𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin
ko ya halatta idan Mutum yaji Sha'awa ta kamashi ya biya wa
kansa bukata ta hanyar wasa
da al'aura (Istimna'i)?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Alal-Haƙiƙa wannan wata Mas'alac e da ana iya cewa ta yawaita sosai a wannan zamanin, musamman tsakanin Samari da 'Yammata, ha rma da Matan-Aure da kuma Mazan-Aure, to amma dangane da abinda da ya shafi hukunci akan Istimna'i' (Masturbation) Malamai sunyi Saɓani akai tareda maganganu kamar guda uku:
1. Ƙauli na farko Shine,
Mazhabin
Malikiyya da Hanabila dakuma mafi yawa daga cikin Malamai duk sun tafine akan
cewa haramunne bai
halattaba ga Mace ko Namiji
su aikata hakan, domin kuwa yin hakan Ta'addancine
da ƙetare
iyakar Ubangiji, waɗannan Malamai dai sun kafa Hujjarsune da faɗin Aʟʟaн(ﷻ) acikin wannan aya inda yake cewa:
وَالَّذِينَ
هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ.......... إلَخ
MA'ANA:
(Muminai)
sune waɗanda suke kiyaye
farjinsu (basayin zina kuma basa yarda kowa yaga tsiraicinsu)…………har zuwa ƙarshen
ayõyin:
2. Ƙauli na biyu Shine,
Mazhabin
Hanafiyya da wani sashe na Hanabila
suntafi akan cewa asali dai yin Istimna'i haramunne, to amma yana iya zama halal tareda wasu Sharuɗɗa
kamar haka;
①
ya kasance Mutum bashi da aure.
②
ya kasance in baiyi hakanba to ba makawa dole sai yaje yayi Zina.
③
kada yayi nufin jindaɗi
kawai, saidai yayi nufin yana sone yakarya ƙarfin-Sha'awarne, kokuma ya kasance idan
Mutum bai yi ba hakan na iya haifar masa da wata cuta a jikinsa, suka ce idan
akwai irin waɗannan Sharuɗɗa to ya
halatta Mutum yayi Istimna'i, saboda Ƙa'idar nan ta Usūl da take cewa:
(إرتكاب أخف الضررين)
3. Ƙauli na uku kuma Shine,
Akwaii wasu daga cikin Malamai dasuke ganin cewa kai
tsaye yin Istimna'i ya
halatta, Dalilinsu kuwa suka ce babu wani Nassi daga Alƙur'ani ko Hadisi da yafito afili ƙarara
abayyane yanuna haramcin Mutum yayi wasa da al'aurarsa har yafitar da Maniyyi,
musamman kuma idan ya kasance Mutum yayi
hakanne sakamakon yasamu
kansa cikin tsanani, kamar irin Matan da Mazajensu sukanyi dõguwar tafiya basu dawõba, ko Matar da aka saketa, ko wacce ma batayi
aurenba, ko Namijin da bashida Mace kuma Sha'awa
tana damunsa, kokuma yanada Matar
amma wani dalili yasa
bazai iya kusan tartaba, dadai sauran abubuwa makamantansu, sukace irin waɗancan babu laifi suyi,
Saidai duk dahaka sukace yinsa ɗin
abin ƙyamane
ga wanda Sha'awar bata tsananta agareshiba. Sannan sukace ai dukkan Malamai sunyi Ittifaƙi
akan cewa ya halatta
Mace tayi wasa da Azzakarin-Mijinta haryakai ga fitar da
Maniyyi, hakanan shima ya
halatta yayi wasa da Farjin-Matarsa harta gamsu, sukace to
inda ace akwai wata cuta da zata
samu Mutum adalilin hakan kamar yadda ake faɗa,
to da Shari'a bata halatta yin hakan ga Ma'aurata
bab.
Sannan
sukace babu wani Hadīsi da ya tabbata daga bakin Mαnzon AAʟʟah Sallallahu alaihi
Wasallam da yayi magana akan wannan Mas'ala, balle harkaji ana cewa wai duk
wanda yamutu yanayi to ranar Alƙiyama za a tasheshi yayiwa hannunsa ciki, babu Hadīsin
da ya inganta akanhaka,
Saidai
kuma agaskiya maganar da mafi yawan Malamai suka tafi akanta na cewa
haramunne, ko shakka babu cewa maganarsu tana da ƙarfi
sosai, danhaka dai zaman lafiya
anan shine, barin aikata Istimna'i shi yafi zama alkhari, musamman dan Mutum ya
kuɓutar da kansa daga
cikin Saɓanin-Malamai,
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'αʟαм
AMSAWA
Mυѕтαρнα Uѕмαn
08032531505
Doмυп
пεмαп ƙaяıп вαчaпı sαı
αdυвα шαɗαппαп
ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
↓↓↓
"اَلْـمُـصَـنَّـف" (7/392)
"أَضْـوَاءُ الْـبَـيَـانِ"
(5/525)
"اَلْـمـُحَلَّـىٰ بِـالْآثَـارِ"
(6/175)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
Hukuncin Masu Masturbation Ta Waya
TAMBAYA (117)❓
Assalamu alaikum warahmatullah. Tamabayata shine me hukuncin
saurayi da budurwa wanda suke Masturbating kansu in suna waya kuma bayan basuyi
aure bah. Bissalam
AMSA❗
Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhu
✍️AMSA A TAQAICE
(Kamata yayi idan har da gaske suna son auren to suyi haquri
tun da idan sunyi aure ya halatta suyi abinda yafi masturbating din la'akari da
yin masturbation yana kawo illa ga masu yi don haka haramun ne duk da cewar
wasu malaman sun ce mubah ne tun da bai kai matsayin babbar zina ba)
Bismillaahir Rahmaanir Raheem
Ijmain malamai sun tafi akan cewar haramun ne mutum ya dinga
wasa da gabansa har ya fitar da maniyyi duk da dai wasu sunce mubah ne tun da
bai kai matsayin aikata babbar zina ba
Idan har aikata hakan haramun ne ko abin kyama ne to ina
kuma ace mace da namiji baligai da basuyi aure ba su dinga masturbating ta waya
har su biyawa kansu buqata?
Kamata yayi idan har da gaske suna son aure to suyi haquri
tun da idan sunyi aure ya halatta suyi abinda yafi masturbating din
Wannan masturbating da suke zai iya haifar musu da fadawa
tarkon shaidan idan sun hadu a zahiri wato zasu iya aikata zina. Wannan idan ma
an ajiye maganar cutarwar da masturbation yake haifarwa ga lafiyar mutum kenan
A shawarce, su dinga azumin litinin da alhamis ko azumin
13,14 da 15 na kowanne wata ko kuma irin azumin Annabi Dawud (Alaihis Salam)
wanda yake azumi yau gobe ya sha, kamar yanda Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) ya koyar domin kuwa azumi yana katange mutum daga aikata alfasha
kamar yanda ya tabbata a cikin Qur'ani
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.