𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum don Allah mlm Ina tambaya ne game da Magani irin na Mata akwai magani za ka ga mace ne take siyar da shi maganganun Nan Mata ne za ka ga an ce idan kin kwace tuwon ki mushiyar tuwon ki kankare shi tuwon da ke jikin mushiyar ki haɗa da garin zogalen ki zuba mishi a Miya ya ci, wannan mlm gaskiya Ni a ganina Bai halatta ba tambaya dai nake Yi hakan ya halatta kuwa? Sa'annan Kuma za ka maganin Mata ne Amma hunra ne sai ace wannan Hunran su shafa shi kasan Matar ki ko a shafa shi a Jirkin ki ko Kan Karan Hancin ki ko goshin ki idan mijin ki ya shigo gida ya ji wannan kamshin Zaki ga Ydda zai Rika Jin son ki ko zai Rika makale miki duk abun Kika Tambaye shi a wannan ranar Zaki samu ga shi dai ba gurin boka aka amso ba Mace ce ta zo a gida ta kawo da sunan maganin mata take siyarwa idan kamar kace Kai kana Jin tsoron irin wannan maganin kamar sidda baru sai su ce ai garin ita ce magani ne.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam:
Toh Malama Idan har Halin Mace Matar Aure Yana
dakyau, Tarbiyyar ta, da Darajar ta, da Mutuncin ta, Ƙimar ta da kuma Martabatan ta, da iya sanin
Zamantakewar Aure, da iya Sanin Kissar mata, da iya Ladabi da Biyayya duk abun
da mijin ki zai ce kiyi a take kike tashi kiyi ko ma menene wannan abun matukar
ba Saɓon Allah bane.
Iya girke-girke na zamani da wadda ba na zamani
ba, da iya kwalliya kullum kina cikin tsaftar jikin ki, Yin Lalle kullum a
Hannayen ki da kafafun ki, kullum a Ɗakin ki ya shigo Turare ne ke tashi, Tsaftar Gashin Kanki, Farjin ki komai
naki cikin gidan sa, da iya tarairayan Mijin ta, Malama Idan har mace ta iya waɗannan abubuwan da ma wasu dabarun ku na mata, toh wallahi
Bai sai ta Nemi wani Maganin Hunra Wai domin Mijin ta ba, Ke kanki idan kin
Cika Mace Magani ce ba sai kin nemo wani ba, wannan kaɗai da wasu dabarun ku, zai sa wallahi idan kina tare da
Mijin ki sai wasu su Rika cewa ai Asiri kike Masa shiyasa yake rudewa a kanki
kamar zai Mutu, Alhalin kawai iya sanin Zamantakewar Auren ki ne, da yadda Za
ki Tsarrafa Namiji, shine kawai kike da ilmi akai shiyasa ake ganin kamar kin
Yi Masa Asiri ne Alhalin ke master ce a gurin iya rike Miji.
Amma idan kin ga Mace Wai sai ta Kara da Maganin
Mallakar Miji irin yadda yanzu Mata Suke Yi, ko kuma wai a yi magani Me Kwado
da key 🔐, toh wallahi da
Sauran ta ina ji har yanzu Bata Cika Macen ba, Amma duk Matar Auren da ta Cika
Mace, toh Bata Neman wani Maganin Hunra ko wanin sa domin Mallakar Miji ko Miji
ya Kara son ta ya Rika yi Mata duk abun da ta ke so, ita kanta wallahi maganin
ne, haba ai ku mata Kuna da Hanyoyi da dama Wadda idan Kuna yin su Mijin ki zai
ba ki Kyautar ma ba tare da ya san ya ba ki shi ba, sa'annan duk abun da kike
so a cikin gaggawa jikin sa na bari zai miki shi Kai wani ko ba ki nema ba zai
miki dalilin kawai kin isa Mace kin cika Mace.
