Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarkin Noma Ummaru

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Sarkin Noma Ummaru

Ummaru sarkin noma ne na garin Kalgo a cikin ƙaramar hukumar Sabonbirni ta jihar Sakkwato. Manomi ne wanda ya tara albarkar gona, don haka Amali  Sububu ya waƙe shi.

G/Waƙa : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

 

   Jagora: Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

    ‘Y/Amshi: Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

 

  Jagora: Da munka shigo Kalgo,

: Tunda hantci,

: Kartau[1] na gonatai,

   ‘Y/Amshi: Shi ko Jatau yar rage mai,

   : Yal lunhwasa nan,

  : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

         Jagora: Da munka shigo Kalgo,

   : Tunda hantci,

   : Kartau na gona tai, 

    ‘Y/Amshi: Shi ko Jatau yar rage mai,

   : Yad dakanta nan,

  : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

 

   Jagora: Na gode ma,

: Garba karo,

   : Ban raina ma ba,

    ‘Y/Amshi: Garba yau da hura tai,

   : Mun ka kara,

: Ga nono ta sha,

  : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

 

   Jagora: Garba karo,

: Godiya yakai,

   : Garba maji daɗin sarki.

    ‘Y/Amshi: Yau da hura tai mun kara,

   : Ga nono zalla,

  : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

 

   Jagora: Yak kwaɓi,

    ‘Y/Amshi: Ta ima daka,

: Lalayya[2] an nan,

 

   Jagora: Yak kwaɓi,

: Ta ima daka,

    ‘Y/Amshi: Kindirmo[3] an nan,

 

   Jagora: Garba ‘yak kwaɓi ta,

    ‘Y/Amshi: Ima daka,

: Lolayya[4] an nan,

 

   Jagora: Ko da na cika,

: Bakina da dawo[5],

    ‘Y/Amshi: Sai susab baya,

  : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

 

   Jagora: Jikan liman da Baƙo,

   : Ɗan Hawwa da Alhaji,

    ‘Y/Amshi: Bukar magabata babu kure,

   : Garba Majidaɗi,

  : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

    

  Jagora: Maza ku yi noma,

   : Tara dame,

: Shi ak kyan ku maza.

   ‘Y/Amshi: Da in ga manomi bai da dame,

   : Shi ab bulloso[6],

  : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

 

  Jagora: Maza ku yi noma,

   : Ku yi sutura,

   : Kuma ku aje gero.

 

   ‘Y/Amshi: Da in ga manomi baida dame,

   : Shi as shaɗari,

  : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.

 

  Jagora: Ni da goɗiya tay yi magana,

   : Mamaki niy yi,

   : Tac ce mani noma abu ne,

   : Jatau mai ƙwarya,

   : Tac ce kai dai ad da dame?

: Shin ko ko ni dai?

   : Nic ce ke dai ad da damen nan,

: Ki zama tamna,

: Tac ce Kartau ya yi guza,

: Bai zan hwanko[7] ba,

    ‘Y/Amshi: Gidan Ummaru an tara dame,

: Ya ebe haushi.

  : Koma gona,

: Gak ka sake,

   : Noma sabo nai,

   : Sarkin noma,

: Ummaru mai,

   : Albarkar hannu.



[1]  Manomi

[2]  Lumui-lumui, wato iya daka da kyawo.

[3]  Kamantawa ya yi a nan, kindirmo nono kenan wanda aka burke tare da mansa, ba a ƙara ruwa ba.

[4]  Daka mai kyawo da ƙwarewa.

[5]  Gayan fura.

[6]  Aikin banza.

[7]  Wanda bai da arziki/samu.

Post a Comment

0 Comments