Bitar Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Hausawa na Mutuwa

    Article Citation: Sani, A-U, Shehu, M. & Rambo, R.A. (2023). Bitar Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Hausawa na Mutuwa. Scholars International Journal of Linguistics and Literature, 6(12), 498-502. www.doi.org/10.36348/sijll.2023.v06i12.007.

    Bitar Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Hausawa na Mutuwa

    Abu-Ubaida SANI
    Department of Languages and Cultures,
    Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria
    Email: abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng, abuubaidasani5@gmail.com

    Da

    Dr. Musa Shehu
    Department of Nigerian Languages
    Usmanu Danfodiyo University, Sokoto-Nigeria
    Yawuri3327@gmail.com

    Da 

    Dr. Rabi’u Aliyu Rambo
    Department of Nigerian Languages
    Usmanu Danfodiyo University, Sokoto-Nigeria
    dirindaji12aa@gmail.com

    Tsakure

    Manufar wannan bincike ita ce nazarin ƙwaƙƙwafi domin gano nau’ukan tasirin da addinin Musulunci ya yi wa al’adun Hausawa na mutuwa. An yi amfani da dabarun sanya ido da nazartar kundatattun rubuce-rubuce domin tattara bayanai. An ɗora aikin kan fahimtar Hausawa ta “idan mai wuri ya zo, mai tabarma sai ya naɗe.” Sakamakon binciken ya gano cewa, tasirin Musuluncin bai kawar da dukkannin al’adun Hausawa na mutuwa ba. A maimakon haka, lamarin ya kasu gida huɗu, inda aka samu al’adun mutuwa (i) amintattu da (ii) gyararru da (iii) korarru da (iv) sauyayyu da (v) 'yan kunnen ƙashi. Daga ƙarshe binciken ya nuna dacewar nazartar dalilan da suke sa ake ci gaba da riƙo da waɗansu daga cikin al’adun mutuwa har ya zuwa yau, ƙarni na ashirin da ɗaya (Ƙ21).

    Fitilun kalmomi: Mutuwa, al’ada, Musulunci

    1.0 Gabatarwa

    Shigowar Musulunci ƙasar Hausa ya samar da sauye-sauye da dama kusan a dukkannin ɓangarorin rayuwa. Wannan ya haɗa tun daga kan tsarin zamantakewa da kasuwanci da fahimta da tunani da auratayya, har abin da ya shafi bauta da sauransu. Akwai nau’ukan tasiri daban-daban da ya yi kan muhimman matakan rayuwar Hausawa (aure da haihuwa da mutuwa) da suka kasance bayyanannu. Misali, a ɓangaren aure, ya kawar da waɗansu hanyoyin mallakar mace na gargajiya irin su cire da samame da yaƙi da tsintuwa da makamantansu. A ɓangaren haihuwa kuwa ya kawar da al’adu kamar hanyar tabbatar da ɗiyanci.[1] A fannin al’adun mutuwa kuwa ya kore bukukuwan uku da bakwai da na juya kafaɗa.

    Abin tambaya a nan shi ne, shin bayan ire-iren waɗannan bayyanannun al’adu da ake iya lura da ɓacewarsu tare da ganin gurbinsu kai tsaye, babu waɗansu nau’ukan tasirin da addinin Musulunci ya yi a kan al’adun Hausawa na mutuwa?Binciken nan na da manufar yin nazarin ƙwaƙƙwafi domin gano amsar wannan tambaya. Maƙasudin binciken shi ne (i) zaƙulo nau’ukan tasirin da addinin Musulunci ya yi a kan al’adun Hausawa na mutuwa, da (ii) ƙalailaice nau’ukan sakamakon da tasirin addinin Musulunci kan al’adun Hausawa na mutuwa ya samar.

    1.1 Dabarun gudanar da bincike

    Wannan bincike ne da ke da tsarin tsurar bayani (qualitative form of research). An yi amfani da lura (observation) a matsayin babbar hanyar tattara bayanai daga tushe na farko (primary source). Babbar hanyar tattara bayanai daga majiya ta biyu (secondary source) da aka yi amfani da ita ta kasance bincika rubuce-rubucen magabata, musamman kundatattu.

