Ticker

6/recent/ticker-posts

Turken Habaici a Waƙoƙin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Turken Habaici a Waƙoƙin Amali Sububu

Shehun malami Ɗangambo ya bayyana habaici da cewa “ Magana ce mai ɓoyayyar manufa” (Ɗangambo 1984, sh 42).

Habaici shi ne gugar zana, wanda Hausawa kan ce ma a laɓe ga guzuma a harbi karsana. Amali ya kawo wannan turke a wasu wurare a cikin waƙoƙinsa kamar yadda za a gani:

Jagora : In ɗan dandi tay yi mai daɗi,

 : Ba ya son gida,

 : Amma ko da ta yi mai ƙono,

 : Sai ya lissahwa[1],

’Y/Amshi : Ka ji ya ce gida ni kai,

 : An ce baba na kira na.

 : Riƙa da gaskiya,

 : Noma ba kashi yakai ba,

 : Yari Ɗan Bagge,

 : Noma ba ya sa ka rama.

(Amali  Sububu: Yari ɗan Bagge)

 

A wani wuri kuma cewa ya yi:

Jagora : Ai naga tuwonki wance sai makaho,

: Sai ko wanda ba gida kusa,

: Da ya ci tuwon kwabo,

: Ya burkuce hanji,

    ‘Y/Amshi  : Sai zuwa wurin amai.

 :  Za ni ga Gora uwar tuwo,

 : Ta  Sa’idu buƙatakki ta biya,

   (Amali: Gora)

 

Amali  Sububu ya yi habaicinsa a wani ɗan waƙa inda yake cewa:

Jagora : Su wane ba su da aiki x2,

     ’Y/Amshi : Sai dai karɓar bashi,

 : Wuce maza bisa noma,

 : Kulkin horon jema,

 : Na sada ka yi ma aikin gona,

 : Shiɗa maiki.

 

Jagora : Ku dai jiddun[2] bashi,

 : Ku dai jiddun bashi,

’Y/Amshi : Sai bashi ya ci ku,

 : Wuce maza bisa noma,

 : Kulkin horon jema,

 : Na Sada ka yi ma aikin gona,

: Shiɗam maiki.

(Amali  Sububu: Salau na Maimuna)

 

A wata wani ɗan waƙar kuma ya yi habaici kamar haka:

 

Jagora : Ko kaɗan ban yi zato ba, x2

’Y/Amshi : Ashe Mazuru madaƙuƙi[3] ne,x2

 : Mu taso mu taho gaisai,

 : Batunai luguden sabra.

(Amali  Sububu: Buda)

 

Wani wurin kuma ya ce:

 

Jagora : Na ga yunwa ta tuzga[4] da matar raggo,

’Y/Amshi : Na ji an ce hat ta saci garin kwaki,

: Na taho in kai mai dandama garka tai,

 : Buda ko san noma baya hi nai ƙarhi.

  (Amali: Buda)

 

Wannan turken ya fito a wata waƙar inda Amali ya ce:

 

Jagora : Masu zuwa haji kui ta zuwa haji,

’Y/Amshi : In don karen ɓuki ba ya zuwa haji,

 : Sai dai ya sami gyaɗa ya yi ƙanƙara,

  : Ko da rani baya zama gida,

     : Gidan Karimun  Za ni wurin kiɗi.

(Amali  Sububu: Abdulkarimu)

 

Makaɗa Amali Sububu ya kawo turken habaici a cikin waƙoƙinsa kamar yadda aka zaƙulo misalan. Dubi yadda ya yi habaici ga raggo wanda shi a ganinsa shi ke fita dandi ya faɗi yadda yake cewa in ta yi mai ƙono sai y ace komawa gida yake yi don ko aikin marece ya riƙa zuwa, haka kuma ya yi shaguɓen  ga wata da bai ambaci sunanta ba mai tuwo-tuwo da kuma wasu da ya ce wa su wane ba su da aiki sai dai karɓar bashi, sai kuma y ace wani ɗan waƙar ya kira wani mazuru kuma wai shi madaƙuƙi ne! a wata waƙar kuma ya yi wa wani da bai kira sunansa bad a suna karenɓuki wanda y ace in don shi baya zuwa haji.



[1]  Yin tunani bayan an sha wuya.

[2]  Kodayaushe.

[3]  Marowaci, wanda ba mai cin abinsa.

[4]  Kamar yadda gaɓa take yi idan ta zaizaye. A cikin waƙar yana nufin yunwa ta kama matar raggo.

Post a Comment

0 Comments