Ticker

6/recent/ticker-posts

Aikau Jikan Tayawo

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Aikau Jikan Tayawo

Malam Musa almajiri ne kuma manomi ana kiransa Aikau, shi ma a garin  Sububu yake kuma ɗan’uwan Amali ne, yadda zumuncin yake shi ne mahaifiyar Aikau ita ce ‘yar macce shi kuma Amali shi ne ɗan namiji, wato abokan wasan juna ne.

 

 G/Waƙa : Ya riƙa noma,

  : Da gaskiya na Bakwai,

: Bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen[1] hwashin ƙasa.

 

Jagora: Ya riƙa noma,

  : Da gaskiya na Bakwai,

: Bai saba ba da gida,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Dabgi[2] mai hwashin ƙasa, ɗan Isah.

‘Y/Amshi: Ya riƙa noma,

  : Da gaskiya na Bakwai,

: Bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

Jagora: Riƙa kada gona ta kwana ɗan Mamman,

  : Jagu[3] mai awon ƙasa ɗan Isah.

 ‘Y/Amshi   : Riƙa kada noma ya kwana,

: Ɗan Mamman,

  : Gyado[4] mai awon ƙasa,

 

 Jagora: Kana yi ma gona kamar gudun ƙato. x2

  : In ya hangi gobara,

: Har in yaz zan gidan su tak kama,

  : Ban san mai tare shi ba,

    ‘Y/Amshi: Rannan ko galbi[5] as saman hanya,

  : Sai dai yai ƙire biyu.

  : Ya riƙa noma,

  : Da gaskiya na Bakwai,

: Bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

   

Jagora: In dai sallah ka kai  bar tsahi,

: Ba ka dai gadi yinta ba.

: In kuma tsahin ka kai ka bar sallah,

: Ka san ba su gamuwa.

    ‘Y/Amshi: Ku diba idanun mutum kamar maye,

  : Jawur ba su da hwari.

  : Ya riƙa noma,

  : Da gaskiya na Bakwai,

: Bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

    

Jagora: In dai sallah ka kai  bar tsahi,

: Ba ka dai gadi yinta ba.

: In kuma tsahin ka kai ka bar sallah,

: Ka san ba su gamuwa.

    ‘Y/Amshi: Ku diba idanun mutum kamar maye,

  : Jawur ba su da hwari.

  : Ya riƙa noma,

  : Da gaskiya na Bakwai,

: Bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

   Jagora: Aikau har inda nig ganai arne,

: Bai san yau da gobe ba.x2

    ‘Y/Amshi: Da duk kac ce yau da gobe Sai Allah,

: Sai dai yai ta dariya.

 

  Jagora: Kuma ba shi zuwa idi,

   ‘Y/Amshi: Bai zuwa Jumu’a,

  : Kada ‘yanyara su ganai.

  : Ya riƙa noma,

  : Da gaskiya na Bakwai,

: Bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

  Jagora: Riƙa kada gona ta kwana ɗan Mamman,

  : Jagu[6] mai jiran ruwa ɗan Isah.

   ‘Y/Amshi: Riƙa kada gona ta kwana ɗan Mamman,

  : Gyado mai awon ƙasa.

 

  Jagora: Yarinya za ta kai hura daji,

  : Tad dace da Dugumi,

  : Tac ce Aikau irin gidan Mamman,

  : Aikau ba ka dariya!

    ‘Y/Amshi: Yac ce bari don kak ki sa ni in dara,

  : In watce maku maza!

: Ya riƙa noma,

  : Da gaskiya na Bakwai,

: Bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

Jagora: Tac ce Aikau ba ka dariya,

  : Arne ko diddigin da munka iya,

  : Ban ce ka iya shi ba,

  : Arne ko kwarmaton da munka iya,

  : Ban ce ka iya shi ba,

  : Aikau ko jangirad da munka iya,

  : Ban ce ka iya shi ba,

  : Koko Aikau ba ka da gira?

   ‘Y/Amshi: Yana da giratai rashin kulawa ne,

  : Bai koma ma kanku ba.

: Ya riƙa noma,

  : Da gaskiya na Bakwai,

: Bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

  Jagora: Ai yau da ka ja wan Bakwai ga noma,

   ‘Y/Amshi: Ƙara ka dace da ƙaddara,

: Ta hana maka halin zuwa gida.

 

  Jagora: Ai yau da ka ja wan Bakwai ga noma,

   ‘Y/Amshi: Ƙara ka hau goriba ka hwaɗi ka suma,

: A hesa maka ruwa,

  : Ya riƙa noma da gaskiya,

  : Na Bakwai bai saba da zama,

  : Aikau jikan Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

  Jagora: Ni dai aikau yadda nig ganai,

: Ya yi tabi’a[7] bakwai hwara,

   ‘Y/Amshi: Kuma ya yi tabi’a bakwai baƙa.x2

 

  Jagora: Tabi’a Aikau hwara guda,

: Ya kira ka ya miƙa maka tuwo,

   ‘Y/Amshi: In kac ci ya miƙa maka hura.

