Ticker

6/recent/ticker-posts

Kunun Noni, Kunun Aya, Kunun Dankali, Kunun Kwakwa, Kunun 'Ya'yan Itace, Kunun Kuskus, Kwastad, Yogot, Ayis Kirim

A wannan shafi, an kawo bayanai game da yaddda ake sarrafa Kunun Nono da Kunun Dankali da Kunun Aya da Kunun Kwakwa da Kunun 'Ya'yan Itace da Kunun Kuskus da Kwastad da Yogot da Ayis Kirim.

Kunun Nono

i. Gero   

ii. Kayan ƙamshi 

iii. Madara

iv. Nono 

v. Ruwa  

vi. Suga  

vii. Zuma

Za a samo nono adadin yawan kunun da za a yi, sai a raba shi kashi biyu. Za a burkake kashi guda a sanya masa kayan ƙamshi a ciki. Kashi gudan kuwa za a haɗe shi tare da gumbar gero. Za a dama kashin da aka haɗe da gumbar gero tare da ruwan zafi. Sannan sai a sanya sauran nonon da aka ajiye a matsayin gasara. A wannan gaɓa ne kuma za a iya ƙara madara ta ruwa ko ta gari tare da zuma.

Kunun Dankali

i. Dankalin Hausa

ii. Gero ko Dawa

iii. Kayan Ƙamshi

iv. Ruwa

Akan jiƙa gero ko dawa amma ba mai yawa ba. A gefe guda kuma sai a fere dankalin Hausa a yayyanka cikin wannan gero ko dawa. Za a ƙara kayan ƙamshi ciki sannan a kai markaɗe. Bayan an dawo da shi, za a tace a cire gasara sannan a dama kunu tamkar yadda ake dama kunun koko. Daga baya ne kuma za a sanya wannan gasara da aka tanada.

Kunun Aya

i. Aya   

ii. Dabino  

 iii. Kayan ƙamshi

iv. Kwakwa  

v. Madara  

vi. Ruwa   

vii. Suga

Za a fece aya, sai a wanke, sannan kuma a jiƙa ta. An fi so a yi amfani da ayar Hausa. Yayin da za a kai markaɗe, za a sanya kwakwa da dabino (bayan an cire ƙwallon dabinon) tare kuma da kayan ƙamshi. Bayan an markaɗo za a tace sannan a zuba madarar ruwa ko ta gari.

Kunun Kwakwa

i. Kayan ƙamshi

ii. Kwakwa

iii. Ruwa

iv. Suga

v. Ɗanyar Shinkafa Ta Tuwo

Wannan nau’in kunu ne da ɗanyar shinkafa ta fi yawa a ciki. Da farko, za a jiƙa ɗanyar shinkafa ta jiƙu. Bayan ta jiƙu, za a sanya kwakwa adadi mai yawa tare da kayan ƙamshi, sannan sai a kai markaɗe. Bayan an dawo da ita, za a tace, sannan sai a dama ta da ruwan sanyi. Ana iya sha haka nan, ana kuma iya sanya suga.

Kunun ’Ya’yan Itace

i. Abarba  

ii. Ayaba

 iii. Kankana  

iv. Kayan ƙamshi

v. Kwakwa  

vi. Ruwa  

vii. Shinkafa  

viii. Tuffa

Wannnan nau’in kunu ne da ya ƙunshi ’ya’yan itatuwa iri daban-daban. Da farko, za a jiƙa shinkafa, a gefe guda kuwa, za a tanadi nau’o’in kayan marmari kamar yadda aka bayyana a sama. Abu na gaba, sai a haɗe su da wannan jiƙaƙƙiyar shinkafar, sannan sai a ƙara kayan ƙamshi a kai wurin markaɗe. Bayan an dawo da shi daga markaɗe, za a tace a fitar da gasara gefe (ba dole ba ne a yi gasara) daga nan sai a dama kunu. Bayan ya damu, sai a kawo gasarar da aka tanada a sanya a ciki tare da ci gaba da damawa. Ga mai son ya yi ɗanɗanon zaƙi sosai (shazumami), sai ya ƙara suga kafin ya fara sha.

