Ticker

6/recent/ticker-posts

Turken Godiya a Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Turken Godiya a Waƙoƙin Amali Sububu

Mutum kan yaba wani abin kirki ko wata kyauta da wani ya yi masa, wannan yabawar ce ake kira godiya.

Jagora : Da arziki na irin na yanzu,

  : Da arziki na ina da raina,

  : Ina da ƙanne ina da yannai[1],

  : Ina da ‘ya’ya irin na kaina,

  : Akwai rikoda ina da keke,

  : Ina da shanu ina da jakkai,

  : Ina da doki ina da mashin,

  : Ina da gero abin dakawa,

  : Akwai tuhwahin da  Za ni sawa,

  : Ina da kuɗɗi abin kashewa.

’Y/Amshi  : Amali sai godiya ga Jabbaru,

  : Shi da yac ce hakanga Jatau.

  : Ya biya mai kudin manoma,

  : Mu kai dumanmu gidan Nadada.

(Amali  Sububu: Nadada)

 

Amali a nan yana godiya ne ga Allah maɗaukakin Sarki wanda ya halicce shi ya kuma sa ya kasance mai wadata a cikin jama’a. 

 

A cikin wata waƙa ma wannan turken ya fito kamar haka:

Jagora : Ɗan Kogi lalle mun gode da kyautar girma.

’Y/Amshi : Da kyautar girma.

: Na taho in kai mai dandama garka tai,

  : Buda ko san noma baya hi nai ƙarhi.

 

Jagora :Sai godiya Makau don ko kari[2] yay yo man,

’Y/Amshi : Don ko kari yay yo man.

 

Jagora : Sai godiya Mudi,

’Y/Amshi : Don ko kari yay yo man.

 

Jagora : Ni Shehu na gode.

’Y/Amshi : Don ko kari yay yo man.

 

Jagora : Ni Jaɓɓi na gode,

’Y/Amshi : Don ko kari yay yo man.

 

Jagora : Ko Ɗangaladima,

’Y/Amshi : Shi ma kari yay yo man,

: Na taho in kai mai dandama garka tai,

 : Buda ko san noma baya hi nai ƙarhi.

 (Amali  Sububu: Buda)

A waɗannan ɗiyan waƙar Amali  Sububu ya ambaci duk wanda ya yi masa kyauta saboda waƙar da ya yi, yana gode masa da irin wannan kyautar, Hausawa dai sukan ce yaba kyauta tukuici.

 

A wata waƙar kuma akwai wannan turken:

 

Jagora : Na gode Allah da Annabi,

  : Na gode girman manoma,

  : In na yi taggo da riga,

  : Albarkacin masu kafce,

  : In ka ga ƙube[3] ga kaina,

  : Albarkacin masu huɗa,

  : In na yi zoben azuhwa,

  : Albarkacin masu ƙwazo,

  : In na yi mata na wari,

  : Albarkacin masu kaibe[4],

  : Na gode Allah da Annabi,

  : Na gode girman manoma,

’Y/Amshi : Ba mu rena girman manoma ba,

  : Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa[5],

: Namijin da noma ka wa haske[6].

        (Amali  Sububu: Garba)

 



[1]  Yayye waɗanda suka grime ma mutum.

[2]  Ba makaɗi kyauta.

[3]  Hula wadda ake ɗinkawa da zaruruwa kala-kala.

[4]  Sharar gona – ma’ana manoma.

[5]  Sauka – baƙo ya ziyarci wani mutum.

[6]  Wanda yake samun riba ga aiyukan noma. Komai ya noma yana kyawo.

Post a Comment

0 Comments