Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Kayan Kwalama Da Makulashe (Danmalele, Ligidi, Kantun Gana, Kantun Ridi, Gugguru, Gada Da Sauransu)

Abubuwan Da Ke Ciki

Gabatarwa

Abincin   ƙ walama ko ma ƙ ulashe sun kasance nau’o’in abinci n da yawanci ake cin su ba don tare yunwa  ba. A maimakon haka, ana cin su ne kawai domin kwa ɗ ayi. Wannan shi ne ma dalilin da ya sa ake kiran su da abincin ƙ walama. Yara da mata sun fi ta’ammuli da irin wannan  nau’in abinci. Wannan babi na ɗ auke da bayanai game da wasu daga cikin abincin ƙ walama da aka san su wurin Hausawa .

Ɗanmalele

i. Kamu          

ii. Kayan lambu          

iii. Kayan ɗ an ɗ ano

iv. Mai            

v. Ruwa

Za a tafasa ruwa a saman wuta , sannan a kawo kamun gero  a zuba ciki. Za a ci gaba da juyawa har sai ya dafu ya yi dan ƙ o. Ana iya zuba shi bisa faifayi  kamar yadda aka yi bayanin a ci da mai. Sannan ana iya zuba shi cikin kwano ko roba ko dai wani masaki mai kama da wannan . A samansa ake yanka kayan lambu, duk wanda ya sauwa ƙ a, sannan a sanya kayan ɗ an ɗ ano irin su gishiri da magi da makamantansu.

Alewar Gya ɗa

a. Gya ɗ a  

b. Ma ɗ i

A daka gya ɗ a  sai ta yi gari , sai a zuba ma ɗ i a tukunya  a ɗ ora a wuta  ba sai an sa ruwa ba. Za a yi ta juyawa har sai ya narke ya koma ruwa. Daga nan sai a zuba gya ɗ ar a yi ta tu ƙ awa har sai ta yi ja. Bayan ta yi ja, za a samo faranti a shafa masa mai (man zai hana gya ɗ ar ta kama shi idan an zuba). Za a zuba wannan  gya ɗ a r da aka dafa cikin ma ɗ i a kai. Bayan ta bushe , za a ri ƙ a ɓ allawa ko yankawa  daidai gwargwadon girman da ake bu ƙ ata.

Kantun Gana

1. Gyada

2. Ma ɗ i

Da farko, z a a soya gya ɗ a , b ayan ta soy u sai a fece ta, wato a bushe ɓ awon bayan ta . Daga nan za a sanya a turmi  a yi ta daka ta, har sai ta ɗ auko laushi. A gefe guda kuwa za a ɗ ora tukunya   a saman wuta  tare da ma ɗ i a ciki. Bayan ma ɗ in ya yi zafi , sai a sanya wannan  gya ɗ a ciki a yi ta juyawa har sai sun ha ɗ e sosai. Ita ma za a shafa mai a faranti kafin a zuba ta. Bayan ta bushe sai a ri ƙ a ɓ a ɓɓ allata.

Ha njin Ligido /Ligidi

i. Lemon tsami  ko tsamiya

ii. Ruwa          
iii. Ma
ɗ i

Wannan nau’in ma ƙ ulashe kuwa, suga za a sanya a cikin tukunya , sai a ɗ an tarfa ruwa ka ɗ an. Za a bar shi har sai ya narke. Bayan ya fara ja, sai a ɗ an tarfa lemon tsami  ko tsamiya  a ciki. Za a yi ta juyawa har sai ya ha ɗ e gaba ɗ aya. Daga nan za a tanadi sanho [1] daidai adadin wa ɗ anda za su ɗ ebi ligidin gaba ɗ aya. Sannan za a tana ɗ i ƙ ananan tsinkaye, musamman na tsintsiyar kwakwa , su ma daidai adadin wa ɗ annan sanho. Za a ri ƙ a ɗ iban dafaffen sugan ana zubawa cikin sanho sannan a sanya tsinke guda ciki. A gefe guda kuma za a tanadi faifayi  ko kwano ko wani abu mai kama da haka ɗ auke da ƙ asa cikinsa. Za a ri ƙ a jera wa ɗ annan sanho ciki a tsaye, bakinsu na kallon sama. Haka za a bar su har sai sun bushe. Bayan sun bushe, tsinken da ke jiki zai zama kamar mari ƙ a kenan.

Taba r Malam

a. Kayan yaji

b. Ƙ uli

c. Sure/Yakuwa

Za a tanadi sure  busasshe a ha ɗ a da kayan yaji sannan a daka. Bayan ya daku sai a sanya ƙ uli- ƙ uli tare da gishiri a ƙ ara dake su. Daga nan za a ri ƙ a ƙ u ƙƙ ulla ta a cikin farar leda. Ƙ ullin zai kasance ƙ anana- ƙ anana.

