizon sauro da makamantansu. Wannan
ya sa birni da ƙauye ake
amfanin da miyar sanga-sanga. A garuruwan ƙasar
Hausa kusan ba inda ba a amfani da miyar. Sai dai an
fi amfani da ita a ƙauyuka sama da yadda
ake amfani da ita birane.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.