Ticker

6/recent/ticker-posts

Turken Wa’azi a Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Turken Wa’azi a Waƙoƙin Amali Sububu

Hornby (1998) ya ce:

Wa’azi shi ne yin jawabin da ya shafi addini[1].

Haka kuma:

Wa’azi shi ne jawabi kan abin da ya kamata Musulmi ya yi da abin da bai kamata ya yi ba, ta kawo hujjoji daga Ƙur’ani da Sunna, da niyar mai da al’ummar Musulmi tafarkin gaskiya[2].

Wa’azi na nufin ambaton wasu kalamai a cikin waƙa masu dangantaka da addini da niyar shiryar da Musulmi ga tafarki madaidaici da kuma tsoratar da su daga barin wannan tafarkin.

 Ga misalan wuraren da makaɗa Amali  Sububu ya yi turken wa’azi a cikin waƙoƙinsa kamar haka:

 

Jagora : Mahaukaci bai ci duniya ba,

  : Mahaukaci bai ci duniya ba,

  : Ku gane ko ya ci bai sani ba,

  : Abin da ak kyau ga ɗan Musulmi,

  : In ka ji daɗi tuna da gobe,

  : In ka ji ɗaci tuna da gobe,

  : Tuna da Sarkin da yay yi ranka,

  : Ka san da shi ya halicci ranka,

  : Ka gane shi ne mara iyaka,

  : Ka hangi ramen[3] da za a sa ka,

  : Kowa ka dubin irin hakanga Jatau,

  : Ai ba shi gurin ya tabka ɓanna,

  : Kowa yi ɓarna tana ga kainai,

  : In ya yi gyara shina ga kainai.

’Y/Amshi : Ya rasulu ya kyauta ƙarshenmu,

  : In ji Ɗan Iro mai tahwashe.

  : Ya biya mai kuɗin manoma,

  : Mu kai dumanmu gidan Nadada.

        (Amali: Nadada)

Kusan dukan kalaman da Amali ya yi a cikin wannan ɗan waƙa tamkar wa’azu ne yake yi wa mutane, saboda duk wanda bai yin tunani a harkokin duniya zai iya faɗawa a cikin nadama komai daɗewa, kuma zai mutu a sa shi cikin kushewa. Idan mutum yana tunanin haka to bai gurin ta tafka ɓarna.

 

Jagora : Akwai ruwa akwai hatsi cikin duniya,

  : Akwai tuwo akwai hura cikin duniya,

  : Daɗin duniya kowa samu yakai,

  : In kana da gero, gero za ka ci,

  : In ba ka da gero, gero za ka ci,

  : Amma hwa lahira da wuyas samu take,

  : Ran kwana duniya ba kwana lahira,

  : Ran kwana lahira ba kwana duniya,

  : Duh halin da kay yi yana iske maka,

  : In tana da gyara rannan ji ka kai,

  : Ko ba ta da gyara rannan ji ka kai,

  : Sai tana da gyara aka gyara maka,

  : In ba ta da gyara gyara ba shi yi,

  : Dab bayan dangana,

  : Wayyo ni raina.

’Y/Amshi : Baƙon duniya.

  : Zahin rana bai tauye ka ba,

  : Sabon Goje Isah Maikware,

(Amali  Sububu: Isah Maikware)

 



[1]  Hornby (1998).

[2]  (CNHN:2006)

[3]  Kabari.

Post a Comment

0 Comments