Ticker

6/recent/ticker-posts

Turken Yabo a Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

 Turken Yabo a Waƙoƙin Amali Sububu

Yabo wani babban turke ne wanda mawaƙan Hausa suke amfani da shi kusan fiye da sauran turakun, Yabo shi ne  ambaton kalmomin sambarka da nufin nuna amincewa da hali ko wani abin da mutum ya yi nagari. Gusau, S.M (2008)

Jagora : Rana ta hwaɗi bai hwasa gab,

: Cen kuyye ba,

: Raɓa ta jiɗa,

: Duk ta jike mai baya nai,

: Rana ta ɓaɓɓako dag gabas,

: Ta cinno mai,

: Rana ta cika ta sa ka yin ƙarhin baya.

 

’Y/Amshi : Bai san gajiya ga gona ba,

 : Dinga sai swahe,

 : Koma gona,

 : A gaishe ka alkali Musa,

 : Komi ni ka so ga Musa,

 : Ya na miƙo man shi.

 

Jagora : Rana ta hwaɗi bai hwasa,

: Horon kuyyai ba,

: Raɓa da jida dut ta jiƙe,

: Mai baya nai,

: Rana ta ɓaɓɓako da gabas,

: Ta cinno[1] mai,

: Rana ta cika ta sa ka yin,

: Ƙarhin baya,

’Y/Amshi : Bai san gajiya ga gona ba,

 : Dinga[2] sai swahe,

 : Koma gona ,

: A gaishe ka alkali Musa,

: Komi ni ka so ga Musa,

: Yana miƙo man shi.

(Amali  Sububu: Alkali Musa)

 

Amali Sububu yana yabon gwarzonsa da aikin gona komai yawan raɓa ko rana shi bai fasa zuwa gona ya yi noma. Don haka idan ya fara noma bai tsayawa sai safiya ta waye.



[1]  Haskensa.

[2]  Ci gaba ba tare da tsayawa ba.

Post a Comment

0 Comments