Kunun Kuskus (Couscous)

i. Kuskkus

ii. Madara

iii. Ruwa

iv. Suga

v. Tuffa

Za a tanadi madarar gari a kwaɓa ta tare da suga a sanya a cikin tukunyar da aka ɗora bisan wuta. Idan ta dafu, sai a ɗauko kuskus a riƙa barbaɗawa ana juyawa/gaurayawa a hankali. Da zarar an zube kuskus ɗin tsaf, za a gauraya sosai domin ko’ina ya haɗe. Daga nan sai batun saukewa.

Kunun Yara

i. Alkama 

ii. Dawa ja  

iii. Gyaɗ

iv. Masara

v. Ruwa 

vi. Waken suya 

vii. Zuma

Za a jiƙa alkama da masara da waken suya su kwana. Washe gari sai a soya gyaɗa a cire ɓawon a haɗa a markaɗo su gaba ɗaya. Bayan an dawo daga markaɗen, sai a tace sannan a cire gasara. Ana dama shi kamar kunun koko, sannan sai a sanya gasara daga baya. Zai ƙara armashi idan aka sanya zuma cikin irin wannan nau’in kunu.

Kwastad (Custard)

i. Dawa 

ii. Gyaɗ

iii. Masara

iv. Ƙwai 

v. Ruwa  

vi. Suga 

vii. Waken suya

Idan za a yi kunun kwastad, gyaɗa za a soya sai ta koma ja, sannan ɓawonta ya fita. Daga nan sai a murje ta a fece a aje gefe guda. Bayan wannan, sai a soya gero da dawa da kuma masara daban-daban sai a haɗe su waje ɗaya da gyaɗar. Za a kawo waken suya a zuba a kai wajen niƙa. Bayan an dawo daga niƙa, sai a tankaɗe shi. A gefe guda kuma, za a tanadi ruwa a saman wuta. Da zarar ruwan ya tafasa, sai a riƙa ɗiban wannan gari ana barbaɗawa a hankali ana damawa. Kenan dai shi kwastad a kan wuta ake dama shi saɓanin sauran nau’o’in kunu da ake zuba ruwan zafin kansu. Bayan an kammala damawa za a fasa ƙwai a kwaɓa sannan a zuba cikin kwastad ɗin da ke saman wuta.

Bayan an zuba ƙwai, za a sake jujjuya shi domin ya haɗe gaba ɗaya. Daga nan sai a sauke shi. Bayan an sauke, ana iya sanya madara ta ruwa (akan ma iya sanya ta gari) da kuma suga. An fi ba wa yara irin wannan nau’in kwastad. 

Yogot (Yoghurt)

i. Madarar gari

ii. Nono

iii. Ruwa

Za a ɗora ruwa bisa wuta a tukunya mai kyau domin ya tafasa. Bayan ya tafasa, sai a sauke a bar shi ya ɗan huce kaɗan. Daga nan sai a kawo madarar gari a riƙa barbaɗawa a hankali ana damawa, har sai ya yi kauri. Za a lura da shi sosai domin kada ya yi gudaji. Bayan wannan ya kamala, sai a kawo nono mai kyau mai kauri kuma wanda ba shi da tsami. Za a riƙa zuba wannan nonon a hankali ana gaurayawa. Bayan an kammala wannan, sai a rufe a ajiye a wuri mai ɗan ɗumi na kimanin awa huɗu. Bayan nan za a ɗauko a sanya filebo da suga. Ana buƙatar a sanya shi cikin firijin a wannan gaɓa. Yayin da aka zo cire shi, za a tarar da ya yi kauri sosai ya zama yogot.

Ayis Kirim (Ice-Cream)

i. Ayaba

ii. Filebo

iii. Madarar ruwa

iv. Ruwa

v. Suga

Za a sami ayaba mai kyau gwargwadon adadin ayis kirim ɗin da ake son haɗawa. Sai a yayyanka wannan ayaba ƙanana-ƙanana, a zuba a bilanda a markaɗe. Ba a buƙatar sanya ruwa yayin wannan markaɗe. Daga nan sai a juye ayabar a cikin roba ko kwano mai kyau. Sai kuma a fasa madarar ruwa a sanya a ciki. Za kuma a ƙara filebo amma ta ayaba (filebon ayaba). A kula, filebon da za a sanya kaɗan ne. Sannan za a sanya suga shi ma ba mai yawa ba. Idan ana buƙata, za a ƙara sanya ɗanyen inibi a ciki. Da zarar an yi wannan, sai a juye cikin robobi sannan a sanya cikin firijin. A lokacin da ya yi ƙanƙara, shi ke nan ya zama ayis kirim.

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments