Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Waƙar Na Dadada
Sunan Nadada Ali a garin gidan bisa yake, wato garin da mahaifin
Amali ya koma da zama. Shi ma Amali ya yi masa waƙar ne saboda shahararsa ga aikin noma.
G/Waƙa : Ya biya,
: Mai kiɗin manoma,
: Mu kai duman,
: Mu gidan Nadada.
Jagora: In
kai duma,
: In gano na Nadada.
‘Y/Amshi: Mu samu gero,
: Abin dakawa,
Jagora: Goɗiya yay,
: Yi man ta kaina,
: Ya ba ni do..,
: Ki na hwan tamanin,
: Ya ba ni sirdin,
: Da zan azawa,
‘Y/Amshi: Amali sai,
: Godiya ga Ƙwazozo[1],
: Ta yi sir..,
: Din zanen atanhwa,
: Taho-taho,
: Ba ta sa ni in zo,
: Wuce-wuce,
: Ba ta ɓata raina,
: Da hankalina,
: Ina da wayau,
: Amali na san,
: Idon masoya,
: Ina ganin,
: masu son kiɗina,
: Ina ganin,
: Wanda ba ya so na,
: Wahabu Allah,
: Ka ceci ɗan Jijji,
: Inda shegen,
: Da ba ya sona.
: Gadauniya[2],
: Mai sabatta burgu,
: Ina gani nai,
: Da rege-rege,
: Ina gani nai,
: Da kutce-kutce,
: Ya ɗora yawo,
: Cikin gidaje,
: Ya ɗora yawo,
: Cikin riheni[3],
: Ya ɗora yawo,
: Cikin mutane,
: Ku daƙile,
: Ƙaddara ta
shahe shi,
: Tunda yac,
: Ce yana iyawa.
‘Y/Amshi:
Nadada mai,
: Lahiyag gizago,
: Cikin gida,
: Ba ka jin hwaɗa nai,
: Cikin gari,
: Ba ka jin hwaɗa nai,
: Amma a ko,
: Ma cikin mazaje,
: A ɗauki kal..,
: Me a ɗaura walki,
: A ɗaura walki,
: A kama gabce,
: Ka iske ƙa..,
: To yana hawaye.
‘Y/Amshi:
Dabaibaya,
: Mai tsayad da jaki,
: Ta kinkime,
: Ta hana shi motci,
: Kai had da do,
: Ki tana riƙewa,
: Ga rijiya,
: Nan gaba tamanin,
: Mutum ya hwa,
: Ɗa ta anshi
rainai,
: Maza ku sake,
: Shiri na ‘ya Ali,
: Sai mutum wan,
: Da yaj ji kainai.
‘Y/Amshi:
Nadada a..,
: A ka kai da Jatau?
: Amali ya kwa..,
: Na ba ta gari[4],
: Ya koma ya,
: Tashi bai kara[5] ba,
: Inda kamab,
: Ba ka taka kimshe,
: Da sai mu ce,
: Ma halin rashi ne,
: Amma da yaz,
: Zan kana da kimshe[6],
: In baka ‘yam..,
: Man ka ba ni ɗauke,
: Mu samu gero abin dakawa.
: Ya biya,
: Mai kiɗin manoma,
: Mu kai duman,
: Mu gidan Nadada.
Jagora: Nadada ya,
: Ba ni bai hana ba,
: Ya koma ya,
: Ba ni ya daɗa man,
: Nadada a,
: A kakai da taro,
: Gida yana,
: So dawa tana so,
: Waɗanga na,
: So waɗanga na so,
: Waɗanga na,
: Son ka ba su ɗauke[7],
: Waɗanga na,
: So ka ba su rance,
‘Y/Amshi: Waɗanga na,
: So ka ba su kyauta.
: Ya biya,
: Mai kiɗin manoma,
: Mu kai duman,
: Mu gidan Nadada.
