Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Son A Ba Ni Maganin Mallaka Da Na Farin-Jini?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam dan Allah ina so a ban maganin mallaka amma a cikin ayoyin Kur'ani dan na ji an ce akwai, saboda ina son saurayina ga shi za a yi maganar kawo kuɗi, kuma malam wallahi ban da niyyar cutar da shi saboda Allah. Sannan ina so a ba wa kanwata maganin farin jini a temaka.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, ƴar uwa a magana ta gaskiya, wacce take duk wani malami na Allah da Annabi, in dai ba kuɗaɗenku yake son ya karɓe ba, to zai faɗa maku cewa ba wasu ayoyi da Allah ya saukar da sunan ayoyin mallake miji ko saurayi ko na farin jini ga mace, Allah S. W. T. Bai saukar da Alqur'ani da manufar haka ba, sai dai kawai ayoyin Alqur'ani da hadisan Manzon Allah sun bayyana duk hanyoyin da mutum zai bi don ya sami karɓuwa a wurin Allah da wurin bayin Allah.

Kyawawan ɗabi'u da kyautata mu'amala su ne tushe na gaskiya da mutum zai mallake zuciyar abokin rayuwarsa, matuqar babu kyakkyawar mu'amala a tsakanin mata da miji, ko saurayi da budurwa, to tabbas komin siddabarun da boka zai ba mutum ba zai taɓa samun nasarar mallake abokin rayuwarsa ba, in ma ya samu to na ɗan lokaci ne aka yi masa talala kafin Allah ya kama shi, sannan kuma ga fuskantar mummunar makoma a wurin Allah ga wanda yake harka da bokaye da ƴan tsibbu, ko da mai harka da bokaye ko ƴan tsibbu ya ga kamar ya ci nasara, to ya sani ba nasara ya samu ba, talala Allah yake masa domin ya turmutsa shi a Jahannama, saboda duk wanda ya mutu yana mu'amala da waɗannan miyagu to lallai zai haɗu da fushin Allah.

Bisa shawara ga wadda take son mallake mijinta, ko take son ta yi farin jini, to ta dage da yin addu'a ba dare ba rana, kuma ta dage da kyautata mu'amala a tsakaninta da mijinta idan matar aure ce, idan kuma budurwa ce sai ta riqi kyawawan ɗabi'u da addu'a, da jin tsoron Allah a cikin al'amuranta, ta dalilin haka sai Allah ya ba ki nasara a rayuwarki, amma duk wata hanya akasin wannan za ta iya kai mutum ga rasa imaninsa, saboda idan wannan buqata taki aka yi rashin sa'a kika faɗa hannun maras tsoron Allah, to zai ce maki ne akwai maganin farin jini ɗin da na mallaka kuma ta amfani da ayoyin Alqur'ani, wadda kuma qarya ce tsantsa ya faɗa maki.

Saboda wasu ƴan tsibbun suna yin amfani da Alqur'anin ne wajen yaudarar kwastamominsu, shi wanda bai sani ba da zarar ya ga an ɗauko Alqur'ani, ko an karanto wata ayar Alqur'ani, sai ya za ta maganin Allah da Annabi za a ba shi, nan kuwa bai san yaudararsa za a yi ta hanyar amfani da Alqur'anin ba, don haka a yi taka tsan-tsan a koma ga Allah kurum!

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments