Ticker

6/recent/ticker-posts

Turken Tauhidin Rububiyya a Wakokin Amali Sububu

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Turken Tauhidin Rububiyya a Waƙoƙin Amali Sububu

Tabbatar da cewar babu mai halitta da bayar da arziki da rayarwa da kashewa, kuma babu mai jujjuya al’amurra sai Allah Shi kaɗai[1]." Shi wannan nau’in tauhidin shi ne wanda duk ɗan Adam yake da shi ko Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, kowa ya yarda cewa Allah shi ne Mahaliccin kowa da kowa kuma shi ke kashewa da rayawa, Shi ke azurtawa Shi ke talautawa da jijjuya lamura. Ga irin misalan wannan turken a cikin waƙoƙin Amali  Sububu kamar haka:

 

A wani wurin ya ce:

Jagora : Allah ubangijinmu,

Hiyayye mai sama,

  : Jabbaru mai dare,

Mai rana haliƙu,

  : Na gode mashi,

  : Yai min lahiya,

  : Da hura[2] ta ya daɗa,

  : Suturata Mai sama,

  : Kuɗɗina Haliƙu,

  : Matana Mai sama,

  : Mui ta zaman duniya,

  : Kahin lahira ta ce masu,

  : Ta amshe[3] masu,

  : Jatau ,duniya!

’Y/Amshi : Ba komi ba ce,

  : Zahin rana,

: Bai tauye ka ba,

  : Sabon Goje,

: Isah Maikware.

(Amali  Sububu: Isah Maikware)

 

A cikin waɗannan ɗiyan waƙar, Amali ya fito da turken tauhidin Rububiyya a wurare daban-daban, inda yake nuna cewa Allah maɗaukakin sarki shi kaɗai ne yake yin baiwa, dubi yadda ya fara da gode ma Allah saboda lafiyar da ya ba shi da hura (wato abincin) da ya ba shi, da sutura da matan aurensa.   



[1]  Sheikh Abdulwahab ya  bayyana Tauhidi Rububiyya a cikin Littafinsa mai suna Tafsiru kalimatut Tauhid

[2]  Abinci Amali yake nufi.

[3]  Ya mutu kenan.

Post a Comment

0 Comments