Kafilun, ishi bayinka,
Ka ishe ni da girmanKa,
Ka faɗi na kiraye Ka,
Ka ji na faɗi sunanKa,
Kai da kaya duk naKa.
Rabbana, Ka yi min buɗi,
Nai nufin wani ɗan taɗi,
Wanda babu ciki murɗi,
Damina in ta faɗi,
Duk mu ka san albarka.
Kar na kai magana nesa,
Duk abin da ya bunƙasa,
Yadda duk ya birinƙinsa,
Damina ce farkonsa,
Tun da dai asali shuka.
Damina in ta bauɗe,
Al’amurra sun ruɗe,
Arzuka sun guggurɗe,
Duk dabaru sun murɗe,
Warware su akwai shakka.
Damina, ba don ke ba,
Da ba a ci, ba a sha ba,
Har a nemi hawan daba,
Duk a ba a yi waɗannan ba,
Ban da kin yi ruwan shuka.
Damina babban maki,
Kyan cikinki da bayanki,
Duniya duk ta so ki,
Ba ta kuri sai naki,
Damina mai albarka.
Damina na gaishe ki,
Nai kirari dominki,
Wanda ya gwada ƙyamarki,
Yai abin ban mamaki,
Ke ka zub da ruwan shuka.
Marhaban da isowarki,
Mun ji daɗin saukarki,
Sai mu ce miki, lale ki,
Godiyarmu da ke ninki,
Damina mai albarka.
Gargaɗina, al’umma,
Duk mutum in ya kama,
Ya wuce a yi mai gama,
Sai ya sami abin homa,
Har da ɗimbin albarka.
Mai hatsi ba ya yunwa,
Mai isa ba ya tsiwa,
Gaskiya
ba ta gwiwa,
Murmushinka
da ban shawa,
Damina mai kyan fuska.
Allah bai wa damo gashe,
Arziki, shi ya mai
tushe,
Daminarmu ta yo halshe,
Har fari shi mace mushe,
An yi mai mugun duka.
Ya Mudabbiru, ya Allah,
Kai Ka gyara ma’amalla,
Mun yi roƙo, ya Allah,
Kyauta kome duk jimla,
Damina ta yi albarka.
To maza, na ce,
“Hayya!”,
Duk a zabura, ai niyya,
Karkara, da na alƙarya,
Kowanenmu ya shisshirya,
Duk mu wa rani duka.
Zamani yau ya juya,
Yanzu noman fartanya,
Ya ƙaranta cikin dunya,
Injunanga na kimiyya,
Su ya kyautu mu ɗaɗɗauka.
Don mu je mu yi ayyukka,
Sassabe ya zuwa shuka,
Yau ƙasashen Afrika,
Duk yawanci sun farka,
Ba gayauna, sai eka.
Yanzu noman zamani,
Bincike fanni-fanni,
Ɗan ƙasarmu, shigo ƙarni,
Kwashi takin zamani,
Bunguɗa shi a gonarka.
In da hali, sai mota,
Nem ta noma, tarakta,
In da hali ya ƙanƙanta,
Ko haya ma karɓo ta,
Don ka aikace
gonarka.
Ga nasiha na ƙyafe,
Na bi kome na tsefe,
Kar mu yarda zama gefe,
Mai kuɗi shi ne kyafe,
Wanda ke da abin harka.
To, mutan Nijeriyya,
Na sako babbar murya,
Nai kira don soyayya,
To, mu bai maraɗa kunya,
Masu ƙin
mu da albarka.
Damina in ta kama,
ƙoƙarinmu
shi kankama,
Sai rago, marashin
himma,
Zai nadama sau goma,
Don ƙarancin
albarka.
Yau mutum mai son aiki,
Mai yawan halin kirki,
Tun da rani, sa taki,
Ka ga alheri ninki,
Daminarka da albarka.
Taimako, wane tawul!
Dauriya, ya ta ki-bawul,
ƙamsasa, wane jawul!
Zan daɗe mu garambawul,
Kan batun mai-albarka.
Damina, ke ce Inna,
Mu, zuwanki muke murna,
Don kadan har kin zauna,
Duniya ta amfana,
A wadatu da albarka.
In ƙasa ta busanta,
ƙeƙasa
ta same ta,
Har ta zo ta ƙishirwanta,
Wa akan aiko gunta?
Damina mai albarka.
Sai ta zo kuɓutashe ta,
Girgijenta ya shashe ta,
Tai ado ya irin nata,
Shuke-shuke da
tsirranta,
Sun cika ta da albarka.
‘Yan uwa sai mun gana,
Zantukan da na zazzana,
Ya kamata ku a’auna,
Kila ko ma amfana,
Babu cikas, ba suka.
Nune-nune na nuna,
Allah sanya sun zauna,
Zuciyarku marar ƙuna,
Ma yawaita ciki murna,
Gaskiya sak, ba shakka.
Kun shina tuni ma an ce,
Damina in ta kauce,
Arzuka kuwa sun goce,
Addu’armu ta mece ce?
Allah ba mu ruwan shuka.
Damina mai ban samu,
Mai yawan jinƙai,
Ummu,
Tallafe mu, ki goye mu,
Ba abin da ya dame mu,
Kin raba mu da rarauka.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.