Ticker

6/recent/ticker-posts

Nau’o’in Lemo Na Zamani da Yadda Ake Yin Su a Abincin Hausawa

Gabatarwa

Idan aka ce lemo a nan, ana nufin nau’o’in abin sha da ake amfani da kayan itatuwa  wurin ha ɗ a su. Bahaushe  yana da kayan itatuwa iri-iri da suka ha ɗ a da wa ɗ anda ake samu cikin gida je da ma wa ɗ anda aka fi samu a gonaki da kuma dazuka . Wa ɗ ansu kuwa yakan same su ne daga ba ƙ in al’umm u ko ma ƙ asashen ƙ etare. Irin wa ɗ annan kayan itatuwa ne Bahaushe ke sarrafawa cikin hanyoyi mabambanta domin sha. Wannan babi na ɗ auke da wasu daga cikin nau’o’in lemo da Hausawa  ke amfani da su.

Lemon Tsamiya

i. Filebo

ii. Kayan ƙamshi

iii. Ruwa

iv. Suga

v. Tsamiya

Za a wanke tsamiya, sannan sai a sanya ta a cikin tukunyar da aka ɗora bisan wuta domin dafawa. Bayan ta dafu, sai a sauƙe ta, sannan sai a tace da matata. Daga nan za a ƙara mayar da tataccen ruwan saman wuta. A ciki za a sanya kayan ƙamshi tare da filebo. Za a bar shi kimanin mintuna ashirin kafin a sauke. Sai a sanya suga sannan a bar shi ya sha iska, sai kuma a sanya cikin firijin. Shi ke nan lemon tsamiya ya samu.

Lemon Ɗanyar Citta

i. Filebo

ii. Lemon tsami

iii. Ruwa

iv. Suga

v. Ɗanyar citta

Za a wanke citta ɗanya, sannan a goge ta tsaf a kai markaɗe. Za kuma a iya markaɗa ta da bilanda ko a daka a turmi. Daga nan za a sanya ruwa a ciki a tace da matata. Za a zuba lemon tsami da suga da filebo cikin tataccen rowan, sannan a zuba cikin firijin.

Lemon Abarba

i. Abarba

ii. Filebo

iii. Kayan ƙamshi

iv. Ruwa

Za a fere abarba, sannan a yanka ta ƙanana-ƙanana yadda za a iya amfani da bilanda wurin markaɗa ta. Da zarar an markaɗa, sai a tace sannan a sanya kayan ƙamshi da filebo. Za a iya ƙara suga cikin wannan naui na lemo.

Lemon Abarba da Kwakwa

i. Abarba

ii. Filebo

iii. Kwakwa

iv. Madara

v. Ruwa

vi. Suga

Wannan nau’i na lemo ya na kama da wa ɗ anda aka yi bayani a sama , b ambancin kawai shi ne kayan ha ɗ in. Idan an tashi yin sa, z a a yanka abarba a marka ɗ e ta . Kwakwa r kuwa idan da hali a na so a kankare bayanta kafin a marka ɗ a ta . Idan kuma ba a samu haka ba, za a iya marka ɗ a ta haka nan. Daga nan s a i a tace ta a sanya filebo da suga.

Lemon Kukumba  da Abarba

i. Abarba         ii. Kayan ƙ amshi        iii. Kukumba

iv. Kwakwa    v. Ruwa                      vi. Suga                       vii. Ɗ anyar citta

Wannan lemo ma kamar yadda ake na sama haka ake yin s a. Za a fere  kukumba tsaf kafin a marka ɗ a ta. Abarba  da kwakwa  da citta su ma za a gyara su sannan a marka ɗ e su . Bayan wannan  ya samu duka, sai a sanya kayan ƙ amshi sannan a tace. Bayan an tace , sai a ƙ ara suga.

Lemon Gwaiba  da Tuffa  da Abarba  da Kwakwa

i. Abarba         

ii. Filebo                      

iii. Gwaiba      

iv. Kwakwa

v. Ruwa          

vi. Suga ko zuma        

vii. Tuffa

A wannan  nau’in lemo, za a samu gwaiba da abarba da tuffa da kuma kwakwa . Sai dai amma, a na bu ƙ atar a daidaita adadin wa ɗ annan kayan marmari n da za a yi amfani da su, wato kada wani ya rinjayi wani a yawa. Daga nan sai a tace a sanya filebo da suga.