    Bayan haka, an yi amfani da hira (interview) a matsayin hanyar tabbatar da ingancin bayanai. An samu bayanai game da waɗansu hukunce-hukuncen addinin Musulunci da suka shafi mutuwa daga malaman addini. Waɗansu tsofaffin al’adun mutuwa kuwa, an samu ƙarin bayaninsu daga bakunan masana al’ada. Kai tsaye wannan hanya ta taimaka wajen samun ƙarin haske kan muhimman batutuwa.

    An ƙwanƙwance bayanan da aka tattara ta hanyar ƙalailaicewa da sharhi a falsafance. Bugu da ƙari, an yi amfani da dabarar kwatanci tsakanin batutuwa. An bi tsarin madogara da manazartar APA, sabuntawa ta 7 (APA 7th edition) a duk faɗin nazarin.

    1.2 Ra’in bincike

    Mutuwa na ɗaya daga cikin muhimman ɓangarorin matakan rayuwar Hausawa, wato aure da haihuwa da mutuwa. Wannan ya ƙarfafa guiwar nazarin wajen amfani da Bahaushen ra’i domin yi masa jagoranci. Binciken nan ba shi ne karo na farko da aka yi amfani da Bahaushen ra’i ga ayyukan da suka shafi harshe da adabi da al’adun Hausawa ba. An yi amfani da karin magana a ayyukan Hausa daban-daban ciki har da na Bunza, (2019) da Yahaya, (2021) da Shehu, (2022) da Sidi, (2023).

    An ɗora wannan binciken a kan fahimtar Hausawa ta “Idan mai wuri ya zo, mai tabarma sai ya naɗe.” Idan aka ɗora maƙasudin binciken a kan wannan fahimta, za a iya bayanin cewa, al’adun mutuwa tabarma ce da aka daɗe da shimfiɗawa. Addinin Musulunci kuwa ya zo da dokoki da ƙa’idojin da a cikinsu akwai waɗanda suke wajibi ne a bi su. Ya kasance mai wuri saboda shi ne dole.[2]

    A bisa wannan fahimtar, binciken yana da hasashen cewa, a yanzu dokoki da ƙa’idojin addini ake bi ga dukkanin lamuran da suka shafi mutuwa. Binciken shi zai tabbatar da wannan hasashe ko ya kore shi.

    2.1 Taliyon al’adar mutuwa a Bahaushen kadada

    Mutuwa na nufin gushewar rai daga ganganr jiki da ake iya tabbatarwa ta la’akari da manya da ƙananan alamomin da suka haɗa da daina motsi da sandarewar jiki da kafewar idanu da ɗaukewar numfashi da tsayuwar bugun zuciya na tsawon lokacin da ya zarce na suma a sababbiyar al’adar tsarin halittar ɗan’adam. Lamarin mutuwa yana da babban gurbi a Bahaushiyar al’ada tun tale-tale.

    Ayyuka daban-daban sun kawo bayanai dangane da al’adun Hausawa na mutuwa na gargajiya. Bibiyar waɗannan al’adu tiryan-tiryan zai kasance tamkar maimaici ne. Misali, aikin Abdullahi, (2008) ya kawo cikakken bayani shakundum game da al’adun. Sauran rubuce-rubuce da suka gabata game da al’adun Hausawa na mutuwa sun haɗa da Chamayo, (2018) da Nuhu, (2020).

    2.2 Waiwaiyen shigowar Musulunci ƙasar Hausa

    A ƙarni na 21 (Ƙ21), Musulunci na nufin sauƙaƙƙen addini da ya shafi shika-shikan imani shida: Imani da Allah da manzanninsa da mala’ikunsa da littattafansa da ranar ƙiyama da kuma ƙaddara mai kyau ko mummuna, wanda kuma ya ginu a kan ginshiƙai guda biyar: Imani da Allah da salla da azumi da zakka da aikin Haji ga wanda ya samu iko, tare da gudanar da bauta da zamantakewa da hulɗa da tunani da duk sauran ayyuka bisa koyarwar saukakken littafin ƙarshe (Alƙur’ani), da sunnar manzon ƙarshe (Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)) da ijima’in malamai.[3]

    Tarihin shigowar Musulunci ƙasar Hausa ba sabon al’amari ba ne. Tuni masana da manazarta suka baje kolinsu wajen tono wannan tarihi. Rubuce-rubucen da suka taɓo tarihin shigowar Musulunci ƙasar Hausa sun haɗa da na Ajayi & Crowder, (1971) da Bagobiri, (2008) da Chamayo, (2018) da Bala, (2021) da makamantansu masu tarin yawa.

