Haliƙal halƙi ya Jabbaru,
Ga ni ga kiranKa ya ƙahharu,
Ya Zaljalali ya Sattaru,
Ya Mau-ilal-Ufati ƙadiru,
Jalla komim matsa mini jaya min shi.
Kullum Ka yo swalati Ka ƙara,
Dud da tsira gama su su
jera,
Hag ga Manzon da yai yi
bushara,
Duk Musulmi mu tsira ga
Nara,
Has Sahabbai da Ali aminnai nashi.
Mai tsarewa tsare mu ga sharri,
Mai rabawa raba muna hairi,
Tunkuɗe min haƙon
asharari,
Tun da baiwa gare Ka da ƙari,
Arzikin dud da ban ni da ƙaro min shi.
Mun biɗa inda wanda ka ba mu,
Wanda yai yi mu Shi ka tsaron mu,
Wanda yai yi mu rabo Ya samu,
Ni kiran duk da nai maka amsam min shi.
Ga ni ga kiran ka na ɗaga murya,
Har ƙwarai babu duk jin kumya,
Kai ka ba mai uba da
maraya,
Inda duk zamani yai
juya,
Inda sauƙinka
duk shike juya min shi.
ƙara jin ƙan da Kay
yi ka kyauta,
Kullu yaumin mu ƙara ni’imta,
Sa wadata ta ƙara yawaita,
Don iyawakKa kam mu talauta,
Inda duk za shi tsaurara sa mai tabshi.
Tun da ga zamani ya
sake,
Kai muka kira zama mun
tabke,
Ga shi duk talikai sun
tsunke,
Mai buga ya bi duk ya rabke,
Dud da suna garai nana Shago wai shi.
Ga shi yau shi kaɗai ka kirari,
Yau sabatta mu ɗai shi ka guri,
Ga shi nan ya nufo mu da
sharri,
Mun yi ƙara gare ka ƙdiri,
Tun da kai aƙƙadiru buwayan min shi.
Shago ya yo haruru gare
mu,
Wai nufo tai shi zo shi
tare mu,
Bugun kashi shi ka nufar
shi buge mu,
Agaza Jalla kas shi taɓe mu,
Inda duz za shi zabura dafe min shi.
Ba mu ismi shi tsare mu
gare shi,
Bugu da dwaga gare shi
da naushi,
Wata nufa wadda nag ga
gare shi,
Zabura za shi yi shi yi
taushi,
Sadda duk za shi yunƙura taushe min shi.
Daɗa ku kau Shago ya naɗe damtse,
Inda duk ya nufata a
watse,
Ba a tarbansa dole a
ratse,
Mai bugu har su hanji su katse,
Jalla ni ba ni immi shi tarbe min shi.
Ya fi bom ya fi bindiga
sharri,
Mai bugu shi yi iza shi yi shuri,
Shago farta gare shi da
mari,
Hadda rura garai da
kirari,
Jalla tun ba mu taƙa ba kiyaye min shi.
Shi ka korak ka har shi
matse ka,
Ka so tsayi ga shi ya
rinjai ka,
Gudu kakai ba shi sa shi
shi bar ka,
Inda duk kan nufata shi
bi ka,
Ga halin Shago bai iya jin lallashi.
Har gida shika biya shi
yi taushi,
Da mai gida ya fito shi
tare shi,
Bugu guda shika yi mai
shi saɓe shi,
Shina da rai ga shi ya
gaza tashi,
Ga shi ga ‘yan ɗiyansa
abin zah haushi.
‘Yan ɗiya duk shi bi su shi darje,
In uwa tat tare shi shi
murje,
Ba a jimirin bugunsa a
cije,
Ran faɗa Shago ya ɗara soja,
Ya fi ko soja-manja bugun ban haushi.
Kaɗo ai dole na a gude shi,
Wanda duk yab buga bai
tashi,
Ai bugun kaɗo ni na san shi,
Yaka sa kunnuwanka ka ji
shi,
Kaɗo ba tanƙwara ciki ba tarkoshi.
Bugunka
hanjin mutum shi ka suya,
Zucciyar
taliki shi shi ka tuya,
Wanda
duk kab buga bai kumya,
Bai
gudun cin tuwo bisa hanya,
Ba shi ko shan tayi ga surukkainai.
Maƙetaci kaɗo
ba tuna Allah,
Shi ka koya ma karuwa
salla,
Kaɗo ba kare kumallo da ƙola,
Ba sayen dawo a jingina
dila,
Ci da ɗan Hausa taiba shi ce zal laushi.
Tanƙwaro mai tsawo shi gajarta,
Sa ma guntu tsawo shi
tsawaita,
Kaɗo sa tagumi shi yawaita,
Sa idanu dufu su
dufunta,
Sai gashi garu-garu a ce yai burshi.
Tajiri kam raba shi da
mali,
Kashe manomi bale
dillali,
Karya halshe a ko gaza ƙauli,
Kaɗo sa ɗa shi furfura hali,
Sa shi ‘yan roƙe-roƙe
a ce yai tabshi.
Rabki boka shi bar maka
saye,
ƙum guda hankalinsa shi juye,
Jikkunam maganinsa su
yoye,
Nan da nan gaskiya ta yi
kaye,
Ga kare kwance ya rasa mai shi ko shi.
Tashi bugi kan kilaki ta
koka,
Banna fodad da tay yi ga
fuska,
In fa kaina ka yamutse
bukka,
Sai ta kirci ka sa mata
tsika,
Tsotse naman jikinta ka sa mai kaushi.
Malami kam kashedi gare
shi,
Kai wuce kaɗo kak ka taɓe shi,
Shi mutunci gare shi ka
bar shi,
Shago don Allah kak ka buge shi,
Kaɗo ya rantsa ba shi karatu wai shi.
Ga mareninka ɗan albashi,
Ko wata fam guda aka ba
shi,
Inda duk kag ganai ga
buge shi,
Nan da nan na ka bar shi
da bashi,
Kaito ka bar shi can bisa alwashi shi.
Wuri guda nig ga kaɗo ka tada,
Inda bai son shige musu
fada,
Don gudun kar shi faɗa lifidda,
Masu sulke su bi shi da
rida,
Dole bauɗe ma fada tudun ban kashi.
Gwamma shi dai batun ga
a bar shi,
Ammanin kaɗo dambe gare shi,
ƙasa gudu shika ishe ma su bar shi,
Shi watse kowa cikinta
su tashi,
Ga shi shi ɗai
na bagara ba lallashi.
Shago kam maganinsa du’a’i,
Babu duk Shago ban da
bala’i,
Sai mu roƙa ga wanda ka ma’i,
Shi yi ruwa don mu wanke waba’i,
Babu duk mai rabo mu da Shago sai shi.
Rabbana
mun biɗe
ka karimci,
Sa
Musulmi su ɗebe
talauci,
Kawo
sauƙi
mu jirkita kwanci,
Ba
mu yalwat tufa da abinci,
Ba mu yardakka tare da jinƙai ko shi.
Koma daɗa yin salati ka ƙara,
Nan ga Manzonka Ahma ka ƙara,
Har sahabbai da Ali a
tara,
Nawa laifi da nai yi ka
gyara,
Tun da sunanka Gafiru yafe min shi.
Pensuri daɗa tsaya in huta,
Don dare ya yi sai in
kwanta,
Dubi waƙag ga yau nay yi ta,
Bisa nufar Jalla niw waƙe ta,
Babu mai ba mutum hikima baicin shi.
Godiya Jalla na gama waƙa,
Addu’a niy yi nik ko roƙa,
GunKa domin mu samu haƙiƙa,
Ba mu sunanka kai mai waƙa,
Sai ku ce I/C laƙabin sai
ko shi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.