Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Turken Zuga a Waƙoƙin Amali Sububu
Wani
masani yana cewa
Zuga tana ɗauke da wasu kalmomi ne da ake amfani da su a koɗa wani mutum, a ciccoɓa shi, a nuna fifikonsa kan wasu. Gusau, S.M (2008)
Amali
ya kawo wannan turken a cikin waƙoƙinsa kamar haka:
Jagora : Ai yau da ka ja wan Bakwai ga noma,
’Y/Amshi : Ƙara ka dace
da ƙaddara,
: Ta hana
maka halin zuwa gida.
: Ya riƙa noma da gaskiya,
: Aikau jikan
Tayawo Ɗan Mamman,
: Kunkelen hwashin
ƙasa.
Jagora : Ai yau da ka ja wan Bakwai ga noma,
: Ƙara ka hau
goriba ka hwaɗi,
: Ka suma a hesa maka ruwa.
: Ya riƙa noma da gaskiya Na Bakwai,
: Bai saba da zama,
: Aikau jikan Tayawo ɗan Mamman,
: Kunkelen hwashin
ƙasa.
(Amali Sububu:
Aikau)
A wata waƙar kuma ya
zuga gwarzon nasa yana cewa:
Jagora : In dai sallah kakai ka bar tsahi,
: Ba ka dai gadi yin ta ba.
: In kuma tsahin ka kai ka bar sallah,
: Ka san ba su gamuwa.
’Y/Amshi : Ku duba idanun mutum kamam maye,
: Jawur ba su da
hwari.
: Ya riƙa noma da gaskiya,
: Na bakwai bai
saba ba da zama,
: Aikau jikan Tayawo
ɗan Mamman,
: Kunkelen hwashin
ƙasa.
(Amali Sububu:
Aikau)
Akwai turken zuga a cikin waɗannan ɗiyan waƙar Amali, dubi yadda yake zuga wanda yake yi wa waƙar da cewa gara ƙaddarar da
ke iya hana maka halin zuwa gida da ka ja Aikau da noma! Ko kuma ka hau goriba
ka faɗo har ka suma a fesa maka ruwa kafin ka farfaɗo. Dubi
kuma wata zugar da ya yi wa Aikau yana cewa wai in dai yana sallah ya bar yi
don basu haɗuwa da tsafi. Wannan dukansu idan an biye su sai a faɗa wani
hali, shi mawaƙin babu ruwansa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.