Kwaɗo a ƙasar Hausa ya kasu kashi-kashi. Wannan kuwa ya shafi hanyoyin da ake sarrafa shi da kuma kayan haɗin da ake amfani da su. A nan, za a kawo wasu daga cikin nau’o’in kwaɗon da ke a farfajiyar ƙasar Hausa, tare kuma da taƙaitaccen tsokaci a kan kowanne daga cikin su.
Kwaɗon Shinkafa Da Alayyafu Ko Zogale Ko Tafasa Ko Sanga-Sanga
Irin wannan kwaɗo akan dafa shinkafa ne dafuwar wasa-wasa kafin a yi shi. Bayan ta dafu,
sai a kawo kayan haɗi a kwaɗanta.
Kayan haɗin da ake amfani da su sun kasance
kamar haka:
i. Albasa
ii. Tattasai
iii. Gishiri
iv. Gyaɗa
v.
Tarugu
vi. Ƙuli
vii. Ruwa
viii. Shinkafa
ix. Mai (idan an ga dama)
x. Allayahu ko zogale ko tafasa ko
sanga-sanga (da makamantansu)
Kwaɗon Garin Kwaki Da Salat ko Zogale ko Tafasa ko Rama
Garin kwaki ma akan kwaɗanta shi da ɗaya daga cikin nau’o’in ganyaye da aka
lissafa a sama. Da fari ana jiƙa
garin ne, sannan a shanya shi ya ɗan sha iska bayan an tace ruwan da ke cikinsa. Abuna gaba, sai a haɗa shi da kayan haɗi a gauraya kamar dai yadda ake sauran nau’o’in kwaɗon da aka yi bayani a sama. Kayan haɗin da ake amfani da su sun ƙunshi:
i. Garin Kwaki
ii. Gishiri
iii. Mai (in an ga dama)
iv. Ƙuli
v. Ruwa
vi. Tumatur
vii. Tarugu
viii. Salat ko zogale ko tafasa ko rama
Kwaɗon Gayan Tuwo
Wannan ma nau’in kwaɗo ne da ake gudanarwa a ƙasar Hausa. Ana amfani da gayan tuwo wajen sarrafa shi. An fi yin wannan kwaɗo a yanayi irin na lalura, wato yanayin da miyar tuwo ta ƙare alhali akwai sauran gayan tuwo kuma ana
da buƙatar cinsa a
matsayin abinci. A irin
wannan yanayi, akan yayyanka
gayan tuwon da wuƙa ko cokali ko
a gutsuttsura shi da hannu. Daga nan sai a sanya masa gishiri da barkono a
gauraya. Wani lokaci har akan sanya mai ko kalwa. Da zamani ya zo, akan yanka
kayan lambu a cikin
wannan nau’in kwaɗo. Bayan haka kuma, akan ƙara masa kayan ƙanshi da na ɗanɗano da suka ƙunshi nau’o’in magi da dangoginsu.
Tsokaci
Kamar dai yadda aka gani a sama, kwaɗo/ɗatu ya kasance nau’o’i daban-daban. Duk da cewa akan yi kwaɗo domin rashi ko toshe yunwa, sau da dama kwaɗo na kasancewa abin marmari, musamman yayin da aka sanya kayan haɗi sosai. Wani abin da yasa ake son kwaɗo shi ne sauƙin sarrafawa da kuma kasancewarsa abincin gaggawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.