Faten Alkama
i. Albasa
ii. Alkama
iii. Gishiri
iv. Kayan yaji
v. Magi
vi. Mai
vii. Ruwa
viii. Tarugu
ix. Tattasai
x. Wake
Da farko, za a yi É“arzon alkama, sai kuma a jajjaga tattasai da tarugu da albasa a saka kayan yaji a ciki. Za a soya kayan miya tare da mai. Idan sun soyu za a surfe wake a saka a ciki. Daga nan, za a saka ruwa ba mai yawa ba. Bayan ruwan miyar ya tafasa za a É—auko É“arzon alkama a zuba a ciki, sai kuma a saka magi da gishiri. Yana da kyau a kula, kar a saka ruwa mai yawa.
Faten Acca
i. Acca
ii. Albasa
iii. Gishiri
iv. Magi
v. Mai
vi. Ruwa
vii. Tarugu
viii. Tattasai
ix. Zogale
Za a jajjaga tattasai da tarugu da
albasa masu yawa, daga nan sai a soya su da mai a saka kayan yaji a ciki. Bayan
haka, za a wanke zogale sosai a saka a cikin kayan jajjagen da aka soya a sake soya su tare. Da
zarar wannan ya samu, sai maganar aza sanwa wadda za a
sanya magi da gishiri ciki. Bayan nan za a wanke acca a saka ta a ciki ta ci
gaba da dafuwa har sai ta nuna. Da zarar faten ya nuna, sai batun sauƙe
tukunya.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.