    Ba a samu daidaito ba a kan lokacin da Musulunci ya shigo ƙasar Hausa. Duk da haka, ana iya cewa Musulunci ya shiga ƙasar Hausa har ya fara yaɗuwa tun a ƙarni na goma sha huɗu (Ƙ14). Ayyukan Ajayi & Crowder, (1971) da Ibrahim, (1982) da Mustapha, (1982) daYahya, (1988) da Ibrahim, (1989) duk suna da fahimtar cewa, Musulunci ya fara yaɗuwa a ƙasar Hausa a wajajen ƙarni na goma sha huɗu (Ƙ14).

    Ibrahim, (1982 p. 74-78) ya bayyana sarakunan farko da suka karɓi Musulunci a Kano da Zazzau su ne,  Sarkin Katsina Muhammadu Korau (1320-1353) da kuma na Kano, Aliyu Yaji (1349-1385). Bunza, (1995 p. 162) ya jaddada cewa Musulunci ya zo Katsina da Kano tun a ƙarni na goma sha uku (Ƙ13). Koma yaya abin yake, a yau (ƙarni na ashirin da ɗaya (Ƙ21)), tuni Musulunci ya mamaye illahirin ƙasar Hausa.

    3.0 Tasirin Musulunci kan al’adun mutuwa na Hausawa

    Musulunci ya yi tasiri kan rayuwar Hausawa ta ɓangarori daban-daban. A ɓangaren al’adun Hausawa na mutuwa, ana iya kallon wannan tasiri ta fuskoki guda biyu kamar haka:

    a.      Kore al’adun da ba su dace da Musulunci ba

    b.      Samar da sababbin hanyoyi da matakai da ba a bin su a gargajiyance

    c.       Samar da sauye-sauye da/ko gyare-gyare ga salo da tsarin waɗansu lamura

    Binciken ya nazarci ayyukan da suka gabata irin na su Abdullahi, (2008) da Chamayo, (2018) da Nuhu, (2020) domin samun haske kan ire-iren tasirin da aka samu a waɗannan ɓangarori.

    3.1 Kore al’adun Hausawa na mutuwa

    Akwai al’adu da dama na mutuwa da ake gudanarwa kafin zuwan Musulunci. Zuwan addinin Musulunci ya kawo ƙarshen da yawa daga cikin waɗannan al’adu. Daga ciki akwai:

    1.      Almubazzaranci: Almubazzaranci na nufin ɓarnatar da kuɗi ko wani abin amfani ta hanyar kashewa ko lalatawa ko banzantarwa da nuna halin ko-in-kula ko riƙon sakainar kashi yayin amfani da shi, wadda hakan ka iya sa ya lalace ko ya ƙare cikin ƙanƙanin lokaci, koma bayan yadda zai yi ƙarko ko auki idan aka bi da shi cikin taka-tsantsan. Hidindimun mutuwa a ƙasar Hausa a da yana cike da almubazzaranci. Yanke-yanken dabbobi da shirya bukukuwa na buƙatar kashe kuɗaɗe da sadaukar da dabbobi masu tarin yawa. Musulunci ya taka wa wannan birki.

    2.      Bukukuwa: A da, akwai jerin bukukuwa da ake aiwatarwa bayan mutuwa a gargajiyance.[4]Sun ƙunshi bukukuwan ranakun uku (3) da bakwai (7) da arba’in (40) da kuma na shekara da ake kira baraya ko bikin juya kafaɗa. Musulunci ya kore waɗannan baki ɗaya.

    3.      Jinkiri kafin kawar da gawa: A da, ana iya jira har na tsawon kwana ɗaya ko biyu don jiran ‘yan uwan mamaci da za su taho daga nesa kafin a binne gawa (Abubakar a cikin Chamayo, 2018 p. 152). Amma kai tsaye Musulunci ya hana irin wannan jinkiri. Ya umurci da a gaggauta jana’iza ga gawa tare da kai ta makwanci.[5]

    4.      Kalamai: Akwai nau’ukan kalamai da Musulunci ya sa aka yi watsi da su waɗanda suka shafi al’adun mutuwa. Daga ciki akwai sanar da mamaci da ake yi kan cewa idan aka tambaye shi, to ya ce shi kaɗai ne ya rage, kuma ga shi ya iso. Ma’ana dai kada mutuwa ta dawo duniya ko cikin wannan zuriya domin ƙara ɗaukar wani. Daga cikin gaisuwar mutuwa ma ya kore kalamai da suka haɗa da irin su: “Ashe wane bai jure ba!” da “Ashe wane ya yi kasala!”

