Dafa-Dukan Wake da Taliya
Kayan haÉ—in da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Gishiri
iii. Kayan yaji
iv. Magi
v. Ruwa
vi. Taliya
vii. Tarugu
viii. Tattasai
ix. Tumatur
x. Wake
xi. Zogale
Za a wanke wake a dafa sannan a ajiye gefe guda. Daga nan sai a jajjaga kayan miya a soya tare da kayan yaji. Za a yi sanwa a saka magi da gishiri. Idan ta tafasa a saka wake da taliya a ciki. Idan ana buƙata za a saka zogale da taliya in kuma ɗanya ce a murje a saka.
Dafa-Dukan Kuskus da Wake
Kayan haÉ—in da za a tanada su ne:
i. Alayyafu
ii. Albasa
iii. Gishiri
iv. Kori
v. Kuskus
vi. Magi
vii. Man gyaÉ—a
viii. Nama
ix. Ruwa
x. Tattasai
xi. Wake
Za a wanke wake a dafa shi a ajiye shi gefe. Sannan sai a tafasa nama da magi da gishiri kaɗan. Daga nan a jajjaga tattasai da tarugu da albasa a soya su soyu, sai a yi sanwa tare da magi da gishiri da kori a rufe tukunya. Idan ya taso, sai a zuba tafasashen naman da aka ajiye gefe da wake a yanka albasa da alayyafu da kabeji a zuba tare. Idan sun ɗan yi mintuna kimanin biyar, sai a saka kuskus a juya shi a saka kayan ƙamshi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.