Wannan ma na ɗaya daga cikin nau’o’in miyar da Bahaushe ya karɓa hannu-biyu-biyu saboda alfanun da ke da ita. Ƙuli-ƙuli shi ne babban kayan haɗi yayin samar da wannan miyar. Kayan haɗin da ake amfani da su, su ne:
i. Barkono
ii. Gishiri
iii. Ƙuli-ƙuli
iv.
Mai
v. Ruwa
vi. Tarugu
vii. Tattasai
viii. Tumatur
Yadda
ake Miyar Ƙuli-Ƙuli
Yayin da ake ƙoƙarin samar da miyar ƙuli-ƙuli, da farko za a ɗora mai bisa wuta. Yayin da ya yi zafi, sai a sanya niƙaƙƙun
(ko jajjagaggun) kayan miyan da aka tanada (kamar tumatur da tarugu da tattasai).
Bayan sun soyu, sai a sanya ruwa. Za a bar wannan ruwan har sai ya fara tasafa.
A gefe guda kuwa, za a daka ƙuli-ƙuli. Bayan ruwan da aka sanya ya tafasa, sai a zuba wannan dakakken ƙuli a ciki. Za a rufe tukunyar a bar shi ya yi ta dahuwa, har sai ya haɗe gaba ɗaya. Yayin da miyar ta dahu, za a tarar ta yi kauri sosai.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.