  : Ya riƙa noma da gaskiya,

  : Na bakwai bai saba zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Kukelin hwashin ƙasa.

 

 Jagora: Tabi’ar Aikau hwara guda,

: Ya kira ka ya ɗamra[8] maka hatsi.

  ‘Y/Amshi: Ya riƙa noma da gaskiya,

  : Na bakwai bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

Jagora: Tabi’ar Aikau hwara guda sawo maka,

  : Doki kana hawa,

  ‘Y/Amshi: Ya riƙa noma da gaskiya,

  : Na bakwai bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

Jagora: Tabi’ar Aikau hwara guda,

: Ya zuba maka kubta kana ƙawa.

: Tabi’ar Aikau hwara guda,

: Ya gama ka da kuɗin kashi kuma.

: Tabi’ar Aikau hwara guda,

  ‘Y/Amshi: Anne ba ka san yi da ba da wani.

  : Ya riƙa noma da gaskiya,

 : Na bakwai bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen  hwashin ƙasa.

 

Jagora: Tabi’ar Aikau baƙa guda,

: Ya sakamma su tsutsa ga karkara,

 ‘Y/Amshi: Ta kashe musu shikka suna gani,

  : Ya riƙa noma da gaskiya,

  ; Na bakwai bai saba ba da zama,

  : Aikau jikin Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

 Jagora: Tabi’ar Aikau baƙa guda,

: Ya sakam maka ciwon barin gida,

  ‘Y/Amshi: Kuma ba ka biɗa kai ta dawara[9].

  : Ya riƙa noma da gaskiya,

  ; Na bakwai bai saba da zama,

  : Aikau jikan Tayawo ɗan Maman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

Jagora: Tabi’ar Aikau baƙa guda,

   : Ya sakam maka ciwo ga damana,

 ‘Y/Amshi: Kowa na daji kana gida,

  : Ya riƙa noma da gaskiya, ,

  : Na bakwai bai saba da zama, ,

  : Aikau jikan Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

Jagora: Tabi’ar Aikau baƙa guda,

: Ya kira ka ya nuna ga aljana,

‘Y/Amshi: Ta riƙe ka ta tsotce maka jini,

 

     Jagora: Tabi’ar Aikau baƙa gudu,

  : Dab baya garai baya dibuwa.

‘Y/Amshi: In kad dubai kai ta dunduni[10],

  : Ya riƙa noma da gaskiya,

  : Aikau jikan Tayawo ɗan Mamman,

  : Kunkelen hwashin ƙasa.

 

     Jagora: Kyawon yaro ya auri yarinya,

  : Shi ak kyau hakanga dai.

: Kyawon yaro shi auri yarinya,

: Ga kyawonta ga hali.

: Kyawon yaro ya auri yarinya,

: Ga kyawo da natsuwa,

; Kuma dus sadda yas shigo ɗakin,

: Ta zanna mashi gado.

: Kuma dus sadda tag ganai ɗakin,

: Ga shanya tana yi mai,

: Sai ta yi ban hihhike[11],

: Ta kyabta idonta,

: Ta ɗauka mashi  gira.

: In wani wayau gareshi ta anshe,

: Rannan bashi da shiya,

; Sai ka ga yaro shina rawa da haɓa,

: Ta hyaɗa shi ga gado.

: Ba ta bari nai hita cikin ɗakin,

: Sai ta ƙoshi da shiya,

: To ko ta bashshi ya hito ɗakin,

: Ba shawad da zai gani.

 ‘Y/Amshi: Ai duw wata shawa tana cikin,

  : Ɗakin dawo wa yakai maza.

  : Ya riƙa noma da gaskiya,

  : Na bakwai bai saba ba da zama,

: Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

: Kunkelen hwashin ƙasa.

 

     Jagora: Kyawon yaro ya auri yarinya,

  : Shi ak kyau hakanga dai,

 ‘Y/Amshi: Baran wani ya kwashi raƙumad daji,

  : Bai gane ma kanta ba,

  : Ba ta da kyau,

: Ta kare ga kunkuru,

  : Ga ƙaton ciki kuma.



[1]  Ƙato mai ƙarfi

[2]  Wata dabba ce mai haƙora zage-zage, mai tonon ƙasa da haƙoransa ya shige da sauri idan an koro shi za a kama shi.

[3]  Wata dabba ce mai tonon rame da sauri.

[4]  Wata dabba ce mai haƙora zago-zago, wanda yake amfani das u wajen tonon rami idan an biyo shi sai ya shige cikin ƙasa.

[5]  Sanke, wasu itace da ake gittawa a garke don kar shanu su fita.

[6]  Wata dabba ce mai tonon rame da sauri.

[7]  Ɗabi’a.

[8]  Ya baka kyautar hatsi.

[9]  Tafiya a ruɗe wadda mutum bai sai inda ya nufa ba.

[10]  Makanta ko rashin gani sosai

[11]  Jan hankalin don tayar da sha’awar saduwa.

Post a Comment

0 Comments