Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Waƙar Isah Mai Kware
Isah Maikware a garin Dukkuma yake ta ƙaramar hukumar Sabonbirni yamma ga Adamawa[1] a
cikin jihar Sakkwato. Shahararre ne ga noma don haka Amali ya kai masa kiɗansa.
G/Waƙa : Zahin rana,
: Bai tauye[2] ka
ba,
: Sabon Goje[3],
: Isah Maikware.
Jagora:
Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
‘Y/ Amshi : Zahin
rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora:
Kurman doki,
: Isah ɗan Buwa,i x2
: In ya dinga,
: Sai in an tare,
‘Y/Amshi: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora:
Ranad damana,
: Ba ciwo ba ta,
‘Y/Amshi: In an daure,
: Komi ba ta yi,
: Zahin
rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora: Ku yi gona kui noma,
: Bana gero za a
yi,
: Maiwa za a yi,
: Wake za a yi,
: Dawa za a yi,
: Masara za a yi,
: Gujiya[4] za
a yi,
: Rogo za a yi,
: Shinkahwa za a
yi,
: Kuma duk kyawo
sukai,
: Kowa noma.
‘Y/Amshi: Samo wa yakai.
: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora:
Allah Ubangijinmu,
: Hiyayye mai sama,
: Jabbaru mai
dare,
: Mai rana Haliƙu,
: Na gode mashi,
: Yai man lahiya,
: Da hurata ya
haɗa,
: Suturata Mai
sama,
: Kuɗɗina Haliƙu,
: Matana Mai
sama,
: Mui ta zaman
duniya,
: Kahin lahira
ta ce masu,
: Ta anshe masu,
: Jatau duniya!
‘Y/Amshi: Ba komi ba ce,
: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora: Na biyo cikin Ɓula,
: Hak Kuka tara,
: Girnashe ni
biyo,
: Nik kwan niw wuce,
: Na biyo
Tsabre,
: Na kwan na wuce,
: Tsabren
Citumu,
: Na kwan na wuce,
: Tsabren ɓauna,
: Na kwan na wuce,
: Tsabren sarki,
: Na kwan na wuce,
: Na biyo
Shalla,
: Na kwan na wuce,
: Sai na lwaye[5],
‘Y/Amshi: Na kwan Dukkuma.
Jagora:
Sai na kwan nan,
: San nan zan wucewa.
‘Y/Amshi: Ko can an ce,
: Komi yi sukai.
: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora: Akwai
ruwa,
: Akwai hatsi,
: Cikin duniya,
: Akwai tuwo,
: Akwai hura,
: Cikin duniya,
: Daɗin duniya,
: Kowa samu yakai,
: In kana da
gero,
: Gero za ka ci,
: In ba ka da
gero,
: Gero za ka ci,
: Amma hwa
lahira,
: Da wuyas samu take,
: Ran kwa..,
: Na duniya ba kwa..,
: Na lahira,
: Ran kwa..,
: Na lahira ba kwa..,
: Na duniya,
: Duh halin da
kay yi,
: Yana iske maka,
: In tana da
gyara,
: Rannan ji kakai,
: Ko ba ta da
gyara,
: Rannan ji kakai,
: Sai tana da
gyara,
: Aka gyara maka,
: In ba ta da
gyara,
: Gyara ba shi yi,
: Dab bayan
dangana,
: Wayyo ni raina!
‘Y/Amshi: Baƙon duniya[6].
: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora: Raggo
yana ganin,
: Mai kandu na daka,
: Raggo kana
ganin,
: Tcadadda na daka,
: Sai ta yi
rangaji,
: Ta yi yabƙi[7]
nan haka,
: Yabƙi ɗai takai,
: Yanga ɗai takai,
: Yat tambaye ni
yac ce,
: Yabƙin mi takai?
: Yabƙi takai mijinta,
: Ta dai gane mashi,
: Ta dai sami gaba nai,
: Rana ta dushe,
: Bakin ƙarhe bakwai,
: Kaiwa ƙarhe takwas,
: Bakin ƙarhe tara.