    5.      Kiɗa da rawa: Ko ba lokacin mutuwa ba, Musulunci ya tsawatar game da kiɗa da rawa.[6] Bukukuwan mutuwa na gargajiya suna cike da kaɗe-kaɗe da raye-raye. Addini ya sa an yi watsi da waɗannan.

    6.      Yanka a kan kabari: A da, Hausawa sukan yi yanke-yanke a kan kabarin mamaci kamar yadda (Abdullahi, 2008 p. 331-342) da Chamayo, (2018 p. 55) suka nuna. Tasirin addinin Musulunci ne ya sa aka daina wannan a yau.

    7.      Binne gawa tare da kayayyakin amfani: A da, akan binne gawa tare da waɗansu tarkace. Misali, akan binne namiji tare da kayan sana’arsa, kamar fartanya da sauransu. Mace kuwa akan binne ta da kayan girke-girke. Addini ya kawo ƙarshen wannan.

    A ɓangaren tunani kuwa, Musulunci ya kawar da fahimtar gargajiya game da dalilan mutuwa, wato tsufa ko ciwo ko maita ko baki da makamantansu. A maimakon haka, an riƙi sabuwar fahimtar cewa, mutum yana mutuwa ne idan kwanansa ya ƙare, ko da kuwa babu wani dalili.

    3.2 Samar da sababbin hanyoyi da matakai

    Bayan kore al’adu da aka tattauna a ƙarƙashin 3.1, Musulunci ya kawo waɗansu matakai da hanyoyi da suka shafi lamarin mutuwa da binne gawa.

    1.      Jana’iza: Jana’iza tana nufin matakan shirya gawa tun daga bayan mutuwa har zuwa binnewa a ƙabari bisa koyarwar addinin Musulunci. Musulunci ya zo da cikakkiyar koyarwa game da jana’iza. Manyan abubuwan da ta ƙunsa sun haɗa da (a) wankan gawa da (b) sanya likkafani da (c) sallar jana’iza da (d) gina ƙabari (e) bin dokokin saka gawa a ƙabari da (f) gajarce tudun kabari.

    2.      Wankan gawa: Wankan gawa wani nau’in wanka ne na musamman da ake yi wa mamaci, wanda ake gudanarwa bisa shatattun ƙa’idojin addini da suka shafi mai yin wankan da matakan aiwatar da shi. Musulunci ne ya kawo wannan.

    3.      Turare: Addinin Musulunci ya koyar da sanya turare a gawa.

    4.      Likkafani: Likkafani farin yadi ne da ake suturta mamaci da shi ta hanyar rufe shi tun daga kai har ƙafafu bayan wankan gawa, gabanin a gudanar da sallar jana’iza. Musulunci ne ya zo da wannan. A da, akan rufe mutum ne da tufafinsa na yau da kullum tare da waɗansu daga cikin kayan sana’arsa.

    5.      Maƙabarta: Maƙabarta wuri ne na musamman da ake keɓewa, mafi yawa a bayan gari, domin binne mamata bisa tsarin jera ƙaburbura. Kafin zuwan Musulunci, Hausawa na binne mamatansu ne a gidaje da gonaki. Musulunci ne ya zo da tsarin keɓe maƙabarta.

    6.      Fuskantarwa zuwa alƙibla: A da babu wani takamaiman tsarin saka gawa a rami. Hasali ma, akwai waɗanda ake sakawa a zaune ko a tsaye.[7] Addini ne ya koyar da a fuskantar da gawa alƙibla yayin binnewa.[8]

    7.      Kwantarwa ta hannun dama: Kamar yadda aka yi bayani a ƙarƙashin “3” da ke ƙasan “3.2”, duk tsare-tsaren kwantar da mamaci da gina nau’in ƙabari na musamman ya samu ne daga koyarwar addinin Musulunci.

