Dafa-Dukan Indomi
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Indomi
iii. Kayan yaji
iv. Magi
v. Mai
vi. Nama
vii. Ƙwai
viii. Tarugu
ix. Tattasai
x. Zogale
Ita ma indomi ana dafa-dukanta. Abinci ce ta zamani da ta shigo a ƙasar Hausa. Ba kowa ke dafa-dukan indomi ba, saboda abinci ce ta ’yan ƙananan yara da kuma mata. Wannan ya sa wasu jiƙa ta su ke su ci. Sai dai idan aka dafa ta to ta fi daɗi sosai. Za a jajjaga tattasai da tarugu da albasa a saka kayan yaji kaɗan. Za a soya mai ɗan kaɗan a saka albasa tare da jajjage. Idan ya ɗauko soyuwa za a wanke zogale a tace a saka a ciki a ci gaba da soyawa. Idan sun soyu, za a yi sanwa a saka magi da gishiri a ciki. Kada a saka magi da gishiri da yawa, ’yan kaɗan za a saka. Za a iya tafasa nama a sa ciki ko a soya naman kafin a sa. Idan ba a buƙata, za a kaɗa ƙwai da jajjagen tarugu da albasa da ɗan magi da gishiri a haɗe. Za a soya wannan ƙwai sarai sannan a aza shi kan indomi bayan an dafa ta.
Dafa-Dukan Dafaffen Ƙwai da Tattasai Ɗanye
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Ganye
iii. Kayan yaji
iv. Magi
v. Mai
vi. Ƙwai
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix. Tumatur
x. Tattasai ɗanye
Da farko za a ɗauko tattasai ɗanye a yanka shi kare-kare. Haka ma
tumatur za a cire ɗiyan a yanka shi ƙanana-ƙanana. Sai a ɗauko
wata leda mai ƙarfi a fashe ƙwai a ciki a saka kayan yaji da magi
da gishiri a saka tattasai da tarugu da tumaturin da aka yanka a ciki. Za a ƙulle wannan leda sannan a jijjiga ta. Daga nan za a aza
sanwa, sai a riƙa sanya waɗannan ledoji cikin ruwan bayan ya yi zafi. Ba za su ɗauki lokaci ba, za a ga sun rinƙa
haɗewa. Da zarar sun haɗe, to dafa-dukan ƙwai
da ɗanyen tattasai ta samu ke nan.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.