Sabida Haka Ni a gurina duk Macen da Wai sai ta yi
Haka ta samu Mijin ta ya makale mata, ya ji Yana son ta har ya Bata wani kyauta
ko Kuma ya ce Yana son ta Kamar Yaya, toh wallahi har gobe da Sauran ta a cikin
Mata, ta chanja tunani daga Cewa itama ta Cika Mace gaskiya ba ta Cika Mace ba
duk Macen da ta Kai Mace bata neman magani domin Namiji ke kanki maganin ne.
Sa'annan kin San duk abun da mutum zai shafa ko
zai Sha ya je gaban wani, Shi wannan ya ɗauki kuɗi ko wani kyauta ya ba shi, toh ai wannan Bai halatta ba,
domin kusan ɗaya yake da ayiwa mutum
Asiri ki samu abun da kike so, Malamai suka ce wannan ma Sihiri ne, kiyiwa
mutum abu ki je gaban sa, shi Kuma ya ɗauki Kuɗi ko kyauta ya ba ki ba tare da yayi niyyar ba a ransa
ba, inda a Lokacin Hankalin sa ɗaya ne, wato Bai
ji kamshi ko maganin da kika yi ai da ba zai taɓa ba ki abun ba, amma kin sa wani Abu a jikin ki ko kin
ba shi ya ci a miya kin batar da hankalin sa, ya ce Yana son ki har ya ba ki
kyauta, kin ga kenan bai bayar da shi domin Allah ba, sai ga dalilin wannan
maganin da Kika saka ya ɗauke masa
Hankalin sa ya ba ki abun da kike so, Kin ga wannan bai kamata ba Haramun ne
wannan.
Don Haka wajibi ne Mata su ji tsoron Allah gurin
Dena yin irin waɗannan abubuwan
na kawar da hankalin Mazajen su domin wai su samu karbuwa Haramun ne kuma
Sihiri ne.
Ya Halatta Ki Siya Magani domin Lafiyar jikin ki,
ko Gyaran Jikin ki, ko na Kamshi a jikin ki Turaren a iya cikin gidan ki, ko na
Tsaftar Cikin Gidan ki da Ɗakin ku da sauran su. Amma duk abun da za a shafa shi wani yayi Kyautar da
bai da Niyya ga Wadda ya shafa abun ya zo gaban sa, toh an koma wani Ɓangaren da ba a so na Saɓawa Allah, Allah ya tsare.
Sabida Haka Mace ta Koyi Shagwaba, ki koyi
kisisina ki koyi Yadda ake tarairayan Namiji, ki koyi girke-girke irin na
Zamani, ki koyi yadda za ki Tsarrafa Mijin ki ta kowane Ɓangare ne, yanzu misalin ace ke da Jaririn ki shin
Shima Jaririn ki sai kin yi Masa irin wannan ne zai so ki? toh Shi ma Mijin ki
hakane, dole ne ki San komai a matsayin ki na Mace, ki Rika yin ibadar Allah
akan Lokacin sa, ki koyi yadda ake yiwa Miji Ladabi da Biyayya ba tare da an
shiga Haƙƙin Allah ba, Uwa Uba ki
koyi yadda ake yin Tsaftar Jiki, Tsaftar Farjin ki, Tsaftar Suturar Ki, Tsaftar
Ɗakin ki, iya kwalliya
kala-Kala, Lallen ki Kullum Sabo yake, Tsaftar Cikin Gidan ki da Yaran ki Idan
akwai su, Idan Mahaifiyar Mijin ki tana gidan Kuna tare gida 1 da ita, ki tare
a gurin ta komai ta ke so ki kaskantar da kanki ki Rika Yi mata ki Rika kula da
ita sosai, Kai har da Tsaftar Ɗakin ta da Sauran su, ki Rika Shiga kina gyara mata shi domin kema Yar ta
ce, Abinci ki Rika dafawa irin yadda take so, idan ma ba ku tare gida 1, ace
Duk sati ki Rika Zuwa kina yini a gurin ta kina kula da ita, wlh ko kin Yi
Laifi zata goyi bayan ki ta ce ba kiyi Laifin ba, Alhalin Kuma kin aikata, kina
kula da Mijin ki, dukiyar sa Kayan Abincin Sa, ba ki yin Almubazaranci da shi,
komai ya ce kiyi Za ki tashi kiyi a Lokacin ki yi Masa abun da yake so, idan ya
ce Bari za ki Bari Nan take ba tare da ya sake yin Baki na 2 ba.