    3.3 Lauje cikin naɗi

    Ayyukan da suka yi bayani game da al’adun Hausawa na mutuwa (kamar na Abdullahi, (2008)) kaɗai sun isa bayyana cewa addinin Musulunci ya yi matuƙar tasiri kan al’adun. Ƙin ƙarawa kuwa, ayyukan manazarta irin su Chamayo, (2018), sun bayyana ire-iren waɗannan tasirin ƙarara. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, akan samu lauje cikin naɗi yayin da ake sauya wa waɗansu daga cikin al’adun da Musulunci bai zo da su ba salo da siga. Waɗansu al’adun kuwa, akan samu mutanen da ke aikata su cikin Hausawa duk da hanin da Musulunci ya yi. Lura da wannan, ana iya kallon lamarin tasirin Musulunci kan al’adun Mutuwa a ƙasar Hausa ta fuskoki biyar (5) kamar haka:

    1.                  Amintattu

    2.                  Gyararru

    3.                  Korarru

    4.                  Sauyayyu

    5.                  ‘Yan kunnen ƙashi

    1. Amintattu

    Waɗannan su ne al’adun Hausawa na mutuwa da suka dace da addinin Musulunci ko suke da gurbi na musamman a cikinsa. Babban misali a nan shi ne gaisuwa/ta’aziyya ga ‘yan uwan mamaci.

    2. Gyararru

    Akwai nau’ukan al’adun da suka shafi mutuwa waɗanda addinin Musulunci ya yi wa kwaskwarima.[9] Daga cikinsu akwai:

    a.      Samarda cikakken bayani da ƙa’idojin raba gado[10]

    b.      Samar da taƙamaiman ƙa’idoji da matakan gina ƙabari da binne gawa a ciki

    c.       Samarda taƙamaiman lokaci da tsarin takaba[11]

    3. Korarru

    Waɗannan su ne al’adun Hausawa na mutuwa da addini ya kore sannan Hausawa suka yi watsi da su. Daga cikinsu akwai:

    a.      Bukukuwa

    b.      Jinkirta binne mamaci

    c.       Kalaman jahilci

    d.     Kiɗa da rawa

    e.      Yanke-yanke a kan ƙabari

    f.        Binne gawa da tarkace cikin rami[12]

    4. Sauyayyu

    Waɗannan su ne al’adun Hausawa na mutuwa da addini ya kore amma Hausawa suka ci gaba da riƙo da su bayan sun sauya musu fasali. Misalansu sun haɗa da:

    a.      Bikin kwana uku da suka sauya da sadakar uku

    b.      Bikin kwana bakwai da suka sauya da sadakar bakwai

    c.       Bikin kwana arba’in da aka sauya da sadakar arba’in

    d.     Bikin shekara da aka sauya da fidda’u ko sadakar shekara

    Talata Mafara, (1998 p. 10-12) ya kawo waɗansu bidi’o’i da Hausawa ke aiwatarwa waɗanda suka shafi mutuwa. Idan aka lura da su, za a tarar da cewa suna kama kai tsaye da waɗansu al’adun gargajiya da aka sauya wa fasali bayan zuwan Musulunci. Daga cikinsu akwai ambata wa gawa kalmar shahada (wanda ya yi kama da ba wa mamaci saƙo). Akwai kuma binne gawa tare da rubutun Ƙurani ko sunayen Allah ko wani abu da ke da nasaba da addini. Shi ma ya yi kama da aladar binne mamaci da waɗansu kayayyakin sana’arsa.

    5. ‘Yan kunnen ƙashi

    Waɗannan su ne al’adun Hausawa na mutuwa da addini ya kore amma wasu daga cikinsu suka ci gaba da aiwatar da su:

    a.      Kukan mutuwa ta hanyar ɗaga murya ko ihu

    b.      Jinkirta jana’iza har sai wani babban mutum ya iso

    c.       Zaman makoki, wanda shi ma wani nau’i ne na almubazzaranci da ɓata lokaci

    4.0 Sakamakon Bincike

    Lamarin addinin Musulunci da al’adun Hausawa, ana iya cewa da mai wuri da mai tabarmar na da ɗan jituwa. Addinin Musulunci bai kore waɗansu daga cikin al’adun mutuwa ba da suka haɗa da bayyanannu da kuma ɓoyayyu kamar yadda aka gani a ƙarƙashin “3.3” da ke sama. Duk da haka, ya yi tasiri matuƙa wurin hana waɗansu al’adu tare da kawo sababbin matakai da ƙa’idojin da suka shafi lamarin mutuwa.

