Miya mahaɗi ce ga tuwo da sauran nau’o’in abinci da ke da buƙatar amfani da miyar. Nau’in mahaɗin abinci ce mai ruwa-ruwa, wanda ake samar da ita ta hanyar amfani da wasu mahaɗai kamar tumatiri da tattasai da attaruhu da sauran kayan haɗin miya a cikin ta. Nau’o’in mahaɗan miya yana danganta ne ga nau’in miyar da ake so a samar. A ɓangare guda kuma, za a iya kallon miya a cikin abin da ke gyara tuwo. Domin duk daɗin tuwo, ba ya ciwuwa idan dai babu miya. Yayin da miya ta yi daɗi kuwa, ba a ma gane daɗin tuwo ko rashin daɗinsa. Malam( Dr.) Aliyu Namangi Zariya ya furta wani abu dangane muhimmancin miya a abinci a waƙensa na Infiraji inda yake cewa:
.....................................................
Wanda ke da uwa a murhu,
Ba zai ci tuwonsa ba miya ba.
Wannan babi ya karkata ne
ga duban iri-iren miya da ake samu a ƙasar
Hausa. Wasu daga cikin irin waɗannan miyoyi na gargajiya ne. Wato Bahaushe ya taso ya tarar da ana yin su a muhallinsa,
sannan akan samu kayan haɗinsu a muhallin nasa; tamkar dai yadda
akan ga bishiyar kuka ko’ina a ƙasar
Hausa. Wasu nau’o’in kuma na miya, Bahaushe ya same su ne daga wasu al’ummu da
yake mu’amala da su na kusa da na nesa.
Al’ummun kusa sun haɗa da, Fulani da Yarbawa da kuma
Igbo (Inyamurai). Al’ummun nesa kuwa sun haɗa
da Larabawa da kuma Turawa. A duba NAN.
Haƙiƙa, Bahaushe yana da nau’o’in miya daban-daban da yake amfani da su yayin da aka yi la’akari da bayanan da suka gabata. Wasu daga cikin waɗannan ire-iren miya ya gaje su ne tun iyaye da kakanni. Yayin da waɗansu kuwa, ya same su ne daga baya, a sakamakon cuɗanyarsa da baƙin al’ummu na kusa da na nesa. Baya ga haka, za a lura cewa Bahaushe na amfani da wasu daga cikin nau’o’in miyoyi a matsayin magani. Da ma dai, Bahaushen mutum sananne ne ta ɓangaren yi wa kansa tanadin magungunan cututtukan da ke damunsa, walau na jiki ko na zuciya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.