Lemon Abarba Da Citta

i. Abarba

ii. Citta

iii. Kayan ƙamshi

iv. Ruwa

v. Suga ko Zuma

Wannan nau’in lemo ma ana samar da shi ne kamar dai yadda aka yi bayanin sauran da ke sama. Bayan an markaɗa citta da abarba, sai a sanya kayan ƙamshi sannan a tace su. Daga nan sai a sanya suga ko zuma.

Lemon Kukumba

i. Filebo

ii. Kayan ƙamshi

iii. Kukumba

iv. Lemom Tsami

v. Ruwa

vi. Suga

A wannan nau’in lemo ma, ana fere kukumba a markaɗa. Daga nan kuma sai a samu lemon tsami a cire ’ya’yan tare da kayan ƙamshi a markaɗa sannan a tace. A tataccen ruwan za a sanya filebo da suga.

Lemon Kukumba da Citta

i. Citta

ii. Kayan ƙamshi

iii. Kukumba

iv. Ruwa

v. Suga

vi. Zuma

Wannan nau’in lemo ma daidai yake da wanda aka yi bayani a sama. Bambancin a nan kawai shi ne, citta da kukumba su ne kayan ha ɗ i.

Lemon Kukumba  da Lemon Zaƙi

i. Kayan ƙamshi

ii. Kukumba

iii. Lemon zaƙi

iv. Ruwa.

v. Suga

vi. Zuma

Wannan nau’in lemo daidai yake da yadda ake lemon kukumba da lemon tsami . Bambancin a nan kawai shi ne, ana amfani da lemon za ƙ i ne a maimakon lemon tsami.

Lemon Gwanda

i. Gwanda

ii. Karas

iii. Kukumba

iv. Ruwa

v. Suga ko zuma

vi. Ɗanyar citta

Yayin samar da wannan  lemo, za a fere  gwanda a cire ’ya’yan , sannan sai a yayyanka ta a marka ɗ a da bilanda. Ita ma kukumba r za a fere ta a marka ɗ a. Karas  kuwa za a kankare a yayyanka sannan a marka ɗ a. Citta ma za wanke  sannan a marka ɗ e ta . Daga nan s a i a ha ɗ e su wuri guda a tace. A na shan wannan lemo da suga ko zuma.

Lemon Gwanda  da Ɗanyar Citta

i. Citta

ii. Gwanda

iii. Kayan ƙamshi

iv. Ruwa

v. Suga ko zuma

Ana samar da wannan  nau’in lemo ne kamar yadda aka yi bayanin na sama. Bambancin kawai shi ne, a nan ana amfani ne da gwanda da kuma citta.

Lemon Mangoro

i. Gwaiba        

ii. Kukumba               

iii. Lemo

iv. Mangoro    

v. Ruwa                      

vi. Suga ko zuma        

vii. Tuffa

Wannan nau’in lemo ma hanya guda ake bi da na sama wajen samar da shi. Bambancin kawai shi ne , kayan ha ɗ insa, wa ɗ anda su ka ƙ unshi mangoro da gwaiba da tuffa da kuma kukumba.

Lemon Lemon Za ƙi

i. Kukumba

ii. Kwakwa

iii. Lemon Zaƙi

iv. Ruwa

v. Suga ko zuma

vi. Ɗanyar citta

Shi ma wannan  kamar sauran nau’o’in lemo n da aka yi bayani a baya, sai dai   k afin a marka ɗ a lemon za ƙ i n sai an ɓ are bayan ( ɓ awon) sannan an cire ’ya’yan.

Kammalawa

Ha ƙ i ƙ a akwai nau’o’in lemo daban-daban da Bahaushe  ke samarwa bayan lemokan zamani da ake sayarwa a kantuna. Sau da dama masana na ƙ arfafa guiwar al’umma kan yin amfani da irin wa ɗ annan lemoka da ake ha ɗ awa a gargajiyance kasancewar sun fi lafiya ga jikin ɗ an Adam. 

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments