Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Samun Kauna Da Farin-Jini

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

malan ina san zama mai farin-jini a duk inda nike da kwarjini da kauna a idon jama'ah , Shine nike bukatar taimako cikin wanda Allah y hore maka . Ngd Allah saka d alkairi

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Kaɗan daga cikin abubuwan dake sanya Kauna, Farin-jini da Kwarjini, bugu da kari kuma ayyukan lada ne da suka dace da sunnan Annabi sun haɗa da:

1. Yin fara’a, sakin fuska da murmushi ga mutane tare da Sallama a garesu.

2. Kiran mutane da mafi soyuwan sunayen su, tare da girmamawa cikin salon murya mai daɗi.

3. Girmama na gaba da kimanta na kasa tare da nisantar wulakaci ko tozarci agare su acikin mu’amala ko Magana.

4. Tsafta da cikakken tsare a cikin sutura, abinci, da duk wata mu’amala da mutum yakeyi a rayuwarsa.

5. Yin Ado da kwalliya tare da kamshi da shiga ta kamala.

6. Nuna farinciki yayin farin-cikin mutane, da damuwa acikin damuwarsu tare da bada gudun muwa a cikin rayuwarsu.

7. Gaskiya da rikon amana, tare da taimokon gaskiya ta masu gaskiyar.

8. Kyauta da kawaici, tare da kauda kai da rashin kwaɗayi.

9. Taimako ga mabukata da rashin hasada ga waɗanda Allah ya yi wa ɗaukaka.

10. Adalci da girmama mutane.

11. Hakuri da dogaro ga Allah tare da rashin hadama.

12. Rashin girman kai.

13. Karɓan gyara da nasiha idan mutum yayi kuskure.

14. Jin tsoron Allah da kyautata ibada tare da tsare dokokin Allah.

A karshe, ba zaka iya samun kauna da soyayyan kowa da kowa ba, amma kuma zaka iya canja tsarin rayuwarka ta hanyar kyautata halayenka da dabi’unka har Allah ya soka kuma ka samu kauna daga mafi yawan al’uma.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments