Kwaɗon/Ɗatun Zogale
Kwaɗon zogale na ɗaya daga cikin nau’o’in kwaɗo da aka fi gudanarwa a ƙasar Hausa. Kusan za a iya cewa, yadda ake kwaɗon zogale haka ake yin na tafasa. Yayin samar da shi, akan tanadi kayan haɗi da suka haɗa da:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kayan yaji
iv.
Mai (idan an ga dama)
v. Ƙuli
vi. Ruwa
vii. Tafarnuwa
viii. Tarugu
ix. Tattasai
x. Tumatur
Kwaɗon Tuwon Dawa Ko Masara Ko Shinkafa
Yayin samar da wannan kwaɗo, ana buƙatar kayan haɗi kamar haka:
i. Albasa
ii. Barkono (tonka)
iii. Gishiri
iv. Mai (idan an ga dama)
v. Ƙuli
vi. Ruwa
vii. Tuwo
Akan yi wannan kwaɗo ne da tuwon da ya saura. Zai iya kasancewa tuwon gero ko dawa ko shinkafa da makamantansu. Yayin da za a yi
kwaɗon, akan gutsuttsura gayan tuwon ko dai da hanu ko da wani abu na daban
kamar cokali ko wuƙa. Daga nan sai
a sanya kayan haɗi kamar yadda aka lissafo su a sama.
Kwaɗon Ƙanzo
Ƙanzo, sauran tuwo ne da yake maƙalewa a ƙasan tukunya yayin da ake tuƙa tuwon, wannan ya sanya babu
wurin da ake samunsa sai
a ƙasan tukunya, wato wanda ya laƙe a jikin tukunya bayan an kwashe
tuwo. Irin wannan ƙanzo da shi ne ake kwaɗo. Akwai waɗanda ke kwaɗanta shi a ɗanyensa, akwai kuma wanda
akan bar shi ya bushe sannan a kankare shi daga jikin tukunyar a
sarrafa. Irin wannan ƙanzon da ya bushe, akan jiƙa shi ne yayin kwaɗo. Yayin samar da kwaɗon
ƙanzo, ana tanadar kayan haɗi kamar haka:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kayan Yaji
iv. Mai
v. Ƙanzo
vi. Ƙuli
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix. Tumatur
Kwaɗon/Ɗatun Ɓula
Wannan nau’i ne na kwaɗo da ake samarwa daga ɓula. Ɓula kuwa akan sarrafa ta ne kamar tuwo, tamkar dai yadda aka yi bayaninta a
sama. Yayin da aka samo ɓula, akan yayyanka ta sannan a kwaɗanta. Kayan haɗin da ake amfani da su sun haɗa da:
i. Albasa
ii. Ɓula
iii. Gishiri
iv. Gyaɗa
v. Kayan
yaji
vi. Mai (idan da hali)
vii. Ƙuli
viii. Ruwa
ix. Tarugu
Kwaɗon Tumatur
Shi ma tumatur akan kwaɗanta shi a ci. Yayin samar da wannan nau’i na kwaɗo, akan samu tumatur masu kyau a
yayyanka. An fi so a samu tumatur mai nama sosai (ma’ana wanda ruwan cikinsa kaɗan ne). Akan tanadi kayan haɗi kamar su:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Mai (in an ga dama)
iv.
Ƙuli
v. Ruwa
vi. Tarugu
vii.
Tumatur
Kwaɗon Tuwo da Alayyafu ko Zogale ko Tafasa ko Sanga-Sanga ko Yaɗiya
Wannan kwaɗo daidai yake da kwaɗon gayan tuwo da aka yi bayani a sama. Bambancinsu kawai shi
ne, a nan akan sanya wani nau’i na ganye, musamman zogale ko rama ko tafasa ko kuma sanga-sanga(majamfari). Saboda haka, kayan haɗin na iya kasancewa kamar haka:
i. Albasa
ii. Barkono (tonka)
iii. Kayan yaji
iv. Mai (idan an ga dama)
v. Ƙuli
vi. Ruwa
vii. Tuwo
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.