    A ɓangare guda kuwa, duk da zayyanannun ƙa’idojin Musulunci game da sha’anin mutuwa, akwai ɗaiɗaikun al’adu da ake ci gaba da aikatawa jefi-jefi a ƙasar Hausa. Waɗansu daga cikinsu an sauya musu fasali kamar yadda aka bayyana a ƙarƙashin “4” na “3.3” da ke sama. Waɗansu kuwa an ƙeƙashe ƙasa ne an ci gaba da aiwatar da su, kamar dai yadda suka fito a ƙasan “5” da ke ƙarƙashin “3.3” da ke sama.

    Tasirin da Musulunci ya yi kan al’adun Hausawa na mutuwa ya haifar da sauƙin lamura da kauce wa almubazzaranci da ɓata lokaci na babu gaira babu dalili. Hakan ya faru ne ta sanadiyyar hana bukukuwa da shagulgulan da ke dabaibaiye da su. Bayan haka, mataki ne na ƙara wayar da kan Hausawa. Ya kore kalamai da waɗansu al’adu da ke nuna tsagoron jahilci, kamar sanya mamaci kabari da kayan sana’a ko tura saƙo zuwa ga mutuwa, da makamantansu.

    Akwai hasashen cewa, ci gaba da aiwatar da al’adu kamar su sadakar uku (3) da ta bakwai (7) da kuma ta arba’in (40) duk suna wanzuwa ne kasancewar malaman gargajiya na amfana daga gare su. Mutanen da ke ci gaba da ribibin zaman makoki ma an fi danganta su da masu zaman kashe wando ko zaman gulma da tsegumi, ko kuma ‘yan zaman ciye-ciye da shaye-shaye kawai (‘yan ina da abinci?).

    Wannan bincike ya fi karkata kan al’adun da ake gudanarwa daga lokacin aukuwar mutuwa zuwa bayanta. Yana da kyau a tuna cewa, ko gabanin mutuwa, akwai al’adu da ake gudanarwa waɗanda ke da alaƙa da ita kai tsaye ko a kaikaice. Binciken ya ɗauke su a matsayin al’adun jinya. Daga jinya suke farawa har su sauya salo yayin da alamun mutuwa suka tabbata ga majinyaci. Sauye-sauyen da addinin Musulunci ya samar kan al’adun jinya sun haɗa da (i) shan rubutu a maimakon shan jiƙe-jiƙe, (ii) yawan furta kalmar shahada ga majinyaci, da dai sauransu.

    5.0 Kammalawa

    Sakamakon wannan bincike ya ci karo da hasashen da binciken ya yi tun farko. Hasashen da aka gina kan ra’in binciken na sa ran ganin Musulunci ya kawar da al’adun Hausawa na mutuwa baki ɗaya. Akwai buƙatar  gudanar da binciken da zai ƙara tabbatar da dalilan da yake sa waɗansu Hausawa ci gaba da gudanar da waɗansu al’adun mutuwa da addini ya kore. A gefe guda kuwa, akwai buƙatar malamai da sauran masana da manazarta har ma da hukumomin da abin ya shafa  su ƙara ƙaimi wajen faɗakar da al’umma. Hakan zai sa a ƙara kauce wa al’adu marasa kan gado tare da rungumar koyarwar addini bisa datacciyar turba.

    Manazarta

    Abdullahi, I. S. S. (2008). Jiya ba yau ba: Waiwaye a kan al’adun matakan rayuwar Maguzawa na aure da haihuwa da mutuwa [Kundin digiri na uku da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Ajayi, J. F. A., & Crowder, M. (1971). History of West Africa. Longman Group Limited.

    Bagobiri, B. I. (2008). The contribution of some selected Gobirawa scholars to the development of Islam in Sokoto and Zamfara states [Unpublished master’s dissertation]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Bala, I. (2021). Gudummawar malaman Kusfa Zariya a fagen ilmi da magunguna a al’ummar Hausawa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Talata Mafara, M. I. (1998). Biyanul bida'i.

