Kwaɗon Sure Ko Soɓorodo
Wannan nau’in kwaɗo na buƙatar wasu kayan miya kamar haka:
i. Albasa
ii. Barkono (tonka)
iii. Gishiri
iv. Mai (idan an ga dama)
v. Ƙuli
vi. Ruwa
vii. Sure(yakuwa)
viii. Tarugu
Za a iya amfani da sure ɗanye ko busasshe a duk lokacin da aka ƙuduri niyyar gudanar da wannan nau’i na kwaɗo. Idan ɗanye ne za a wanke a dafa shi a saka kanwa. Idan kuma busashe ne za a zuba shi a cikin tukunya a ɗan dafa shi a tace ya tsane. Haka shi ma soɓorodo dafa shi za a yi sosai ya dafu. Ana iya yi da soɓorodo mai launin ja ko fari, amma soɓorodo mai launin fari ya fi daɗin kwaɗo. Sannan za a daka ƙuli-ƙuli da barkono (tonka) a ciki, a sake jajjaga tarugu da albasa a saka a ciki a haɗe su gaba ɗaya. Sannan za a saka mai da gishiri. Abin da ya sa ake saka tarugu da barkono (tonka) saboda shi kwaɗon sure ko soɓorodo yana da yami. Idan ya yi yaji zai rage masa yami musamman ga wanda ke buƙatar yaji sosai. Shi ma sure idan ana buƙata za a iya haɗa shi da ƙanzo ko ɓula ko shinkafa wara ko tuwo a wurin kwaɗonsa.
Kwaɗon Rama
Yayin samar da wannan nau’in kwaɗo, akan tanadi kayan haɗi da suka haɗa:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Gyaɗa
iv.
Mai (idan an ga dama)
v. Ƙuli
vi. Rama
vii. Ruwa
viii. Tarugu
A yayin samar da kwaɗon rama, za a tanadi rama dafaffiya sannan a
tsince ‘yan kararen da ke ciki a wanke ta sosai. A wurin kwaɗo (ɗatu)
za a kwaɓa gyaɗa tare da ƙuli-ƙuli a haɗa da
sauran kayan haɗi. Har wa yau,
za a iya haɗa rama da ɓula da ɗata ko a haɗa rama da ƙanzo ko da tuwo ko shinkafa yayin kwaɗantawa. Haka ma, idan ɗanyar rama za a dafa, sai an ɗauko ramar
an wanke ta a cikin ruwa sannan a
saka ta a tukunya a zuba ruwa sai a tafasa ta. Za a tafasa ta a ƙalla kamar sau biyar, kuma ana yi ana tacewa tare da sauya ruwa.
Za kuma a sake samun wani ruwan zafi a ƙara
ɗauraye ta da shi, sai a tace. Daga nan sai a tsane ta domin
raba ta da ruwan da ke jikinta. To da wannan dafaffiyar ramar ne ake kwaɗo, inda ake sanya dakakken ƙuli-ƙuli
da kayan ɗanɗano
da kuma yankakkiyar albasa.
Kwaɗon Tafasa
Ganyen tafasa shi ne mafi rinjaye fiye da
sauran kayan haɗi yayin samar da kwaɗon tafasa. Kayan haɗin wannan nau’in kwaɗo sun haɗa da:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kayan yaji
iv.
Ƙuli
v. Ruwa
vi. Tafasa
vii. Tarugu
viii. Tumatur
Kwaɗon tafasa shi ma kamar sauran kwaɗo ake yin sa. Da farko, za a tsaftace ganyen tafasar ta hanyar
cire dukkanin hakin da ke tattare da shi. Saboda hakin na iya kasancewa illa ga lafiya.
Bayan an wanke tafasa sarai, sai a zuba mata ruwa, wanda a
nan an fi buƙatar a yi
amfani da ruwan zafi. Za a bar ta na tsawon lokaci sannan
a matse ta. A lokacin
ne duk wata
ƙasa da datti da ke jikinta za ta kau. Da zarar haka ta samu, sai batun
sanya kayan haɗi kamar yadda aka lissafo su a sama.
Kada a manta, wannan ana magana ne game da lokacin da aka sayi
dafaffiyar tafasa. Idan kuma a gida za a dafa ta, akan wanke ta sosai a tsafta
ce ta kafin ma a fara dafawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.