Ire-Iren Kwaɗo (Gwaɓe/Ɗatu)
da Yadda Ake Yin Su a Gargajiyance
Gabatarwa
Kwaɗo dai na daga cikin nau’in abincin da Hausawa suka tashi suka tarar a
garuruwansu. Wannan
nau’in abinci, yana ƙunshe da nau’o’i masu yawa
kuma mabambanta. Duba da
faɗin ƙasar Hausa,ire-iren
kwaɗo na bambanta daga wuri zuwa
wuri. Wani lokaci akan
samu bambancin kayan haɗi ko hanyar sarrafawa wadda
hakan kan haifar da banbancin ɗanɗano.
Kwaɗo abinci ne mai sauƙi
da Bahaushe ya fi yi a matsayin abincin rana. Wasu lokutan
kuwa, akan yi kwaɗo a matsayin abincin dare ko ma na
safe wato kumallo. Akwai nau’o’in kwaɗo da dama da ake yi a matsayin abinci yayin da
ake buƙatar hakan. Sai
dai a wasu lokutan, akan yi kwaɗo ne saboda yanayi irin na rashi (don haka aka fi
danganta shi ga talakawa marasa wadata).
A bisa wannan dalili, kwaɗo
kan kasance mafita ga mai
neman abincin da zai toshe masa yunwar da ke damunsa. Ba mamaki wannan na da
dangantaka da kirarin da Bahaushe ke yi wa zogale, kasancewarsa ɗaya daga
cikin ganyayen da ake yawaita kwaɗo da shi:
Zogale gamji mataimaki,
Ana figar ka kana tsira.
Ma’anar Kwaɗo (Gwaɓe Ko Ɗatu)
Kwaɗo nau’in abinci ne da galiban ba ya buƙatar a dafa shi irin yadda ake dafa abinci na
yau-da-kullum. Sai dai
akan samu lokacin da ake amfani da sauran wani nau’in abincin na daban da aka
dafa kamar ƙanzon tuwo da makamantansu, ko wani ganye da aka dafa
kamar zogale ko rama da makamantansu. A taƙaice, kwaɗo nau’in abinci ne da ya shafi cakuɗawa ko gauraya kayan haɗinsa
ba tare da an ɗora shi a wuta domin dafawa ba. Kai tsaye ake yin sa, sannan
a ci shi da sanyi ba tare da wata dafuwa ba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.