Kunun Gero Da Kunun Sabara Da Kunun Sanga-Sanga Da Kunun Aduwa Da Kunun Shinkafa Da Kunun Kanwa

    Abubuwan Da Ke Ciki

    Kunun   Gero   (Kunun Tsaki)

    i. Gero            

    ii. Kayan yaji

    iii. Ruwa         

    iv. Ma É— i

    Za a surfa gero  a wanke , sannan a cire masa dusa r da ke jikinsa . Daga nan za a sanya shi ya bushe , sai kuma a sanya masa kayan yaji. Daga cikinsa ne kuma za a É— ibi wani adadi a ajiye a gefe guda. Sauran da ke ha É— e da kayan yaji nau’in barkono da citta da kanamfari da makamantansu, za a daka. Bayan an daka, za a tanaka É— e shi a fitar da tsakin gefe. Wannan tsaki n ne kuma za a yi ta regaye shi (wankewa) har sai ya zama fari tas, wato duk dusa r da sauran hak ukuwan da ke jikinsa sun fita. Da zarar wannan  ya samu, za a ha É— a geron da aka rage kafin a daka su tare da wannan tsaki  da aka wanke aka regaye. Za a kwa É“ a su tare da shi kansa tanka É— a É—É— e n garin da aka ajiye. Wannan ita ake kira gumba.

    A wannan  ga É“ a akwai za É“ i guda uku da suka ha É— a da:

    a.       Za a iya dama kunun nan take

    b.      Za a iya barin gumbar ta kwana kafin a dama kunu

    c.       Za a iya shan gumbar haka nan ba tare da an dama kunu ba

    Idan a nan take za a yi kunu n , to akan ji Æ™ a tsamiya  domin a kwa É“ a wannan  gumba da ita. Kafin a kwa É“ a , za a É— ebi wani adadi na gumbar a ajiye gefe guda. Wannan shi ake kira gasara. Sauran gumbar ku m a za a dama ta da ruwan tsamiyar. Daga nan sai batun dama ta da tafasasshen ruwa. Za a zuba ruwan zafin cikin wannan gasara da aka kwa É“ a da ruwan tsamiya , sannan a yi ta gaurayawa. Sai kuma a É— auko g asarar da aka ajiye gefe guda a sanya ciki a ci gaba da gaurayawa. Bayan komai ya ha É— e, to kunu ya samu kenan.

    Idan kuwa sai gumba ta kwana kafin a dama kunu n , za a rufe gumbar a wuri ba mai sanyi ba. Bayan gari  ya waye, za a ga ta taso. Irin wannan  gumba r ba ta bu Æ™ atar tsamiya  yayin dama kunu. Kafin a sanya mata ruwan zafi , za a É— ebi Æ™ asari  a ajiye gefe guda. Bayan an z uba wa gumbar zuwan zafi an dama, sai a sanya wannan Æ™ asari kamar dai yadda abin yake a bayanin da aka yi a sama.

    Idan kuma haka za a sha ba tare da an dama kunu ba, to za a É— ebe ta ne a dama da ruwan sanyi. Akan sanya nono ciki sannan a sa ma É— i.

    Kunun  Sabara

    i. Gumba        

    ii. Kayan yaji

    iii. Ruwa         

    iv. Sabara

    Yadda ake kunun gero , haka ake yin wannan  nau’i na kunu. Bambancin kawai shi ne, yayin da za a tafasa ruwan zafi  ana sanya sabara a ciki. Idan an zo inda da za a saka wannan ruwa cikin gumba, sai a yi amfani da rariya ko wani abin tacewa domin dattin sabarar kada ya shiga.

    Kunun  Sanga-Sanga

    i. Gero            

    ii. Kayan yaji

    iii. Ruwa        

    iv. Sanga-sanga

    Yadda ake kunun zogale  haka ake yin na sanga-sanga. Ita ma ana tafasa ruwan ne da ganyen  sanga-sanga ko a sanya shi cikin gero  yayin da za a yo ni Æ™ an gumba.

    Kunun  Aduwa

    i. Aduwa (ganye ko ’ya’ya ko duka biyu)

    ii. Gero             

    iii. Kayan yaji             

    iv. Ruwa

    Shi ma kunun aduwa  na kama da kunun zogale . Yayin kai ni Æ™ an gumba r za a iya sanya ganye ko ’ya’yan aduwa r a ciki. Sannan ana iya tafasa ruwan kunu tare da ’ya’yan ko ganyen  na aduwa.

    Kunun  Maiwa

            i.            Kayan yaji

          ii.            Maiwa

        iii.            Ruwa

    Wannan daidai yake da kunun gero  da aka yi bayani a sama. Bambancin kawai shi ne, a nan ana amfani ne da maiwa  a maimakon gero.

    Kunun  Shinkafa

    i. Filebo           

    ii. Inibi busashe          

    iii. Mangya É— a

    iv. Ruwa         

    v. Shinkafa                 

    vi. Suga

    Za a wanke  shinkafa sannan a shanya ta bushe domin a kai ni Æ™ a. Bayan an dawo da ita , daga ni Æ™ a, s a i a dama garin da ruwan sanyi. A nan ne za a sanya busasshen  inibi da filebo ko madara. A gefe guda ku m a, za a hu ra wuta  a sanya ruwa a cikin tukunya  a É— ora a bisan wutar . A c ikin r u wan , za a tarfa mangya É— a ka É— an. Da wannan  ruwan zafin ne za a dama gumbar. 

    Kunun  Kanwa

    i. Gero             

    ii. Kanwa

    iii. Ruwa         

    iv. Ma É— i ko Zuma (idan an ga dama)

    Hanyar sarrafa wannan  kunu daidai yake da na wa É— anda aka yi bayani a sama. Bambancin kawai shi ne, ana yin amfani da kanwa yayin samar da wanan kunu. Ya d da ake sanya kanwar kuwa shi ne, ana iya sa t a a cikin ruwan da za a tafasa. Ana kuma iya dama garin kunu n da ruwan kanwar yayin kwa É“ i. 

    Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

    Get a copy:
    To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
    +2348133529736

    You can also write an email to:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.