Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne Hukuncin Wanda Ake Bin sa Azumi Har Wani Azumin Ya Zo Bai Rama Ba Yaya Zai Yi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne Hukuncin Wanda Ake Binsa Azumi Har Wani Azumin Ya zo Bai Rama Ba Yaya Zaiyi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai sunyi ittifaqi akan wajabine akan wanda yasha azumi acikin Ramadan yayi gaggawar ramawa kafin wani Ramadan ɗin ya zo, Sun kafa hujja da Abunda Bukhari yaruwaito (1950) da Muslim ( 1146) daga Aisha Allah yakara yarda da ita tace: ( Nakasance akwai azumin Ramadan akaina da'ake bina, bansamu damar ramawa ba sai awatan sha'aban, saboda matsayin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam awajena).

Alhafiz ibnu hajar ya ce: Zamu fahimci kwadayin ramawarta acikin sha'aban, bai halatta jinkirta biyan bashin azumi ba, har zuwa wani Ramadan ɗin ba.

Idan kuma mutum yajinkirta bashin azumi har wani Ramadan ɗin bazai fita daka halaye biyu ba.

1. Yazama jinkirin akwai uzuri acikinsa, kamar mara lafiyan da cuta ta cigaba ajikinsa har wani azumin ya zo, wannan babu zunubi akansa wajan jinkirta azumin, domin shi mai uzurine, babu Abunda zaiyi saidai yarama azumin kawai.

2. Yakasance jinkirin narashin uzurine, kamar wanda yasamu damar ramawa Amma yaqi ramawa harwani azumin ya zo.

Wannan yanada zunubin jinkirinsa, malamai sunyi ittifaqi akan ramuwar tana nan akansa, saidai sunyi Saɓāni akan Shin wajibine yaciyar dakowanne miskini kowacce rana ko bazai ciyarba ramuwa kawai zaiyi?

Imamu Malik da shafi'i da Ahmad suntafi akan zai ciyar, sun kafa hujjah dacewa hakika an ruwaito daka wasu sahabbai kamar Abu huraira da Ibnu Abbas Allah yakara yarda dasu.

Abu hanifa yatafi akan ba wajibi bane ciyarwa akansa rama azumin kawai zaiyi.

Yakafa hujjah da cewa Allah bai Umarni ga wanda yasha azumi dakomai ba, sai rama azumin kawai, bai Ambaci ciyarwa ba.

Allah madaukakin Sarki ya ce

وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ

Wanda yake ahalin rashin lafiya ko ahalin tafiya saiya sha azumi, yarama awasu kwanakin daban. (Suratul Bakara aya ta 185)

Duba Almajmu'u Na nawawi (6/366) da Al-mugny (4/400).

Wannan zancen nabiyu shine imamul bukhari yazaba, acikin sahihin littafinsa ya ce: Ibrahimun naka'iy ya ce: Idan mutum ana binsa ramuwar azumi bai ramaba har wani Ramadan ɗin ya zo, zayi azumin ne kawai bazai ciyar ba, ana Ambatan wata magana daka Abu huraira da ibnu Abbas cewa: Mutum zai ciyar tareda rama azumin, sai Bukhari ya ce; Allah bai Ambaci ciyarwa ba, kawai cewa yayi ( saiya rama awasu kwanaki daban).

SHaik Usaimeen ma ya tabbatar da wannan maganar tarashin ciyarwa akan wanda yayi sakaci bai rama bashin azuminda ake binsaba har wani azumin ya zo.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments