Wadansu Batutuwa Da Za Ku Iya Rubutu a Kansu Domin Gabatarwa Wurin Taron Makada Sa'idu Faru

    Waɗannan jerin batutuwa ne (topics) da aka samar kyauta a cikin zauren WhatsApp da aka ƙirƙira domin tattauna batutuwa game da Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa Da Ƙasa Kan Makaɗa Sa'idu Faru (An International Conference on the Life and Songs of Alhaji Sa’idu Faru “Malamin Waƙa Mai Kwana Ɗumi Na Mamman Na Balaraba”). Kowa na iya zaɓa daga cikinsu domin yin rubutu a kai.

    Muna godiya ga waɗanda suka ba da wannan gudummawa: 

    a. Prof. I.S.S. Abdullahi

    b.

    Domin samun cikakken bayani game da taron, a danna NAN.

    Domin karanta muhimman saƙonnin da aka tura a wannan zauren WhatsApp cikin Hausa, a dannan NAN. Cikin Ingilishi kuma a danna NAN.

    1. Zamfarci a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    2. Fitattun Salailai a Waƙoƙinn Sa'idu Faru 
    3. Fasahar kulla Zaren Tunani a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    4. Lafuzzan Raha a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    5. Salon Zayyana a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    6. Kambamawa a gurbin Yabo a Waƙoƙinn Sa'idu Faru.
    7. A kara duba wadannan ko akwai abin da za a tsinta.
    8. Kalmomin Fannu  a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    9. Fasalin Zambo da Habaici a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    10. Hoton Tattalin Arzikin Hausawa a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    11. Tubka da Walwala a Waƙoƙinn Sa'idu Faru.
    12. Munanan Dabi'u a Mahangar Saidu Faru.
    13. Zumuntar Fasahar Saidu Faru da Wasu Makadan Kasar Hausa 
    14. Koda kai a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    15. Waskiya a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    16. Hoton Rayuwar Sa'idu Faru a Cikin Waƙoƙinnsa
    17. Butulci a Mahangar Saidu Faru
    18. Alakar Sa'idu Faru da Sarakunan Kasar Hausa: Tsokaci Daga Waƙoƙinnsa
    19. Salon Yaba Kyauta a Waƙoƙinn Sa'idu Faru. 
    20. Aron Hannu a Waƙoƙinn Sa'idu Faru
    21. Barkwanci a Bakin Sa'idu Faru
    22. Tsattsafin Tattalin Arziki a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru
    23. Gurbin Noma a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru
    24. Noma a Mahangar Makaɗa Sa'idu Faru

    Abu-Ubaida Sani
    Department of Languages and Cultures, FUGUS
    (Secretary, LOC)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.