Jagora: Da
arziki,
: Na irin na yanzu,
: Da arziki,
: Na ina da raina,
: Ina da ƙan..,
: Ne ina da yanne[8],
: Ina da ‘ya..,
: ’Ya irin na kaina,
: Akwai riko,
: Da ina da keke,
: Ina da sha,
: Nu ina da jakkai,
: Ina da do,
: Ki ina da mashin,
: Ina da ge,
: Ro abin dakawa,
: Akwai tuhwa,
: Hin da za ni sa wa,
: Ina da kuɗ,
: Ɗi abin
kashewa.
‘Y/Amshi: Amali sai,
: Godiya ga Jabbaru,
: Shi da yac,
: Ce hakanga Jatau.
: Ya biya,
: Mai kiɗin manoma,
: Mu kai duman,
: Mu gidan Nadada.
Jagora: Allah
ubana Ubangijina,
: Ubangiji,
: Wanda adda sheɗa,[9]
: Yana gani,
: Ba da ijjiya ba,
: Shi ne ka ji,
: Ba da kunnuwa ba,
: Sarkin da ba,
: A kiɗa ma ganga,
: Sarkin da ba,
: A kiɗa ma kotso,
: Sarkin da ba,
: A kiɗa ma goge,
: Sarkin da ba,
: A ganin naɗinai,
: Sarkin da ba,
: A ganin hito nai,
: Sarkin da ba,
: A gani da riga,
: Sarkin da ba,
: A gani da wando,
: Balle agogo,
: Da sa tabarau,
: Ikon ka shi,
: Ne abin ruhwanka,
: In Ya yi hannu,
: Yana ƙahwahu,
: In Yai hwarut,
: Ta Yana akaihu,
: In Ya yi hanci,
: Yana idanu,
: In Ya yi hal,
: She Yana haƙori,
: In banda Shi wa,
: Ka yin hakanga?
‘Y/Amshi: Mu
san da Allah,
: Mu gyara gobenmu,
: Kam mu saɓa,
: Ma lahirarmu,
: Ya biya,
: Mai kiɗin manoma,
: Mu kai duman,
: Mu gidan Nadada.
Jagora: Mahaukaci,
: Bai ci duniya ba,
: Mahaukaci,
: Bai ci duniya ba,
: Ku gane ko,
: Ya ci bai sani ba,
: Abin da ak,
: Kyau ga ɗan musulmi,
: In ka ji da..,
: Ɗi tuna da
gobe,
: In ka ji ɗwa..,
: Ci tuna da gobe,
: Tuna da sar,
: Kin da yay yi ranka,
: Ka san da shi,
: Yah halicci ranka,
: Ka gane shi,
: Ne marar iyaka,
: Ka hangi ramen[10],
: Da za a sa ka,
: Kowa ka di,
: Bin hakanga Jatau,
: Ai bashi gurin,
: Ya tanka ɓanna,
: Koway yi ɓan..,
: Na tana ga kainai,
: In ya yi gya,
: Ra shina ga kainai.
: Ya Rasulu,
: Ya kyauta,
‘Y/Amshi:
Ƙarshenmu,
: Inji Ɗan,
: Iro mai tahwashe,[11]
: Ya biya,
: Mai kiɗin manoma,
: Mu kai duman,
: Mu gidan Nadada.
Jagora: In
kai duma,
: In gano Nadada.
‘Y/Amshi: Mu
samu ge..,
: Ro abin dakawa.
Jagora: Rijiya,
: Ce gaba tamanin,
: Mutum ya hwa,
: Ɗa ta anshi
rainai,
: Maza ku sake
shiri.
‘Y/Amshi: Na
‘yar Ali,
: Sai mutum wan,
: Da yaj ji kainai,
: Ya biya,
: Mai kiɗin manoma,
: Mu kai duman,
: Mu gidan Nadada.
[1] Sunan mace ne.
[2] Tafiya a ruɗe kamar ba a san inda za a je
ba.
[3] Rumbuna.
[4] Dawa ta dakawa – wato wadda ake mayarwa gari
don yin tuwo,
[5] Cin abincin safe wato kari.
[6] Tsara dawa ko gero ko dai wani amfanin gona a
cikin rumbu.
[7] Gudummuwa.
[8] Yayye.
[9] Numfashi
[10] Kabari
[11] Gangunan kiɗa
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.