    Bunza, A. M. (1995). Magungunan Hausa a rubuce (Nazarin gudummawar ayyukan malaman tsibbu) [Kundin digiri na uku da ba a wallafa ba]. Jami’ar Bayero Kano.

    Bunza, A. M. (2019). Ƙwarya a Farfajiyar Adabi da Al’adun Bahaushe. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 2(12), 720–727.

    Chamayo, Y. (2018). The da’wah activities of some Muslim organizations towards the conversion of Maguzawa to Islam in Kano and Jigawa states [Unpublished doctoral dissertation]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Ibrahim, M. S. (1982). Dangantakar al’ada da addini: Tasirin Musulunci kan rayuwar Hausawa ta gargajiya [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami’ar Bayero Kano.

    Ibrahim, M. S. (1989). Tarihin Ajamin Hausa kafin jihadi. Seminar Presentation. Center for the Study of Nigerian Languages, Bayero University Kano.

    Mustapha, A. A. (1982). A new interpretation of the History of Islam in Kanem Borno [Seminar]. Department of Islamic Studies, Bayero University Kano.

    Nuhu, A. (2020). Zamani abokin tafiya: Wasu al’adun Maguzawan ƙasar Katsina a ƙarni na 21. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Shehu, A. (2022). Jaki a rayuwar Bahaushe [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.

    Sidi, M. (2023). Bature a rubutattun waƙoƙin Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.

    Yahya, I. Y. (1988). Hausa a rubuce: Tarihin rubuce-rubuce cikin harshen Hausa. Northern Nigerian Publishing Company.

    Yahaya, S. U. (2021). Damben Hausawa a zamanance [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.



    [1]Tsohuwar al’ada ce ta tabbatar da cewa jariri ba ɗan shege ba ne.

    [2]Ubangiji ya bayyana cikin Ƙur’ani cewa: “Lallai addini a wurin Allah shi ne Musulunci” (Imran, aya ta 19). Baya ga haka, ya yi gargaɗi mai tsanani kan waɗanda suka ci gaba da riƙo da hanyar ɓata bayan shiriya ta zo musu (Nisa’i, aya ta 113).

    [3]Yana da kyau a fahimci cewa, ma’anar “Musulunci” zai ɗan sauya a yayin da aka yi ƙoƙarin bayaninsa a waɗansu lokuta. Misali, an samu salla da Ƙur’ani ne bayan zuwan manzon tsira, Muhammadu (SAW).

    [4]Yana da kyau a gane bambancin da ke tsakanin “1” da “2” da ke ƙarƙashin “3.1”. Na “1” na magana ne kan almubazzaranci, ko ma ta wace siga ya kasance. Na “2” kuwa na magana ne kan bukukuwan kai tsaye. Almubazzaranci ɗaya ne kawai daga cikin illolin waɗannan bukukuwa. Bayan shi akwai ɓata lokaci da yin abu marar dalili da bin tafarkin Maguzanci.

    [5]A duba Bukhari 1,315 da Muslim 944.

    [7]A gidan tarihi na Ɗanhausa da ke Kano, akwai ƙarafa biyu da aka same su a ramin da aka sanya mamaci a tsaye. An yi hasashen ɗaya ne daga cikin jaruman wancan lokaci, kuma an yi hakan ne saboda karrama jarumtarsa.

    [8]Dumin samun ƙarin bayani a duba Abu Dawud, hadisi na 2,874.

    [9]Yana da kyau a lura a nan domin bambancewa tsakanin al’adun da addinin Musulunci da kansa ya musu kwaskwarima da kuma waɗanda kore su ya yi, amma sai Hausawa suka yi musu kwaskwarima domin ci gaba da aiwatar da su ta waɗansu sigogi na daban.

    [10]A duba Baƙara, aya ta 234.

    [11] A da takaba ba tada wani tsari taƙamaimai. Akan yi ta ne kara zube, cike take da al’adu da camfe-camfe. Musulunci ya zo da tsarin takaba daki-daki tare da kore takabar maza. Ya kuma kore waɗansu daga cikin al’adun takaba irin su ajiye wuƙa da shafa shuni a fuska domin razana mutuwa idan ta dawo da daina yin wanka na tsawon kwanaki, da sauransu.

    [12]A duba lambobi na “2” zuwa na “7” da ke ƙarƙashin “3.1.”

    Bitar Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Hausawa na Mutuwa

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.