‘Y/Amshi: Kahin a kai ga sha biyu,
: Ya sha nakiya[8],
: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora:
Ko kahin a kai ga sha biyu,
‘Y/Amshi: Duk an durmuya[9].
Jagora: Ko
kahin a kai ga shabiyu,
: Hay ya sa giya.
: Raggo yay yi
tagumi[10],
: Yaz zura hannu
baka,
: Yac ce gaya ma
kowa,
: Bana aiki nikai,
: In na yi
jijjihi,
: Sai rana ta dushe,
: In nit taho
gida,
: In riƙa saƙar kaba,
: Wannan abin da
kowa yaka so,
: In yi shi.
: In ya yi macce,
: Ba ya da haushin runguma,
: Ta rungume shi.
‘Y/Amshi: Ya
yi kamay ya tawwaha[11].
: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora:
Dut ta adana shi,
‘Y/Amshi: Ya yi kamad,
: Dai bai da rai,
: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora:
Damana ta dawo,
: Raggo na kuka,
: Ya zo yai noma,
: Rana ta hana!
: Ya dawo gida,
: Ba tsabad[12]
daka,
: Ba kuɗɗin awo,
: Ya koma bara,
: Mata sun hana,
: Kowak kirɓa,
: Gona za ta yi,
: Tsohon shegen,
: Kuka yat tcira,
: Raggo yac ce,
: Wayyo Allah,
: Wayyo Annabi,
: Wayyo yunwa,
: Wai mi yai maki?
‘Y/Amshi: Koko yunwa jimai[13]
za ta yi,
: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
Jagora:
Yarinya tag ga Isah,
: Gona yana ta noma,
: Ya sha gangara,
: Tay yi duƙe tac ce,
: Isah mi a kai?
: Ya waiwayo ta,
: Yac ce mata aiki ni kai,
: Ko kana kwaɗaina,
: Bana amre akai,
: Ko ba ka kwaɗaina,
: Bana amre akai,
: Abin da nih hi
so,
: In riƙa ƙaton dame,
: In yo sussuka,
: In sheƙe da kyau,
: In auna da
kyau,
: In surhe da
kyau,
: In wanke da
kyau,
: In kirɓe da kyau,
: Sai na yi tankaɗe.,
: In aza sanwad
dawo,
: In nig gamo
daka,
: In yi zaman tankaɗa,
: In dunhe da
kyau,
: In kirɓe da kyau,
: In dame da
kyau,
: Kazo ka sha
hura,
: Mui ta zaman
duniya,
: Yac ce
wuce-wuce,
: Ga wata can ta
wuce,
: Waccan da ta
wuce,
: Hakanan tac ce mani,
: Ke ma da kit
taho,
: Hakanan kic ce mani,
: Dubu kamak ki
sun,
: Ce hakanan sun wuce,
: In na biya ku,
: Ɓata biɗata za ni yi,
: Dut mai biye ma macce,
: Shiga kunya ya kai,
: Sai ta yi zanne,
: Tac ce Isan Dukkuma,
: Sabon yaro,
: Mai kyawon shiri,
: Kai min gahwara[14],
: Kai min gahwara,
: Isah ɗan Buwai.
: Ya waiwayo ta.
‘Y/Amshi: Yac ce,
: Ya yahe[15]
mata,
: Zahin rana,
: Bai tauye ka ba,
: Sabon Goje,
: Isah Maikware.
[1] Sunan wani ƙauye ne a cikin ƙaramar hukumar
Sabonbirni.
[2] Hana shi noma ba.
[3] Babban manomi wanda ya shahara.
[4] Gyaɗa.
[5] Sakankancewa
[6] Mutum.
[7] Yanga.
[8] Ya sadu da ita.
[9] Fara saduwa
[10] Zama shiru mutum ya sa hannu ya tallabe
fuskarsa.
[11] Mutuwa.
[12] Hatsi Musamman dawa ko gero
[13] Yin rauni/ sabautawa.
[14] Afuwa
[15] Yin afuwa
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.