Dafa-Dukan Doya
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Doya
ii. Gishiri
iii. Kayan
miya
iv. Ruwa
Ita ma wannan dafa-duka kamar yadda ake yin sauran dafa-duka haka za a yi ta. Inda suka bambanta da sauran shi ne, ba a saka mata wasu ganyaye. Haka nan za a dafa ta tare da da kayan miya haɗi da gishiri. Haka kuma ana iya dafa doyar ita kaɗai ba tare da an saka mata komai a cikinta ba; wato ko fere doya ba za a yi ba. Da zarar an farfasa ta, haka nan za a saka ta a cikin tukunya tare da gishiri da ruwa, a dafa.
Dafa-Dukan Dankalin Turawa da Ƙwai
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Dankalin Turawa
iii. Gishiri
iv. Kayan ciki
v. Kayan yaji
vi. Kori
vii. Magi
viii. Mai
ix. Ƙwai
x. Ruwa
xi. Tafarnuwa
xii. Tarugu
xiii. Tattasai
xiv. Tumatur
Za a fere dankali a wanke shi, sai a saka mashi gishiri a sama a dafa shi shi kaɗai. Kada a bar shi ya nune sosai. Da zarar ya ɗan nuna sama-sama, sai a fitar da shi a tace da kwando a rufe. Daga nan sai
a jajjaga tumatur da tattasai da tarugu da albasa a aje gefe ɗaya.
Sannan a daka kayan yaji a saka a cikin jajjagen. Bayan nan za a wanke kayan
ciki sosai a saka magi da albasa da kori. Kada a saka ruwa a cikin tafasa, zai
tafasa da sauran ruwan da ke ciki. Za a soya mai a cikin tukunya a saka albasa, idan ya soyu a kawo jajjagen kayan
miya a saka, a yi ta juya su sai sun soyu sosai.
Bayan sun soyu,
za a ɗauko kayan cikin nan da aka tafasa a
saka a ci gaba da juyawa. Sannan a ɗauko ƙwai a fasa gwargwadon yadda ake buƙata a kaɗe
shi sosai a saka yankakken
tarugu da dakakkiyar
tafarnuwa a zuba a cikin kayan ciki da jajjage a ci gaba da juyawa har sai ya
fitar da mai. Za a ɗauko dankalin nan a saka shi ciki, a
riƙa juyawa a hankali har sai ya haɗe, sai a jaye wuta saboda kar ya farfashe a ciki. Da zarar ya ƙarasa, to dafa-dukan dankalin Turawa da ƙwai ta kammala.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.