Toh wallahi duk Mace Matar Auren da take yin irin
waɗannan abubuwan, ko Mijin ta da can Yana da Niyyar Kara
Aure toh a Yanzu zai Fasa, Babu Namijin da Matar sa zata Rika Yi Masa irin
wannan abubuwan ya ce zai Kara Aure, domin zai Yi tunanin kada ya Kara Auren ya
Auro masifa, Sa'annan Babu Macen da zata Rika yin haka ma Mijin ace Mijin shima
Bai kula da ita, Bai ba ta Kyautar wani Abun da take so matukar Mijin Yana da
shi wallahi kullum zai Rika Yi Mata 💯.
Sai dai ana iya samun wasu Mazãjen da ko kina Yi
musu kina iya bakin kokarin ki, ba su San ma kina Yi ba, toh irin waɗannan Mazajen Sai Allah kawai ba kiyi dacen Miji ba wlh,
Amma duk Macen da zata Rika yiwa Mijin ta irin wannan ko ta Rika yiwa Mijin ta
sama da hakan, wallahi sai kin ga Chanji sosai.
Toh Amma ba za ku yi ba, Kun Fi son kawai a ɗauki Kuɗi Mai yawa a je
gurin Bokaye ko Malamai a Kashe shi a iska, Wai ai kina son Mijin ki ya So ki
sosai sama da komai a rayuwar sa, Kuma idan kin ce bani Abu Kaza ya ɗauka ya ba ki Nan take, Kin ga ai wannan Zalunci ne,
domin ke ba kiyi abun da za a kyautata Miki ba, Amma Kuma kin nema a ba ki Abu,
kina son ki samu a Banza shi kuma ya Ƙi ba ki, sai Kika ce Bari ki yi Magani ya ba ki amma ba da Son sa ba, me
matsayin ki a gurin Allah? Ga abun da Shari'ar Musulunci ya ce kuyiwa Mazãjen
ku Amma ba zakuyi ba sabida tun can Iyayen ku sun muku Hudubar Cewa namiji ba Ɗan goyo bane, ko Kuma Ƙawayen ki sun zuga ki
Cewa kada ki Sakewa Mijin ki Wai zai Raine ki, don Allah idan ba ki Sakewa
Mijin ki ba Waye Za ki Sakewa? Ɗaukar Shawarar Banza Wadda ba zai gyara Zamantakewar Auren ku yayi Miki
kyau ba, toh shiyasa Wai Mace sai ta Kara da Yin Magani, toh Wallahi Yar Uwa ba
ki Cika Mace ba in dai Wai sai kin yiwa Mijin ki magani kafin ya ce Yana Kaunar
ki Sama da komai, kafin ya ɗauki wani abu na
kyauta ya ba ki, toh ba ki Cika Mace ba.
Wadda ta Cika Mace tana ji ita kanki Macen ce,
wallahi ita kanta ma Magani ne bata zuwa gurin kowa wai don neman Magani akan
Mijin ta ya so ta, domin ta San cewa tana da Maganin a tare da ita, maganin
Kuma shine abun na ambata a sama. Don Haka Mata a ji tsoron Allah da Kuɗin da Za ki Kashe a can a banza a samu Zunubai, gara kin ɗauki kuɗin kin ci nama
da shi tunda ke ba ki bayar da Sadaka, toh gara kin ci namar ki da shi kin San
kin ci Abu. Dafatan kin gane Koh? A tayamu Yaɗa shi domin a gane Gaskiya da ɓata.
WALLAHU A'ALAMU.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.