Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shan Maganin Farin Jini

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu'alaikum Malam muna lafia, ya dalibai? Allah yayi mana jagora. Amin. Malam Dan Allah a taimaka a amsa mani wannan tambayar. Malam mutum ne Allah be bashi mijin aure ba, se aka bashi wani maganin wai rinka sha bayan sallar asuba da Nono wanda farar yar fulani ke saidawa ko kuma ya haɗa da yoghurt se yayi addu' a Allah ya biya mashi bukata shi. To Malam menene hukuncin shan irin abubuwannan, dan ni gaskiya basu kwanta mani ba irin abubuwan nan ba. Allah ya saka da alheri. Amin

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Imani da Qaddara yana daga cikin Ginshikan Imani. Kuma dogaro ga Allah da kuma juyawa zuwa gareshi ko yaushe yana daga cikin alamomin Imani da Qaddara ɗin.

Wannan abin da suka ce ki yi ɗin yana kunshe da surkulle ta ɓangaren kalar irin Matar da zaki sayi nonon awajenta. Da kuma yanayin yadda za'ayi amfani da maganin. Don haka ki watsar da irin waɗannan surkullen. Ki rike Alqur'ani da Sunnar Manzon Allah da kuma fa'idodin addu'o'in da Malamai masu tsoron Allah suka fitar.

Ga sunayen Allah nan guda 99 duk wacce take neman Mijin aure ta rika yawaita ambaton Allah da Waɗannan sunayen sannan tayi Salati ga Manzon Allah sannan tayi addu'arta. Bayan ta gama addu'ar kuma sai ta Qara maimaita salati ga Manzon Allah . Akwai hadisi daga Manzon Allah cewa Duk wanda ya kira sunan Allah "YA AR-HAMAR RAHIMEEN" Sau uku, to wani Mala'ika zai tsaya kusa da shi yace masa "GA ARAHMANUR RAHIMEENA NAN YA JUYO GAREKA". Nan take duk abin da mutum ya roka Allah zai amsa masa.

Ki riki waɗannan addu'o'in ki kyale waɗancan abubuwan. Allah zai yaye miki damuwarki, Zai biya miki bukatarki.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments