Ticker

6/recent/ticker-posts

Turken Tauhidin Uluhiyya a Wakokin Amali Sububu

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Turken Tauhidin Uluhiyya a Waƙoƙin Amali Sububu

Wannan kashin tauhidi ne wanda ke bayanin cewa babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah kaɗai, kuma ba a haɗa Shi da kowa a wurin bauta.  Wannan tauhidi ne wanda kiristoci da Yahudu da Nasara ke musun sa, cewa a bauta wa wani da Allah ya hallitta domin ya zan tsanin masu yin bauta zuwa ga Allah.  Tauhidin Uluhiyya shi ne abin da Kalimatus shahada ke nufi, wato babu wanda ya cancanta da a bauta masa sai Allah, kuma Annabi Muhammad (S.A.W) ManzonSa ne.

Wani wurin a cikin ɗan waƙarsa, Amali ya kawo tauhidin Uluhiyya  ƙarara yana cewa:

Jagora : Ko yanzu Amali,

: Nib bak kiɗi,

: Komi ya yi,x2

: In na mutu kak,

: Ku ce man muta,

: Ne sun ɓassan[1],

: Na shedi karen gida ba ya,

: Wa kura komi,

: Shi Mai sama tunda ya,

: San iya,

: Kak kwanana,

: Kuma ba ya rage su,

: Ko ya yi zwari[2] sai na kai.

     ’Y/Amshi : In na mutu banda sauran,

  : Zuwa garkak kowa,

  : Koma gona,

  : A gaishe ka alkali Musa,

  : Komi nika so ga Musa,

: Yana miƙo man shi.

(Amali  Sububu: Alkali Musa)

 

Mawaƙin ya fitar da turken tauhidin Uluhiyya a wannan ɗan waƙarsa a inda yake nuna cewa babu mai kashewa sai Allah don ko da ya mutu kar mutane su ɗauka wani ne ya kashe shi, domin mahaliccinsa shi ya san iyakar kwanakin da ya ɗebo masa don haka babu wani da zai iya rage su sai ya kai lokacin da allah ya ɗibar masa.[1]  Kashewa.

[2]  Cikawa- ɗiba da yawa.

Post a Comment

0 Comments