Furar Gero Da Furar Maiwa Da Furar Shinkafa

    Furar Gero

    i. Gero             

    ii. Kayan yaji             

    iii. Nono

    iv. Ruwa         

    v. Ma É— i ko Zuma (idan an ga dama)

    Za a surfe  gero  a wanke  domin a cire dusa r da ke jikinsa, sannan a ajiye shi ya tsane. Daga nan za a sanya kayan Æ™ amshi domin a daka. Za a iya rage wani adadi na geron kafin a kai ni Æ™ a. Bayan an kammala, za a tanka É— e garin. Sai kuma a ha É— e garin da surfaffen geron da aka rage ( ajiye ) lokacin da za a kai ni Æ™ a . Sai dai za a rage gari  ka É— an a jiye gefe guda. A wannan  ga É“ a akan samu za É“ i guda biyu, ko dai dambu ko kuma gumba.

    Ga masu yin dambu, za a zuba wannan  gari  da surfaffen gero  cikin turmi  sannan a yi amfani da ta É“ arya domin sake rib É— awa. Sannan za a É— an yayyafa masa ruwa domin y a harha É— e ka É— an. A gefe guda kuwa , an aza tukunya  da ruwa a bisa wuta . Da zarar ruwan ya fara tafasa, sai a ri Æ™ a É— auko wannan gari ana dun Æ™ ulawa domin tsomawa cikin tukunyar. Kafin a sanya, za a É— an hu d a dun Æ™ ulen da yatsa wanda hakan ne zai ba wa ruwan zafin damar ratsawa ko’ina. Bayan an kammala sakawa, za a rufe tukunya domin a bar shi ya dahu. Yadda ake gane ya dahu kuwa shi ne, zai taso sama. Bayan ya nuna , za a cire a sanya shi cikin turmi. Za a yi ta dakawa tare da Æ™ ara ruwan zafi  har sai ya yi laushi sannan ya yi dan Æ™ o. Daga nan za a juye cikin Æ™ warya , sannan a sake juya shi , s ai kuma a fara yanka wa  da hannu ana mulmulawa ana ajiyewa cikin wata Æ™ warya daban. Bayan an kamala , sai a É— auko garin nan da aka rage sannan a zuba kai, a jujjuya domin kowane Æ™ wallon dawo ya zama ya baibaiyu da garin.

    Idan kuma dawon gumba za a yi, bayan an dawo daga ni Æ™ a za a tanka É— e a ha É— a garin da geron da aka rage. Daga nan za a sanya cikin turmi . A wannan  karon za a kir É“ a ne ba dakawa ba. Ma’ana , za a sanya ruwa ne adadin da zai ba da damar garin ya k ir É“ u, duk ya ha É— e. Daga nan sai a duddun Æ™ ula a sanya cikin tukunya  kan wuta . Sauran yadda ake Æ™ arasa wannan nau’in dawo, daidai yake da na dambu kamar yadda aka bayyana a sama. Akan sha dawo da nono da suga ko kuma da zuma.

    Furar Maiwa

    i. Maiwa         

    ii. Nono

    iii. Ruwa         

    iv. Ma É— i ko Zuma (idan an ga dama)

    Yadda ake furar gero  haka nan ake t a maiwa . Bambancin kawai da ke tsakanin su shi ne, a nan ana amfani ne da maiwa a maimakon gero. Ita ma wannan  nau’in f ur a ana shan ta da da nono ko da suga ko kuma da zuma.

    Furar Shinkafa

    i. Kayan yaji              

     ii. Nono           

    iii. Ruwa

    iv. Shinkafa                

    v. Ma É— i ko Zuma (idan an ga dama)

    Za a gyara shinkafa r a wanke , sannan a sanya kayan Æ™ amshi ciki a kai ni Æ™ a. Bayan an dawo daga ni Æ™ a za a tanka É— e garin sannan a sanya a turmi  a rib É— a shi. Za a É— an yayyafa masa ruwa ka É— an daga nan sai a duddun Æ™ ula. A wannan  ga É“ a za a nasa shi cikin ruwan zafi  kan tukunya  kamar yadda ake na gero . Sai dai a nan za a bar shi ya dahu sosai. Bayan ya nuna za a sake sanyawa cikin turmi domin a kir É“ a. Daga an kwashe , sai a cuccura, sai kuma damu. Shi ma akan sha da nono ko madara da suga ko kuma da zuma. 

    Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.