Gugguru

a. Masara  

b. Ma ɗ i

Za a gyara masara  sannan a sanya ta cikin tukunya  kan wuta  ba tare da an sanya komai ba. Za a ri ƙ a gaurayawa har sai ta tsattsage gaba ɗ aya , sai a sauke ta , s annan a saka ma ɗ i a ciki. Za a gauraya su gaba ɗ aya domin su game ko’ina. Ana sanyawa cikin leda ko takarda domin sayarwa.

Ri ɗi /Kantun Riɗi

i. Ri ɗ i                          

ii. Ruwa

iii. Ma ɗ i/suga            

iv. Tsamiya

Za a sanya ma ɗ i kan wuta  a bar shi har sai ya yi zafi . Akan tarfa tsamiya  a ciki tare da ruwa ka ɗ an. Daga nan za a wanke  ri ɗ i a sanya a ciki (Za a iya surfa wannan  ri ɗ i kafin a sanya. Wani lokaci kuwa, ana sanya shi haka nan). Za a yi ta juyawa har sai sun ha ɗ e gaba ɗ aya. Daga nan za a nemi faifayi  a shafa mai sannan a zuba a kai a lailaye saman sa . Bayan ya sha iska, sai a sanya wu ƙ a ko wani abu mai kama da wannan a ri ƙ a yankawa  daidai gwargwadon girman da ake bu ƙ ata.

Da ƙuwar Aya

i. Gishiri           

ii. Ruwa  

iii. Ma ɗ i /suga

Za a gyara aya sannan a soya ta. Wannan aya da aka gyara, za a sanya a cikin turmi  a yi ta daka wa . Bayan ta yi laushi , za a saka gishiri ko ma ɗ i tare da ruwa ka ɗ an. Za a ci gaba da dakawa har sai ta yi lu ƙ ui ta fara fitar da mai. Bayan ta ha ɗ e gaba ɗ aya sai a juye cikin ƙ warya ko akushi. Daga nan za a ri ƙ a gutsura ana mulmulawa da hannu ana ajiye wa gefe guda.

Ƙam ƙam/Kantun Gana

i. Gya ɗ a           

ii. Ma ɗ i

iii. Tsamiya  

Gya ɗ a  za a soya a fece , sannan a ɗ an daddaka ta sama-sama. A gefe guda ku m a za a sanya ma ɗ i cikin wuta . Bayan ya yi ja , sai a zuba wannan  gya ɗ a  ciki. Za a yi ta juyawa har sai ya ha ɗ e gaba ɗ aya. Daga nan sai a shafa mai kan faifayi  a juye a kai. Bayan ya bushe ne za a ri ƙ a ɓ a ɓɓ alla shi daidai adadin girman da ake bu ƙ ata.

Gya ɗa  (Ƙwaras-Ƙwaras)

        i.            Gishiri

      ii.            Gya ɗ a  

Ita ma gya ɗ a  ce busas shiya ake soyawa a saka mata gishiri a ciki. Za a ga a wurin suya r tana farfashewa kamar gugguru. Idan ta sha iska , sai batun ci.

A Ci Da Mai

i. Albasa         

ii. Garin masara         

iii. Mai

iv. Ruwa         

v. Yaji

Za a ɗ ora tukunya  da ruwa bisa wuta . Za a bar ta har sai ta tafasa, sannan a yi talgen garin masara  ko ƙ ullunta. Za a bar shi ya dafu sosai , sannan a juye a saman faifayi  ko wani masaki. Daga nan za a soya mai a malale a samansa . Sai kuma a ƙ ara albasa  da yaji. Za a ri ƙ a yayyankawa da wu ƙ a.

Kammalawa

Kamar yadda aka fa ɗ a a sama, ana cin nau’o’in ƙ walama ne ba domin yunwa  ba, sai don kawar da kwa ɗ ayi kawai. Yara sun fi cu ɗ anya da irin wannan  nau’o’in abinci. Yawanci akan sayar da su a kasuwanni da makarantu da wurin taruwar yara. Kenan dai za a iya cewa, ko bayan kasancewarsu abici, hanya ce ta samu n ku ɗ in shiga da zai iya tsayawa a matsayin sana’a.



[1] Takarda ake na ɗ awa cikin salo. Ana barin bakinta ta ƙ asa rufe, yayin da ta sama kuma ke kasancewa a bu ɗ e. Daga wurin bakin da ke rufe, za ta ri ƙ a ƙ ara girma har zuwa wurin da ke bu ɗ e , wanda shi ne ya fi sauran ɓ angarorin jikinta girma. 

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments